← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 98

Sashe 20

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Naila ta zaro Dari biyu tayi mata rikon tsauri ta tsaya kusa da budurwar me tikar rawar tace a duwawu zan lika miki taje ta manna Dari biyu a duwawun budurwar Nan,da karfi tace aradu ciko ne ciko jama'a,Kuma ta rike kudinta Kam sai ta manna sai ta zare kudinta Yana makale a hannunta, mc Yana ta zugata Dan ta lika tace na ki wayon wlh ficikata baza tayi ciwon Kai ba akan me duwawun ciko ba, ana kallo ta fice tana cewa ciko ne wlh kar Wanda ya lika sisi gwara muci tsire ciko take mirgudawa,na taba maimakon naji wajen Yana karkarwa sai naji yayi dubush baya motsi kar kuyi asarar kudinku,suna ta dariya Yan gidan yari,amma sai da wasu suka lika kudin sosai,Scoler ya Maida kudinsa aljihu ya fasa likin yace asararru

Ba'a wasa da Yan daurin rai da rai ko sun kasheka to fa su hukunci daya dai gashi Nan shi yasa budurwar Yar film sum sum ta koma wajen rawarta bata ce kala ba duk tijarar da Naila tayi mata,kamar ba gidan yari ba yanda ake likin kudi ana zuba naira Banda Spark bare Jamilu Naila da ba gatan kirki shi yasa yaki lika sisi,Scoler ne yazo yace me yasa wai Baki yi likin ba? Allah ya hana likawa irin wannan masu yada badalar kudi haka Malam Jilani suka ce Kuma na dauki wa'azinsu,Scoler yace munafukan malamai Allah yasa kar su kashe Maka zuciya ka daina Daudu,Naila tace a'a wannan ko Sudais ko shureim na Makkah ne suka zo bazan daina ba Daudu yanzu na fara,Scoler yaji dadi yace yawwa ko Mufti Menk ne karki dauki wa'azin,Naila tace hauka nake Daudu for life.

Spark Yana jinsu ko harkarsu bai shiga ba.
Tunda Spark ya zauna baiyi Magana ba daka kallo sai danna waya har ya gaji ya mike zai tafi abinsa Naila bata kulashi ba itama,sai da ya tafi tace Dan iyayi wai shi me kudi dan ya samu ma Ina kulashi sai nayi maganinka.
Tashi tayi ta koma dakinsu Inda kasa kasa tana jiyo surutun mata dakin wasu a Jikin dakinsu yake,Naila ta Dora kanta a Jikin bango tace da karfi Ina son daya a cikinku,Mata ta bangarensu sukaji magana,wata a ciki ana ce mata Beauty tace Ina sonka nima sunana Beauty.

Kasa kasa Naila taji tayi tsalle tana murna,tace Inama da kofa da na Kalli fuskarki,sunana Beauty aka bawa Naila amsa mata sai shewa suke a dakin,Naila tace mashaallah zamu dinga zance ta Nan sunana Jamilu me zamani,Beauty tace daga Jin Muryarka ka hadu,Naila tace da zaki Ganni sai kin dalalar da yawu na hadu,Wata a ciki tace nima Ina sonka,Naila tace duk ku taho Ina sonku ni na mamajo ne ko wacce zan iya da ita,ya aka ji da rashin da namiji a kusa? Beauty da karfi tace muna fama wlh duk gamu taron balagaggu,Naila tana dariya itama da karfi tace iceko bakwa warin balaga? Malam Garzali suna dakin suna jinsu su tunda suke ma basu taba Jin Muryar mata ba sai yau,Kunya duk ta kamasu manya dasu gasu malamai Jamilu duk ya takura musu,ga kaunarsa duk ta kamasu sun rasa sukuni,Beauty tace Kana da waya? Naila tace me kika ce? Banji ba,kana da waya? Naila tace Allah sarki maraya ne ni,Beauty Yar gidan me kudin gaske ce itama kaddara ta kawota tace karka damu zaka yi waya me tsada zansa Daddy ya kawo amma sai munci gaba da soyayya Naila a ranta tace dole na dage naci kudin Beauty, Su Malam Jilani suna jinta sun kasa karatunsu da suke faman yi,Beauty tace da dare zamuyi free call ta jikin bangon nan,Naila tace karki damu sai anjima bye.

Ta Kalli Malam Jilani tace ku malamai ba a morarku sai dai ku Mori mutum wato tunda nazo Kun San maraya ne ni amma ko sisinku ba a ci haka aka koyar daku a Islamiyya,Malam Sharu ya zaro Dari biyar yace ita kenan gareni ungo Dan Allah ka canja wani dakin Jamilu,Naila tace tab Ina nan so kuke ayi min fyade,Malam Garzali a hankali yace mun shiga uku mu dai.

Umma ita kadai ce a gidan yara suna Islamiyya da yamma lis sai Abba yayi sallama ya dawo a gajiye Yana Nishi ya zauna Saman kujera,tace Kai Kuma lafiya? yace yau Nasha aiki jarkar Mai biyar na dauka a wajen aiki duba min kaina na fara sanko ko? Umma ta watsa Masa harara tace yanzu sabo da lalacewa akan ka dauki jarkar mai biyar shine abin gajiya haka har wani sanko zai fito Maka,Abba yace ke kinji nauyi ni gaskiya idan haka zan dinga yi zan bar aikin Nan bazan iya ba,Umma ce ta fashe da kuka,da sauri ya kalleta da Dan cikinta a gaba sanye take cikin riga da zani na atamfa,yace lafiya taki magana sai kuka take yi,yace haba Kubra menene? ta sake fashewa da kuka,Abba duk ya rude Yana tambaya menene? Sai da kyar tace Dan cikina nane yace a dauke shi,Abba ya bude Baki yace ta Ina yayi maganar? ya akayi ni banji ba, through placenta ya fada min uwa ce kawai ke gane yaren danta,Abba ya kalleta yace yanzu Kubra na gaji amma baza ki tausaya min ba,taya zan dauki jaririn Dake ciki? tace ai idan ka daukeni to ka dauke shi,Kubra gata me kiba Abba Dan tsurut haka ya Mike ya yunkura Yana Nishi ya dauke ta da kyar suka tsaya a tsaye,tace kaji wai a zaga da shi yace,Kubra nauyi ne Dake wlh kamar buhun sugar kiyi hakuri kuka ta fara ya fara zagawa da ita a hankali da kyar Yana Nishi,sai da taga ya Sha bakar wahala sannan tace yace a cinyarka zai zauna shi,Abba ya ajiyeta da sauri Yana Nishi kamar me,ya zauna ta zauna a cinyarsa yayi zuru da Ido ransa a bace sai da taga yara zasu dawo sannan tace to danwake zaka yi min yau yace shi zai ci,Abba ya kalleta kawai ya Mike ya shige daki tare da kulle kofar ya sa key shi bazai iya cewa bazai yi mata ba tunda ya Saba Yana yi mata watarana.

Mummy tunda aka kama Spark hankalinta fa ya tashi matuka kuka ba dare ba rana,duk ta rame ta lalace burinta taje taga Danta,sai lokacin ta tuna da Jamilu fa Yana can shima ta dalilinta,share zancen tayi duk da suna waya da Spark amma Sam hankalinta baya jikinta, Mima Kam abin a ranta yake dukanta Wanda ba Wanda ya gane Hakan sai dai a ganta duk ta fige ta rame,Daddyn su Spark shi kansa abin Yana damunsa amma ba yanda zaiyi.

Mima tana dakinsa ya kalleta a hankali Sam bata hayyacinta duk ta rame,tambayarta yayi yace meke damunki ne ko tunanin Spark ne? Mima murmushin karfin hali tayi tace a'a...idonta ya ciko da kwalla sai kuka bata San sanda ta fashe da kuka ba,Daddy ya kalleta cikin shigarsa na kayan manyan sojoji Yana Shirin fita,yace sai hakuri fa kaddara ce sai dai addua.

Rafeeq ne ya shugo ya same su a haka da sauri Mima ta goge hawayenta ta nuna ba komai shima Rafeeq duk da yaji zancen su bai nuna yaji ba,gaishe su yayi kawai sannan Mima tace ya school din? yace Alhmdllh,Kuna waya da Spark kuwa? yace dazu ma munyi waya da shi ai shi baya cikin wahala part dinsa ma daban,Mima tace yayi kyau na kira shi yaki dagawa ai,dole yaki dagawa ni banga laifinsa ba Yana da gaskiya,Ku Baku bari anyi bincike ba Kun kasa tsaya masa Wanda Kun San gaskiya bazai aikata ba amma kuka goyawa iyayen Asmau baya an bata Masa suna sabo da Yan uwantaka,dama Aunty ce ta aiko ni tace ki bata sakon na Kai mata,Mima tace to tana wani bata rai ta dakko sakon ta mika Masa a leda tace yaya kudin baka kawo ajiyar ba, fuska ya daure yace na bawa Aunty ya juya tare da ficewa abinsa.

Mohsin zaune yake Saman Sallaya Yana addua cikin tsakiyar dare Naila yake ta yiwa addua,Hanan ta farka tace wai har yanzu adduar ce kazo ka kwanta karka kashe kanka akan wata,ko kallonta baiyi ba,haushi ya kamata tace wannan Naila din kwai tsinanniya ta Hana mijina sakewa,a fili tace yau kwana nawa kaki kazo ka sauke min hakkina Kuma kasan Ina bukatar namiji a kusa,bai ko saurareta ba,ta ja tsaki tace wlh bazan yarda ba sai na kaika Kara wajen iyayenka kazo ka min abinda nake bukata, mikewa yayi ya bar mata dakin ya dawo Palo,tashi tayi tace wlh baka isa ba akan Yar iskar kanwarka ka wulakantani tazo Yana sallah ya tada sallah ta fado gabansa, ai kuwa ya Kifa mata Mari ya makar da ita gefe ta Fadi can gefe wanwar, sallarsa ya tayar, sabo da ta hanashi sallah ta dinga kururuwa amma bai fasa sallarsa ba har ta gaji.

Washe gari da safe ta riga shi tashi sai gidan su Mohsin Yana bacci Bai San ma ta tafi ba,tana zuwa ta samu Umma suna karyawa da yara yau ba school, tunda Umma ta ganta tasan ba lafiya ba,dama ta tsani Hanan bata mata kyauta kadan take jira,Abba kuwa Yana zaune abinsa ya gama karyawa Hidaya tana aikin gida yara suna wasansu.
Chapter 20 · 0% Book details