← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 98

Sashe 7

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Matasa suka tasa Hashimu gaba da tsokana ana cewa matar Hashimu ta samu ciki,Ashe Hashimu yasan hanya,mata ma sai gulmar suke a gidan biki suna cewa oh ikon Allah wannan waje ko mahaukaci Yana gane shi wai matar Hashimu Dolo da ciki,lokacin Iyayensa wasu Yan bindiga suka harbesu a hanyarsu ta dawowa daga Jos sunje ziyara,tunda Hashimu ya rasa iyaye sai ya siyar da shanunsa kaf ya tafi birnin kano ya siyi gida a can suka zauna da matarsa Kubra ba uwar sana'ar da yake har suka cinye kudin shanun tas,gadonsa duk ya siyar suka cinye kudin a ciki,ya koma sai dai mutanen unguwa su dinga taimaka musu.

Wahala data ishi Kubra sai iyayenta suka siyar da sa aka bata jari kawai ta fara sana'ar siyar da kayan Miya a gida sannan ta shiga makarantar yaki da jahilci,macece kyakyawa ajin farko fara tas,shi Kuma Dolo Hashimu Yana da Dan duhu amma kadan amma kyakyawa ne sai idonsa tsulun tsulun a ciki Kuma duk dolancine ya Maida shi haka,ita dai Kubra jajirtacciyar macece mace me kamar Maza ga zafin nema,a haka tana karatun Nan bayan ta haifi danta na farko Mohsin kyakyawa fari amma ba can ba sai kyau Kam akwai shi ba karya,tana yin arba'in ta biya waec da Neco ta zana jarabawarta,Kuma data fito tayi kyau sosai.

Lokacin ba wahalar samun school da wuri ta samu college a nan tayi NCE kamar wasa kawai sabo da taga mijinta mutum mutumi ne,lokacin Kuma ta haifo yarta ta biyu sankaceciyar gaske kyakyawa ajin karshen karshe fara karkar da ita tsakanin Naila da Mohsin ya Kai Shekara goma,ranar Suna taci Naila.

Bayan Naila ta cika Shekara Uku a duniya Maman Kubra ta rasu sai babanta Affa ya auri wata matar Sahura me kirki,gasu basu da yara dama yarsu daya Kubra,Affa ya damu ya nace sai an bashi Naila,har ga Allah Kubra Bata so ba amma kawai Hashimu Dolo yace dauketa mana ku tafi na baka ita halak malak,ba dama Kubra ta Hana tunda Ubanta ne.

Affa ya tafi da Naila can Daji rugarsu,Mohsin yayi bakin ciki Yar kanwarsa sun Shaku duk Inda zasu je tare, Naila a ruga ta taso cikin sangarta da gata sai abinda take so,Bata San babu ba Sam,Bata San wahala ba,sai dai an sata a Islamiyya da boko,babu makaranta a dajin amma sabo da gata Affa kullum shi ke kaita makaranta a kekensa can a garin tsalle Wanda basu da nisa da garin kuma babban gari ne, sai ya kaita kuma ya dakko ta da kansa a keke,ga makarantar private ce,Naila Allah yayi mata basira da hazaka har ta gama primary ta shiga secondary tana Jin turanci sosai,ga wani bature yazo rugarsu yawon bude Ido a garin yake zaune Naila ta zama kawarsa kullum shi ke koya mata turanci har ta kusa gama Secondary dinta sannan baturen ya koma kasarsa.

Naila kaf kauyen babu me kyawunya sannan babu macen data kaita shekaru a budurwa duk da wuri ake aurar dasu,Naila har cewa suke ta tsufa ba miji sai boko,duk garin babu me taurin kanta da rashin ji,tana zuwa kiwo,tana zuwa Rafi,tana Hawa sama,duk wani Abu da akeyi a kauyen itace ta daya indai ba makaranta sai ta yi, sai rashin jin masifa a gari,Sam a kauyen karatunta baya mata amfani, amma bata da karfi,ita kullum sai dai a bita sai dai ta Mulki mutane ba dai a mulketa ba haka Allah yayita da son Mulki,duk Inda ta shiga sai ta zama shugaba, sannan tafi Jin fulatanci akan Hausa duk da tana Jin hausar Kuma tana yi,har tallan fura take yi idan babu school.

Tare da mazan dajin suke yawo da wasa,yara kanana gasu Nan sai jahilci yasa ba abinda basa aikatawa,suna caca,suna shaye shaye gashi suna neman mata,sai kani ya nemi matar wa,Yaya ya nemi matar kaninsa, haka uba ya nemi matar dansa,Da ya nemi matar uba,gashi Nan jahilci iri iri sana'arsu ce a garin, duk karatun da Naila keyi Inda kasan bata San A ba duk iskancin da akeyi a garin tana ciki, banda bin Maza su dama mazan garin basa bin budurwa sai dai matan aure suke Zinar su,budurwa ta Sha,manya da yara ba maganar iskanci da batsa da basa yi.

Affa shahararren me Bada maganin karfin Maza da maganin matan da basa haihuwa a kauyen,daga gari gari ma zuwa ake wajensa,duk Wanda gabansa baya aiki,ko baya biyawa iyalinsa bukata to azo wajensa Yana da magani sadidan,dai daikune zasu zo basu dace ba.

Shi yasa da yaga Naila jajirtacciya ce sai ya koya mata komai ba abinda bata sani ba na maganin sirrrin komai ta sani,watarana itace take sallamar mutane idan sunzo sai yace ta gansu ta basu magani, Kubra wato Umman su Naila Bata ji dadin koyawa Naila wannan Bada maganin ba na karfin Maza ai lalata ya macene a matsayin Naila yarinya budurwa amma ba yanda zata yi,Mohsin ma bai so ba amma shi Baban Naila Dolo ba ruwansa shi ai anyi dai dai cewa ma yake ai gwara ta koyi sana'a.

Umma da su Mohsin
Da kannen Naila Hidaya,Aslam,da Zarah idan suka je garin Naila ko ta kansu bata bi kamar ba Yan uwanta ba,ita bata so ma suzo tunda taji suna cewa zasu dauketa a maidata birni ganin ta kangare da yawa shi kanshi Affan tafi karfinsa bai isa da ita ba shi yasa ya amince su dauketa din.

Naila fuskarta me Dan Fadi ce me dauke da hanci dan cas baiyi tsayi can ba Kuma ba gajere ba normal hanci ne da ita me masifar kyau,idanuwanta Dara Dara masu kyau,gata da gashi amma irin na Fulani yawanci ja ne ba Baki wuluk ba gashinta jaja dashi kamar na akuya duhun nasa kadan ne ba baki wuluk ba,gata da saje, doguwa ce me Dan kauri ba ramammiya ba Kuma ba me kiba ba,tana da masifar kyan diri gata fara da ita.

Mohsin kuwa School of Nursing yayi Kuma ya samu aiki a Aminu Kano,yayi gidansa me kyau na matasa masu rufin asiri ya auri budurwarsa da suka Dade suna soyayya Hanan kenan Yar gidan Dankoli,Yar talakawa ce futuk a birnin,bayan ya nutsu Yana aiki Yana Dan zuwa kasuwar kwari Yana business na shadda, a haka ya samu ya canjawa iyayensa gida me Dan kyau ya sake gyara musu shi sosai, kayan abinci duk wata shine ke kawowa a gidan,haka kannensa shi da Kubra ke daukan nauyin komai nasu har makaranta,shima Hashimu mutanen unguwa suna ta Masa fada ya samu sana'a,cikin ikon Allah an kawo turawa suna aikin wani gidan ruwa da titin kwalta sai suka ebi masu gadin man petir dinsu na aiki sabo da yanda mutane ke sace musu,cikinsu harda Hashimu shine ya daina zaman banza ya samu gadi.

Ranar da Naila ta fara bin Yan caca a garin,mata da Maza suke haduwa sai su raba dare suna caca amma bai wuce a sa Dari biyu Dari biyar baya wuce haka,tunda Affa ya ganta a ciki ransa ya Baci,ya nemi waya ya kira yarsa yace azo a tafi da Naila abin ya fara yawa.

lokacin ta zana jarabawa sun gama Neco,Naila macece me son gwaninta,tana so tayi abinda babu Wanda ya taba yinsa,ranar da Naila ta shirya saka Gagarumar caca a garin wacce babu irinta sai ta sanar ta sa Budurcinta a caca ana gayyatar kowa duk Wanda yaci ga Naila kyauta zai bare a leda,Kuma a ranta karya takeyi kawai tayi ne Dan ta Bata musu lokaci ta gudu, har shela tasa aka yi a garin, matasan,dattijai kusan kowa dake kauyen Sai da ya shiga cikin cacar har Wanda basa caca, tana so tayi abinda wani baita yi ba,ranar Kuma aka yi da yamma an fara caca Naila ta rike sandar kiwonta ta wani coge a jiki a gefe tana kallo,ana ta buga caca sai aka samu wani Dattijo Malam Ya'u ya lashe gasa, Naila tana ganin haka ta sheke da dariya tace karya nake dama nima caca nayi muku,kowa yace Bata isa ba.
Malam Ya'u da ya lashe gasa ya gigice yace karya ne wlh sai an bani hakkina,Naila ta arce da gudun tsiya da Sandarta

Ana haka kawai sai ga Mohsin yazo a machine dinsa lifan sabo dal yayi parking a gabanta,tana ganinsa bata San ma daukanta yazo yi ba tuni ya karbo kayanta a wajen Affa ya karaso wajen hanyar Inda suke cacarsu,Malam Ya'u yace wlh zamu hadu duk Inda na ganki sai na nemi hakkina, Mohsin kiranta yayi ta taho tana son Mohsin sosai,sai yace sabon machine na siya hau na danaki kiji,zata hau baya yace gaba zaki hau fa,dole ta hau gabansa,tace Yaya Dana ni naji dadi kayi sauri, ya sata a gabansa yasan a baya zata iya dirga ta fece bata Jin magana tana Hawa kawai sai gani tayi an hau babban kwalta sai birni,tayi kuka tayi ihu ta kira Affa yafi dubu amma sai da ya kawota birni dama bata taba zuwa ba tunda aka kaita can,Malam Ya'u yace wlh ko za a Shekara dubu indai Ina raye idona idon Tantiriya sai na karbi hakkina.

Sanda tazo sun Sha wahala da ita da kuka da zagi da masifa sai ta koma kauye,gashi Anki yarda har ta hakura ta saki ranta,daga zuwanta ta samu samari amma duk ta kore su wai lallai sai sunyi bleaching sun koma farare.

Umma Kubra tana da Kawa Hajiya Tagwadas a layinsu,sai watarana Tagwadas tazo tace tunda Naila ta Dan kusa wata guda a gida ta bata aronta zata rakata Abuja gidan Yan uwanta su gaisa, masu kudi ne,daga can ma watakil Naila ta samo miji,ai dama Kubra sai murna taji masu kudi tace ba komai zata rakaki,Naila tunda taji wai zata yi rakiya Abuja har sati biyu tace baza taje ba,Mohsin ma yace gaskiya a'a amma Ummansu Kubra ta nace ita zata tsine musu idan Naila bata je ba,dole Mohsin ya hakura yace Naila taje,shine Naila ta shirya yau zasu tafi,Umma ta shiga kwalawa kira
Chapter 7 · 0% Book details