Sashe 33
Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aka basu takardu suka yi signing sannan sauran duk suka fito suna Murna suna sauri Yan uwansu suna jiransu a bakin gate za a dauke su,amma Chikar Gayu ba Wanda ta fadawa wai mamaki zata bayar, ta ratso cikin ma'aikatan tana kwambo tana wani bubbudawa sai kace Soja tana gadara tace ko za a Maida ni ne eiyeee? ba wani shege da ya isa Allah ya fitar dani waye ya isa, E choke you? Ta tambayi wani Ma'aikaci yace akan me? tace ba Wanda ya isa,sai data tsaya ta kwaso shoki yafi a irga ta cashe ba kida tayi kida da baki ta taka rawa sosai tayi fitsararta suna kallonta,duk wani Dan iska suna kallonsa basa kula mutum,Rafeeq ne yayi parking da mota ya fito yazo wajen Spark tun a mota yaga an fitar da wasu Chikar gayu ta taho zata fice waje,da Gandroba a bayanta zaiyi waje da ita amma tana wani mamar mamar da duwawu a haka take tafiya,shi Kuma Rafeeq a motar kida yake ji me duka yace ah yarinya Kya yi rawa wannan masifar gida ka fito ai kayi abinda yafi rawa sai ya karo mata vol ya bude motar ya fito, Chikar gayu ta gama iskancinta ta Kalli Rafeeq ta Harare shi tace Kai dalla matsa da motarka zan wuce hanya tayi min kadan yau,tazo gaban masu gadi tace a bude min gate wajen shigowar mota,hanya yau ta min kadan,sun Sha kunu tace ko za a Maida ni ne? tabi ta kofar da mutane ke wucewa tace to nace tayi min kadan na kasa wucewa, basu kulata,sai da ta gama iya shegenta ta fice,tana fitowa tace wai wai ta Ina zan gane hanyar gidanmu ma haka ta shiga napep tace Me Napep fara zaga Kano Dani kafin ka kaini tasha na shiga motar Kaduna garin Gomna gidan ubana,yace a zaga Kano? tace da uwar kudina Kai karka min akuya.
Spark ne ya fito Rafeeq yace yanzu naga wata Yar iskar yarinya Yaya an saketa wannan Yar ta gama kangarewa kaga yanda take girgiza tab,Spark yayi dariya yace nima Jamilu Yana ciki ya buwayeni,kasan matsalar namiji ne wlh sonshi nake? Rafeeq ya bude baki,Spark yace hmm bala'in ma da nake gudu idan yazo ko Hira muke yi sai na mike kamar me, Kuma Karin bayani idan banganshi ba bana iya bacci,Rafeeq yace again dai? yace baza ka gane ba Kuma idan ya rike hannuna dadi nake ji,Kai komai yayi birgeni yake wallahi, idan na ganshi da wani sai kishi kamar zan mutu sabo da kishi,Kai ko 'ya mace ban taba sonta haka ba a rayuwa,gashi kullum so nake na kaurace Masa ko zan samu sauki amma bazan iya ba akansa zan iya batawa da kowa,Kuma bana gudun abin kunya,Rafeeq yace Ina girman naka yaya? Kai da kake respecting kanka? Jamilu ya ruguza komai,Kai In Kai Maka karshen zanci sai abinda jamilu yace shi nake yi yanzu,idan yace yi kaza haka zanyi, Yaya Ina masifar taka? Ta gudu babu girman Kai babu duk Jamilu ya sauke min shi, Kai ni yanzu ma na sake fahimtar rayuwa na nutsu,yanzu idan na fito kowa zaiga na nutsu masifar da take afka min tayi yawa.
Yanzu Rafeeq yayanka zai zama Dandaudu me son namiji Dan uwansa Ina tsoro kar na mutu a kaini yankin annabi Lut, Rafeeq yace Allah ya tsare inshaallah zamuyi ta addua Allah ya rabaka da Jamilu, Jamilu ya zama annoba,Spark yace ku samu malamai ku basu sadaka a tayani da addua Jamilu nake so namiji,da zai aure ni murna zanyi,yanda zan biya Sadakinsa ko mace Bata isa takai Jamilu tsada ba a wajena,Rafeeq abin yafi karfinsa ya bude baki,yace Yaya ka daina fadar haka yace gani kuke wasa nake abin Nan wlh bro bana wasa bane da gaske nake son Jamilu Kuma tsakani da Allah amma Jamilu Sam yaki ya yarda Dani Ina sonsa Idan yazo ma na fada Masa sai ya dinga dariya wai wasa ne.
Rafeeq yace abin Nan sai an dage da addua fa, Spark yace shine mafita,wata hirar suka shiga sun gama ya karbi sakonsa ya koma ciki Rafeeq ya tafi.
Spark Yana komawa ciki ya fara dingishin karya yana furta wash,da Jamilu suka hadu zata tafi kallon ball a filin wasa,tana ganin Spark taji wani Sanyi a ranta ta karaso Inda yake tace me ya sameka? Yace daga asibiti nake kafata ce take ciwo Likita yace naje ayi mata ruwan zafi sannan a mata tausa,Jamilu ya rude yace muje bari na karbo ruwan zafi,Spark yaji dadi yace Ina jira kazo ka tafi dani,Naila ta fyalla da gudu taje ta karbo ruwan zafi a cup tazo ta rike hannun Spark tace muje sannu,Yana dingisawa tana cewa sannu, suna zuwa Palo ta zaunar da shi a Palo Saman kujera tasa karamin towel dinsa a ruwan zafin sannan ta zauna a kasa sosai taja kafar tare da dorata a cinyarta, ta Dan dage kafar wandon,farar kafarsa tana shining ta bayyana,tace Nan? Yana wani numfarfashi yace ae nan wash zafi,wayyo zafi,Naila ta Kalli fuskarsa yanda yake yatsina tace Dan Allah kayi shuru haka haba sai kace ka samu Badon mace kana ta wani ihu wai Kai ajebo, dariya ya boye ba shiri, tace Allah ai Kaine ka bari ka adana ihunka sai kayi amarya sai kayi abinka ko Mimanka da Daddynku bazai hanaka ba,Spark yace Allah? Naila tace ai birgesu ma zakayi suce ashe dansu gwarzo ne, yace to Allah ya kaimu tace Ameen.
Dama baiso ya tafi yawo yafi so suyi ta zama tare, haka ta Kai har dare a wajensa tana faman jinya ya hana Jamilu sukuni da wayyo wayyo kafa,dare yayi yace bazai tafi ba,Naila Allah yasa tana period Bata sallah period dinta na biyu kenan a gidan yari, zai kwanta ya damu Jamilu muje mu kwanta,Jamilu Ido ya raina fata,yace Ni zan kwana a Palo, Spark yace dalla bro wai mene haka muna abokai me zai faru ne wai, Naila tana gudu kar ya ganeta haka ta bishi bedroom, ya kwanta a gefe daya,Naila sai zare Ido take yi tana faman zaga gadon tana Jin tsoro tana addua a ranta tace Allah ka kawo min mafita kwanciya da namiji a gado daya babu aure taya zan iya,ta dinga zaga gadon,Spark tashi yayi ya sawa kofar key,Naila kamar zata yi kuka,yace nifa nafi son wajen su Malam Jilani yau Ina da daukan karatu, yace Jamilu wai mene haka sai kace mace wai,Naila da sauri tace ka daina ce min mace tam ta lallaba ta hau can gefe karshen gadon tana furta wayyooo a hankali yanda bazai ji ba, ta kwanta dai tayi shuru tana karanta wasikar Jaki,Shima Spark Yana kwance ya wani baje daga shi sai gajeren wando,Naila kasa kallonsa tayi da kyar take iya hadiyar yawu,yawun bakinta ma ya kafe,Spark Yana kallon Jamilu duk abinda yake yi, ranar Naila kasa bacci tayi,idan Spark ya farka zai lalubeta yaji sai yaga idonta a bude tarrr sai ya koma ya kwanta,
Sai 3am yayi tunanin tayi bacci ya tashi a hankali zai duba ya taba yaji sai Muryar Jamilu yaji yace kaima ka kasa baccin ne? Da sauri ya koma ya kwanta Yana Jin haushi yaki bacci,ranar a haka suka kwana ba Wanda ya runtsa.
Washe gari ta riga shi tashi baccinsa yayi lokacin ita Kuma ta gyara ko Ina fes ta siyo musu tea ta gama kawo komai,ya fito shirye yayi wankansa cikin jallabiya fara me tsada, Naila taga wani kiba yake karawa da kyau sabo da baya fita ko Ina, tace mu karya nima wanka zanyi ka Ara min kayanka na saka wai duk Dan ta fitar da shi daga zargin da yake mata,yace to da sauri wai irin zai kalli jikin Jamilu, tunaninsa jikinta zai nuna a kayansa,sai lokacin tace Good morning,yace whats Good about the morning? Yaja tea dinsa suna Sha,tace ya naga kafa har ta warke? Ya manta ma jiya yace kafa na ciwo,yace Ina tashi naji ta warke.
Sai da suka karya sannan Naila ta shiga toilet dinsa yau ma bata wanke wajen boobs dinta ba ta bar mannewar da tayi bayan ta gama ta shirya ta fito da kayan jikinta,yace kace na ara Maka kaya? Jamilu yace barshi kawai na fasa, Spark tun Yana so ya gane ma har ya gaji ya hakura.
Maman su Asmau ce ta zauna tare da yarta kanwar Asmau a daki suna kuskus tace Kinga wallahi ki rabu da zancen Spark din Nan idan ba so kike Daddy dinku ya gano Ina da sa hannu a kashe Asmau ba,Kinga ki rufa min asiri,nayi zaton Yar uwata ce zata ce a bawa Spark ya aura sai kawai tace Asmau sabo da Asmau tafi ki nunawa a fili tana son Spark,Yar kishiya ce fa Asmau, hauka nake na yarda wata banza can ta auri Spark yaro me kudi da arziki gaki Yar da na Haifa Dan uwanki wata banza can sabo da na riketa a dinga cewa ta zama kamar Yar uwa,wlh karki sake a gane, kin san million biyu na bayar aka kashe Asmau,Kanwar Asmau tace ni wlh Ina son Spark idan ba a fito da shi na aureshi ba nima mutuwa zanyi,ni Ina ruwana ni nace kisa a kashe Asmau ai gwara kiyi kokari ma a hana auren amma kisa aka kashe ta ni Ina ruwana kawai ki San yanda za ayi a fito da Spark na aure shi duk duniya Nafi kowa son Spark ato idan ba haka ba na tona miki asiri.