← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 98

Sashe 12

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Spark kuwa wata ajiyar zuciya ya sauke yace an maidani yaro,matar aure ma ace sai an zabar min a rayuwa ni bani da yanci,me yasa ni ake takura min ne,ba laifi na bane,nayi soyayya da yawa,nayi Yan mata daban daban baza su irgu ba at the end zan gano kudi na suke so ko kyawun da Allah ya min bani ba, sabo da haka soyayya ban Kara yi har abada aure na hakura bazan yi ba dama ban taba yinsa ba.

Kwanciya yayi a Saman 3str ya baje kafarsa daya tana kasa daya Kuma tana Saman kujera,kansa ya dafe yana kallon sama ya Lula tunanin duniya.
Babban Amininsa ne ya shugo Kuma cousin brother dinsa Kamal,Sallama yayi ba tare da ya kalle shi ba ya amsa Masa, Kamal ya kare Masa kallo sanye yake cikin jallabiya coffee color me tsadar gaske kawai shining take tana sheki, hannu Kamal ya mika Masa suka gaisa sannan Kamal ya tambaya Spark how far?

Ashraf Wanda aka fi sani da Spark Sam Ashraf asalin sunansa ya buya kowa da spark yake kiransa har iyayensa,sabo da kalar idanuwansa da kwayar idonsa suke kamar blue kamar baki Kuma irin kalar na wasu turawan, yace I'm good bro,Kamal yayi dariya yace dan wulakanci shine ka Kori Asmau? Kafin ya rufe Baki Spark ya furta mind your Business,ya ja tsaki ya Mike,shi dama bashi da mutunci baya ragawa kowa duk abinda yaga dama kawai zai yabawa mutum a haka ma Dan Kamal ne shi yasa ya raga Masa,mikewa yayi a fusace ya tattara tarkacensa ya bi steps zai haura sama

Kamal ya sheke da dariya yace an dai yi baiko ya zakayi rana za a saka Dan ubanka,Spark Yana bin steps yace sai dai a daura da ubanka,Ubana? Yeah you heard me clearly a daura da Ubanka, Kamal yaji haushi amma ya zaiyi da Dan uwansa abokinsa Kuma yasan halinsa ba wata rayuwa yayi a kasar Nan ba sosai shi yasa yake wasu abubuwan ba tunani,bashi da mutunci ko na kobo,Kamal kwafa ya ja tare da mikewa zai tafi sai ya tsinci Muryar Spark yace kazo upstairs,Yana fadan haka ya juya,Kamal kamar bazai je ba dai sai ya hakura ya haura sama, Saman lafiyayyen bed dinsa na alfarma suka zauna,kawai spark Yana daukan wayarsa yaga sakuna suna ta shugowa ta WhatsApp,budewa yayi sai yaga Asmau ce ta turo Masa pics dinta sun fi ashirin Nan take yayi cilli da wayar ya kwadata da kasa tayi kwatsa kwatsa, yace zan iya kashe yarinyar nan,can you Imagine,Kamal ya rude ya zaci wani Abu ne babba yace me tayi,pics ta tura min sunfi 1million shegiyar yarinya mayya,to taga handsome ba dole ta rude ba cewar Kamal.

A dinga sharhi pls bana son godiyar nan da stickers ni Kam 😅

BOOK 1

Free pages

300 ne ga me bukata

Accnt no
0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank

Katin MTN
08061929616

Yan Niger ku nemi
+227 90 79 59 39

AsmaBaffa
[12/4/2023, 1:28 PM] AsmaBaffa: 🏫 TANTIRIYA 🏫
A GIDAN TARI

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA
GAREKI❤️
AIDA MAMAN TASNIM

11-15

Page naki ne
BESTYNBEELAT

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/J0ZFfbvon6ZGASEYAwZX5s
*Ina mata yan gayu yan kwalisa*
*Ina iyayen da suke so yaron su sufito fes*
*Albishirin ku kuzo gidan sauki da rahusa anan za a share hawayan ku*
*Munada kaya masu inganci nagarta gakuma sauki kayan mu sune kamar hak*
*Atampa*
*Les*
*Abaya*
*Sleep dress*
*Shoes*
*Mayafi*
*Hand bag*
*Misk*
* ETC*

MASU AUDIO BAN AMINCE A JUYA MIN NOVEL BA IZINI BA PLEASE.

Hannu Spark ya mikawa Kamal yace bani wayarka ya mika Masa ya danna wasu numbers yace a kawo Masa sabuwar wata waya wacce taci uwar iphone a tsada da komai,ba ko Ina ma aka San da irin wayoyin ba,a wani kwali take kamar kwalin turare,ba a dade ba aka kawo Masa ya cire layikansa ya Maida cikin sabuwar wayarsa ya mikawa Kamal yace jefa a Dustbin,Kamal yace kana raina min hankali wlh, ai bata wani fashe da yawa ba sabo da almubazzaranci sai a jefa a shara a siyar da ita kayi sadaka da kudin ai yafi,harara ya aikawa Kamal yace ance banda kudin sadaka dalla ka bawa me so bana bukata, Kamal yace an gama ni Ina so tsaf zan gyarawa budurwa ta,idan na bata har ihu zata yi, Spark yayi dariya tare da furta Dan gargajiya ne Kai ai,suka fara hira da surutunsu na abokai a haka Kamal Yana hakuri sosai,Spark yace wai wani ne ya kawo min aiki kaji kudin kuwa ya raina min hankali, Kamal ya kwashe da dariya,Spark baya dariya shi a rayuwa sai tayi bala'in kamawa kullum a Shirin masifa da rashin mutunci yake, yace ai wlh gwara na zauna kullum nayi ta danna ashar,Kamal ya saki dariya yace wannan Dan rainin hankali ne,Spark yace Allah yasa banyi signing ba Kuma kasan company ne,better cewar Kamal haka suka ta hirarsu ta abokai.

Washe gari Monday sai 11am Mummy ta kirashi a waya bai daga ba sai lokacin da ya tashi a bacci, yayi wanka ya shirya tsaf cikin kana Nan kayansa na kirki Yan gaske kana ganinsa kasan ba pure Dan Nigeria bane,ya fito ya Sha kyau Yana kamshi tare da taku cikin kasaita ,da gudu Securities suka bude Masa bayan motar da suka ga ya nufa wata bakar mota,Yana shiga bayan motar shi kadai sai driver,Wata motar securities dinsa suka shiga suka wuce,a hankali yace gidan Mummy,Driver yace okay Sir, Yana hakimce a bayan mota Yana kallon gefen titi karaf ya hango wata budurwa tasha gayu tana tafiya wata tsohuwa tukuf da kyar take tafiya tazo wucewa da abincinta a kwano tana tsaye tana ci,jiri ya kwasheta tayi sauri ta rike budurwar, a haka hannayenta da manja ta shafawa matar manja a Jikin kayanta, budurwa ta saki wawan ihu ta juyo tare da shararawa Tsohuwar Mari ta hankadeta ta Fadi da abincin nata,Nan take Spark yace da driver kayi parking a wajen waccen matan,driver yayi sauri ya tsaya a hankali ya karaso saitinsu sannan yayi parking,Spark ko gama parking ba ayi ba ya bude mota ya fito, nan take budurwar data juya baya taji an fisgota da mugun karfi sai da gwiwarta taje kasa,ta mike zumbur kawai taji Mari ta ko Ina kamar ba mutum bane yake marinta ta zaci Tsohuwar data mara Aljana ce itace ta rikide haka ta dawo namiji saurayi kyakyawa,kyawunsa data Gani ta tabbatar sai aljani,tace iya Dan Allah ki yafe min,Iya kiyi hakuri,sai kace ubanta cikin sojojin da suke tsaronsa ya karbi bulalarsu da suke tafkar mutum da ita ya samu budurwar Nan ya zaneta tas duk sai da ya fasa mata jiki har fuskarta kafin kace me kamanninta sun canja mutane sun taru a wajen ana kallo,su tunaninsu ma kanwarsa ce sabo da yanda ya zaneta,yace mahaukanta jahilai kawai tsohuwa dan ta rikeki zata fadi mummuna irinki ma har wani yanga zakiyi,wahala tasa budurwar ta kwashe takalmanta a hannu ta zura da gudun tsiya tana kuka har tayi gaba sai ta dawo tayi reverse ta juya sai hanyar gidansu Inda ta fito.

Tsaki yaja ya juya ya Kalli Tsohuwar dake yashe a kasa tana ciwon kafa da kyar take tafiya,zuwa yayi ya dagata yace Iya tashi,ku ma tsofaffin nan bakwa ji wasu duk Kuna da gata sai ku fito titi Kuna wulakanta kanku,Tsohuwar tace Dan nan Allah Maka albarka na gode wannan ba yinka bane yin Allah ne,shi ya turoka ka rama min, na tabaka da Alheri wajen Dana nazo tunda ya taho cirani yau Shekara biyu kenan bai dawo ba babu aike ba waya,ya manta Dani uwarsa,shine abokinsa ya taho Dani wajensa ka ganshi can ma shine ya bani abincin nawa Allah ya Masa albarka, Spark yace Uhm tsallakawa zakiyi wajensa? tace ae Dan Albarka,kawai Spark ya dauketa kamar ya dauki tsinke ya tsallakar da ita,ya zaro kudade sababbi Yan dubu dubu Bai ma irga ba ya bata,ya juya abinsa,tana Masa godiya ko waigowa baiyi ba ya koma mota suka Kara gaba.

Gidan Mummy ya nufa ya isa gidan cikin takunsa na mazaje masu ji da kansu,gidane na alfarma me tsari Wanda ba kowa sai masu gadi mutum biyu,Yana parking masu gadin suna gaishe shi ko kula su baiyi ba ya dai mika musu hannu kala bai ce ba ya wuce abinsa,Wani Babban mutum ne ya fito Wanda yasha wankan shadda da alama me gidan ne zai fita shima, Clashing suka yi da Ashraf Spark kenan Nan ma bai kulashi ba shima Alhajin bai kula Spark ba kowa ya wuce abinsa ba Wanda ya nuna alamar yaga wani,direct part din Mummy ya nufa,har yayi nisa yaga bai dace ba sai ya juya ya samu me gidan Yana bude mota yace Ina Kwana Daddy,Ko kulashi dattijon baiyi ba,shima sai juya abinsa ya tafi wajen Mummy, sallama yayi a katafaren palonta ya shiga Wanda kamshi ke tashi ta ko Ina,tana Dining cikin shiga ta alfarma cikin Less me tsada white and Golden,Ransa a hade ya isa wajenta yace good morning...kanta ta dago a hankali ta kare Masa kallo sannan ta hade rai itama
Chapter 12 · 0% Book details