← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 98

Sashe 45

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Direct gidan da Beauty ta basu address aka kaisu dake tayiwa masu gadi da kula da gidan magana suna knocking aka bude musu suka shiga har ciki aka musu iso,gidane na gaske part uku,ko Ina ya hadu sai kallo suke yi suka dauki daki daya su biyu,Beauty me dafa abinci wata yare Sheyi ta kira tace taje gidan anyi baki zata ci gaba da yin abinci,Sheyi sai gata nan da nan,Naila tace amma gidan nan ya hadu gaskiya Beauty suna da kudi wai dankari,Chikar gayu tace Allah ya azurtamu Ameen.
Wanka Chikar gayu ta shiga tana fitowa Naila ma ta shiga tayi wanka suka fito suka shirya cikin kaya masu sauki sauki,Sheyi tana ta girki sai kamshi ke tashi,Naila tace Ina so na koyi girke girke na gargajiya dana zamani amma bani da lokaci,yanzu idan Spark ya aure ni me zance da shi? Chikar gayu tace wlh tun wuri ki koyi girki da zaman nan haka, me kike yi baki iya ba ai kuwa zaki ji kunya,Naila tace ai yanzu na dinga dan lekawa kitchen wannan Sheyi din ta dinga koya min ko zan iya.
Ai kuwa lokacin Naila ta shiga kitchen,tayiwa Sheyi magana da turanci Ashe Sheyi ta iya Hausa ta gaske,Naila tace to maganar gaskiya Sheyi Nan da kika ganni hotiho ce,ta gina bata shiga bace ni domin kuwa ba uwar dana iya na girki gashi na samu mijin aure,ki taimaka Sheyi ki koya min su Amala irin taku da Sakwara,da miyar Ugu yake ko ogu oho muku,Sheyi da Ogbono Soup me yauki da dandanon sabulu sabulu haka,Sheyi tace Ogbno soup ce me dandanon Sabulun? Naila tace haka take mana miyar,da banku,miyar Egusi da sauran su,Sheyi tace ba matsala zan koya miki sosai,Naila tace na gode.
Kamar abin arziki Naila tace ke Yoruba ce? Sheyi tace ae kina Kashi a leda ai ko? to gaskiya ki dinga tsaftacce muhallinki,Sheyi tace ai mun waye tuni wannan sai na kauye,Naila tace haba ko ku fa amma ododuwa ku dinga tafka Kashi a leda ba tsari ku canja hali wlh,abinda kuke yi bakwa kyautawa a kasar irin Nija Mama Africa uwar Africa gaba daya,yanzu dai ki koya min girkinki iri iri,Sheyi tace karki damu kyakyawa,Naila tace Allah me kika ce kyakyawa? Yes nah Sheyi ta sake tabbatarwa,Ya kika ga saurayina zai yaba? Sheyi tace ai ko waye shi karya ne ace bai yaba ba, Naila ta tsaya tana kallon girkin Sheyi tace Spark zan ci kudinka gani nan bisa kansu Ina iyo, Naila ficewa tayi ta tafi zaga cikin gidan tana Shan kallon haduwa,Chikar gayu ta Gani tayi waje ta fice,Naila tace halina da Chikar gayu rashin daraja gidan ubanwa zata je,kafin ta rufe baki sai ga Chikar gayu ta dawo,Naila tace Ina kika je? tace yawu naje na tofar wannan gidan ai yafi gaban a tofar Masa da yawu ko a toilet,Naila tace ke anya kuwa a birni kika girma,duk kyan gida Dan ubansa ki tofar da yawunki Inda kika ga dama amma banda gidan Spark,duk shegen da ya tofar min da yawu ko na juna biyu ne bazai Kara zuwa gidana ba,Chikar gayu ce tace zo muje mu Sha shayin Wiwi,Ido Naila ta zaro tace iskancina bana shaye shaye bane,a gidan yarin kika koyi Sha? Chikar gayu tace ae wasu ne suke dafa mana ta Katanga ake cillo mana da bushashen ganyen Wiwi muna dafa shayi,Naila tace baki da hankali Chikar gayu,kina mace wannan ai na Maza ne,Dan Allah mu Sam me zaku dinga kwaikwayo Kuna koya a rayuwa, Chikar gayu tace iyye ke wata ta kirki ce kin gwamitsa da kartai ba gwara mu ba,Naila tace Chikar gayu ki kiyayeni aiki na kawoki ki min in kin gama Spark zai biya kiyi abinda ya dace za a biyaki,Chikar gayu tayi dariya tace cinikin biri a sama,dariya suka yi Naila ta furta gaskiya beauty tsakani da Allah tana shanawa Bata da Yaya bata da kani,Chikar gayu tana ji tace yo ai ni da babanta ma zai so ni duk katon cikinsa tarairayar kayana zanyi, Naila ta sheke da dariya,Chikar gayu tace wlh tumbin Baban Beauty bala'i wai gashi da cin tsiya yazo mana visiting watarana Kinga yanda yake cin abinci kamar wani zai kwace kamar ba me kudi ba, inda kisan kura, Naila tace ni bama haka ba sai hakoransa na tsakiya daya cire fafaroma, hakora dai suka fice yo ai ba daya bane biyu ne ko uku ya Ilahi nace da kudinsa ya sa na roba mana,Zo Kiga Beauty yanda take kuka tana ce Masa Daddy ni ka saka hakora wlh idan zaka ce s din nan dariya kake bani,Naila tace ke Chikar gayu da munafunci,to Kuma mu ai kowa kallonsa muke tsaf, ko zaren dinkin shaddar mutum ma sai mun kalla.

Palo suka koma ta zauna Chikar gayu taje ta dafa shayinta na Wiwi ta dawo da abinta a cup,Naila tace shedan yau aiki zaibi ta kanka Chikar gayu kiyi Bismillah kafin Kisha shayin Wiwi din nan tunda shedan komai za aci sai yazo ya tsoma baki, Maza ki Masa bakin ciki kar ya Sha miki dadi,Chikar gayu tayi Bismillah ta fara kurba tace ai da ta hayakin nake Sha bazan Bismillah ba zan fara zuka sabo da shima shedan ya zooka ya shake a makoshi.

Chika tana zuka Naila ta kwace ta hankade keyar Chikar gayu tace ke a gidan yarin har wiwi kika koyo sha? Da Allah ku dinga sanin abin kwaikwayo,mene wani Wiwi kina mace dan Allah ki bari ki gama min aiki na lafiya idan yaso daga baya ai Kya Sha abarki,taje ta zubar,Abinci suka ci sannan suka kwanta suna hutawa.
Zuwa dare Sheyi ta Dora girki ta kira Naila tazo ta koya Naila ta shugo kitchen,tukunyar ta leka tace yawwa ai na gane wannan girkin miyar Egusi ce ko zamu yi,yawwa Sheyi idan kika wanke namanki sai ki watsa a tukunya Yana tafarfasa Yana zabalbala sai ki yanka albasa Sheyi ki barbada curry da Maggi,Maggi ki samu me karfi yanda zai bada dandano,ki dakko manjanki idan ya daskare ma ba matsala duk daya Sheyi.....Sheyi ce ta tadakatar da Naila tace ni nake koya miki ne ko ke kike koya min? Naila tace kece mana ai practical nake,Sheyi tace ki tsaya ki koyi Abu idan kinki ke zaki ji kunya a gidan miji,Naila tace Allah ba yasa ba bakinki ya biki, yanzu na tsaya nuna min,Ehem haka zaki ce Yan mata,Sheyi ta shiga koyawa Naila girki har suka gama tare Naila ta gane yanda zata yin miyar da tuwo ko Sakwara ko Amala etc.

Chikar gayu tana Palo tana kallon tashar wakokin Nija,a haka Naila ta dawo ta sameta ta zauna tare da yin shuru ta lumshe Ido tana Jin wakar tace na Lula tunanin Spark gamu can mun fito daga mota mun shiga shopping mall Yana rike da hannuna,gamu can na rakashi Office...muna soyewa a cikin Office,ya dannawa kofar key, yasa key Chikar gayu,gamu can ya kaini awon ciki asibiti mum fito a hadaddiyar mota,ya tafi dani aikin hajji,Gani ga ka'abah,daga can mun wuce America,laaaa snow.....na haihu a can mace na samu,Chikar gayu tana kallonta ta rufe Ido wai tunani take yi,daga Jin kida sai haihuwa Kuma,Naila tace baza ki gane ba,ni nasan me nake ji na rashin Spark Ina zan ganshi?

Ranar haka suka kwana Naila tana zancen Spark Ina zata ganshi,washe gari bayan sunyi Kari me kyau Chikar gayu ta dakko kayanta kodaddu jemammiyar atamfa riga da zani dinkin me Fadi ta saka tayi daurin zani me Bakin almakashi gefe ya zobe baya a dangale ta daura dankwali dan kanti, ta fito da kullin kayanta a leda viva ta rungume a kasan hannunta,tace to matar Spark kira Hajiya Tagwadas,Naila tace ai sai ta gane Kuma na fito a gidan yari.

Nari kiji ta jawo wayarta ta kira Mohsin ya daga tana jinsa suna fada da Hanan ita magungunan basa yi ciwonta yaki warkewa ya maidata asibiti,Naila tace kaga kyale wannan banzar ka kira Hajiya Tagwadas kawar Umma kace address din gidan Mima kake so sun kiraka Abuja akan case Dina,Mohsin yace to ya kashe ya kira wayar Hajiya Tagwadas,tace Dana Mohsin Allah ya Maka albarka Dana Mohsin,Kuma gashi har yanzu naga Hanan taki ta sake haihuwa ko planning take ne?,Mohsin yace kaji gulma a ransa,a fili yace uhm Allah ne bai kawo ba,to Mohsin ko aure zaka Kara? Mohsin yace haka nace miki? a'a wai dama akwai wata ne da nake Maka sha'awarta a makwaftanmu Iklima yarinya me hankali,bana sonta komai hankalinta Mohsin ya furta yace address zaki bani please zanje Abuja an Gayyace ni akan case din Naila ance naje gidan Mima,gidan Ahmad Maleek,Hajiya Tagwadas tace to bari na turo Maka a rubuce ai yafi Mohsin Dan Albarka,yace Ina jira na gode.

Mintuna kadan ta tura Masa a rubuce shi Kuma yayiwa Naila forwarding,Nan take ta mikawa Chikar gayu tare da kudi 3k tace ko me kika gani ki kirani,Kinga maganin nan dana baki ki tabbatar idan kika ji Ashraf zaizo gidan to kisa Masa a abinci yaci shike nan Hallare Kuma sai idan ni naga dama na tashe ta,Chikar gayu tace an gama zanci uban kowa,Naila tace kiyi ba komai yi nane ni na saki a kotu harda wani zuwa suna Jin sharia suna kallo aka daure ni,Allah ya tsare.
Chapter 45 · 0% Book details