← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 98

Sashe 49

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Naila washe gari da wuri taje gidan Mummy a taxi da katuwar akwatinta zata koma gidan Spark da zama,Mummy tace gaskiya na yarda da gaske kike harkar nan,Mummy ta shirya cikin kana nan kaya matsatsu ta yafa Dan guntun mayafi tace muje,Naila ta zaro ido tana kallon Mummy a ranta tace tab,motar Mummy suka shiga,Mummy ta tuka suka nufi gidan Spark, Yana bacci kasancewar ba aiki yau Sunday, har gidan Mummy ta murza hancin motarta ciki, bayan tayi parking Naila tace nazo gidan mijina gidana,tana kallon gidan tunda take bata taba ganin gidan da ya tsaru haka ba sai yau a gidan spark,gidane Wanda an kashe Masa kudi iya kudi,ko da ya fito daga prison sai da aka sake canja kusan komai na gidan, ga motocinsa Nan masu tsada iri iri, duk Inda ake neman gida to gidan Spark ya Kai,Spark ne ya fito Jin mota ta shugo Masa gida,Sanye yake da gajeren wando baki da Yar tshirts brown ba karamin kyau yayi ba duk kuwa da cewa daga bacci ya tashi.

Naila ya kalla ta canja glass yau tasa brown ya mata kyau,sanye take cikin atamfa riga da skert sun masifar mata kyau,ga gashin ya yarfo a fuskarta ta yafa mayafi kawai ba dankwali a kanta mayafi ne a Saman kanta,Spark dariya yayi a ransa yace haba yarinya sai dai kiwa wani basaja ba ni Spark ba,yace wannan karya ne Naila ce yace ni da na zauna tare da ita mun kwana bed daya ma lokacin tana Jamilunta,Bata gaji da wasan nan ba lallai yarinyar nan yarinyar nan da taurin hanci take,Ashe da rabon zanyi kallo na biyu kenan,murmushi yayi a fili tare da danne lip dinsa na kasa da hakoransa na sama,ya Bata rai yace wannan fa, good day sir cewar Naila tana wani sirara Murya,kallonta yake sama da kasa murmushinsa ya kasa boyuwa yace ashe dai Yar wanka ce ko Kuma basaja aka dawo yi min,Mummy tace gata nan zata zauna da Kai zata dinga Maka girki,sabo da kana zama da yunwa ko ka dinga yi da kanka Ina raye bai dace ba,shi tun da ya yaji zancen yasan da wata a kasa Mummy ita tasan me Naila ta fada mata,Kuma shi yasan Naila dai zagin Ashraf take zata dauki fansa kenan ya furta a ransa,wow wannan yarinya amma zan bari naga ni me zata min ta dau fansar ita Kuma Mummy idan bata yi wasa ba kwana nan zata shiga prison domin indai ya tabbata Naila ce wannan to wlh ko makawa babu fansa tazo dauka,Mummy Taga Yar gayu ta yarda da ita Kai duniya,da wani bagidajene yazo baza ma ta kula mutum ba,shi sai yanzu ma ya gano bakin zaren,yace lallai yaro yaro ne Kuma mace mace ce tab,zanga ni ya za ayi dani.

Spark shi bai San tuni ma Naila ta kwantar Masa da Hallare ba yanzu ma magani tazo ta Masa ba tare da ya sani ba shine dalilin zuwanta gidan, shi Kuma yace dole nayi taka tsan tsan da Jamilu yanzu haka ma tunda ta gano nine Ashraf to ta daina so na tabbas,amma bari na gani ya zama dole na kula da me zata yi sannan na dage da addua Allah ya rabani da Sharrin Naila ta shiga bani tsoro,ashe da gaske take, jikinsa ne yayi Sanyi sannan yaji haushin Naila matuka da tazo da niyyar cutar da shi,yace amma ba komai ni Kuma wannan karon indai su Mima sun kawo min matar aure ko wace zan aureta kawai,gaba daya Nan take ya canja kala idonsa ya canja wani tsantsan bacin rai ne kwance a fuskarsa,yace maimakon ta hakura muyi aure kash,juyawa yayi yace zata iya shugowa na amince ta zauna ya wuce kawai ya haura sama.

Naila tasan kayanta ta hango bacin ransa tace hmm baya so shi wata ta rabe shi Allah sarki abin kaunata shi Jamilunsa yake so,Mummy Nan take ta turawa Naila kudin rabi a accnt tace ki kula da shi sosai ina so aljanun su fita kinji,Naila tace an gama,ni daga Nan ma sana'a zan kama na daina harkar film,Mummy tace yanda kika gani amma kin hadu da Jinin arziki zaki ci Naira ki more matukar Spark ya amince da zabin mu yayi aura.

Naila tana shiga ciki a kasa ta zabi bedroom ta shiga ta ajiye kayanta tana ta murna tace wayyo Allah dadi yau Gani a gidan Spark dina,shi Kuma Spark Yana sama ya zauna a gefen bed yayi shuru kawai mamaki yake wai dama Naila ba sonsa take ba amma ko da zata dau fansa a tunaninsa idan ta gano shine Spark zai ci darajar son da take Masa,tagumi ya zuba hawaye zubo Masa a Saman kumatu,yasa handkerchief tare da gogewa,kasa komai yayi wankan ma kasa yi yayi ya koma ya kwanta kawai,mikewa yayi ya sake zama tare da hargitsa gashin kansa ya furzar da wata iska me huci,yace ni na taba soyayya irin wannan haka tunda nake, akan mace har nayi hawaye.

Naila kuwa murna take kawai ta fito ta shiga zaga gidan tana Shan kallo sai da ta gama kallon ko Ina sannan ta shiga kitchen Dan girkin data iya kadan ne Dan ma ta koya a wajen Sheyi,Irish ta soya da kwai ta dafa tea ta zuba a flask ta kawo dining tana jerawa,Spark ne ya fito fuskar nan murtuk,Naila tunaninta Bai ganeta bane shi yasa,a hankali tace sannu sir,ga breakfast,Spark yayi zuciya a ransa yace bari na ci idan ta kashe ni ita tayi asara,ya zauna a fusace a kujera tana murmushi ta gyara glass dinta ta hada Masa tea tun daga yanda ta hada Masa tea yasan wlh Naila ce duk abinda yake so ta sani gashi nan, Bismillah yayi tare da addoui yace a ransa idan na mutu Allah na yafe mata sabo da son da nake mata,Allah ka zama sheda,Naila dai taga Yana addua bata San me yace ba,tea din ya dauka ya fara Shan abinsa zama tayi a kujera tabbacin ta Saba da shi gashi shi tsiyar so baya buya,Naila a nutse ta dinga mika Masa slise bread din Yana karba,sai faman satar kallon juna suke,shi dai baice mata kala ba,amma itace tace Sir abincin yayi? Ko kulata baiyi ba wani haushi take bashi ma harara ya watsa mata tace a ranta bai sanni ba Bai ganeni ba Allah sarki bai San Jamilunsa bace .

Mima kuwa ganin Chikar gayu bata ji amma Kuma ta shiga ranta sai tace wannan itace daidai da Spark za yi maganinsa,sai ta kirata har dakinta,Chikar gayu ta zo zata durkusa,Mima tace Chika ya sunanki na gaskiya ma kika ce? Suhaila,suna me dadi,Ina so muyi wata magana tace to Ina jinki, zaki auri Dana? Chikar gayu ta zaci Misam ne da sauri tace ae me zai hana ai kina da kirki Kuma tunda na shugo gidan Nan nasan Ku mutanen kirki ne,a ranta Kuma tace karya nake ku ba mutanen kirki bane Yan wulakanci in kuka ga talaka ne mutum, Mima tace Spark nake so ki aura,Chikar gayu wani gumi ne ya keto mata tace a ranta ai Naila sai ta kashe ni Allah ya tsareni da cin Amana,a fili tace a'a Mima kiyi hakuri wlh bazan iya ba dama wani ne a ciki ba Spark ba,Spark ya haramta a gareni,ba Wacce zata ce baza ta so shi ba amma Banda ni wlh kiyi hakuri a canja min wani,Mima tace to kuwa sai dai ki bar gidan nan,Chikar gayu tace gari da yawa ai maye baya cin kansa,dama ni karya nake miki baku da halin arziki yawwa in fada miki gaskiya Ina da gatana,karki ganni a nan kice bani da gata,Mima tace to hada kayanki ki bar min gida,tace ko baki ce ba dama,ta juya ta fice kayanta ta tattaro tayi wanka tun a gidan ta canja kayanta masu kyau ba Wanda zai ganta ya rainta ta fito Palo tazo ta jefawa Mima Jakarta tace gashi nan dama aro su nayi Dan Allah a kone su ko a kaiwa dangi a kauye.

Kuma bari kiji nafi karfin na muku bauta shi yasa kuka ga Ina muku rashin mutunci iri iri yawwa, danki Kuma bazan aura ba a likawa wata mu bamu gaji cin Amana ba yawwa,ta juya tana murguda duwaiwaka tace ayyiriri mamarrrrrrrrr......ta wuce tana jijjiga jiki tana waka,Mima baki ta rike tace ashe da Karuwa muke zaune.
Chikar gayu tace Allah ya rabamu da zuriar masu kisan Kai mugun iri,ta juyo ta Kalli Mima tace byeeeeee....

Tana fitowa Misam ya shugo Allah yayi shi da neman matan tsiya gashi mata suna rububinsa sabo da shima ba karya,Chikar gayu ya Gani ta fito tana karkada jiki zata fita,Bai taba kulata ba sai yau,yace Chik....da iyayi Juyowa tayi ya kalle shi Yana birgeta a rayuwa yanzu Kam tasan yanda tayiwa uwarsa fitsara Ina zata bari ma suyi alaka.

SANARWA

DAN ALLAH YAN PAID GROUP KU RIKE AMANA KARKU BAWA WASU KYAUTA.
ITA TA KASA SIYA KE KIN SIYA KIN BATA TA PRIVATE TASAN BA SIYA TAYI BA DOLE TA BAWA WASU A HAKA ZASU TURA SHI GROUPS DA YAWA.

YAU DA ACE ITA KADAI ZATA KARANTA TA PRIVATE DA SAUKI SAI KU BAYAR A WATSA SHI A GROUPS

WLH DA AYI WANNAN GWARA MUTUM BAI SIYA BA.
AKWAI CIWO GA WRITER DA WANDA SUKA SIYA.

AsmaBaffa
[12/14/2023, 8:24 PM] AsmaBaffa: PAID BOOK

Accnt no

0175487861
Asmau Garba Muhammad Gtbank

Katin MTN
08061929616

Yan Niger
+22790795939

🏫 TANTIRIYA 🏫
A GIDAN YARI

BOOK 1

51-55

Official

By
AsmaBaffa

Sadaukarwa gare ki
AIDA MAMAN TASNIM

Page naki ne
HASEENA AHMAD DAURA

Hey lovelies

Ke matar aure ce kuma kina neman business din dazakiyi daga gida da kuma baya bukatan jari?

Kai dan makaranta ne kuma kana neman inda zaka ringa samun kudin kashewa?

Ko a'a ke kinada business dinki Amma kina neman wani side hustle haka da zai Kara Miki extra source of income?

Ko kinada business idea da kikeson kifara Amma Babu jarin farawa?

Toh duk ku tarkato wannan training din, dan ga solution nan nasamo muku, kawai ki danna wannan link din Dan Samun damar shiga group din

https://wa.link/49vn47
Chapter 49 · 0% Book details