← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 98

Sashe 41

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har ta fice sai ta dawo tace in tafi banyi komai ba ai karya ne Hanan ce fa a gidan,Glass ta hango na Hanan da take daukan wanka wani pink faskeke ta dauke shima tace kolabo zan fara,yanzu na koma yar kolabo Kuma,sai ta haska kafar Hanan ta ganta a kumbure suntum,ta haska idon kadan kamar an kawo wuta an dauke ta ganshi tsabar kumburi ya manne ma da kasan idon,Hanan tayi dariya marar sauti harda rike ciki duk ba sauti,tasa hannu ta latse idon Hanan,Hannan ta farka a tsorace tana cewa wayyo idona wayyo Naila ta fisgi kafar me ciwo wacce ta kumbura ta ja da karfi ta Murda ta saki ta fice fit, Hanan ta tashi tana ta dube dubenta shuru,ba kowa tana ta kiran Mohsin shi Kam Yana sallah .

Naila fitowa tayi ta koma ta dakko katon hijab again tazo tayi Sallah sannan ta surfa addua ta mike sanye da hijab,ta fito Mohsin ma Yana idarwa ko ta kan Hanan baibi ba ya fitar da machine Naila taje ta hau suka bar gidan ta rufe fuskarta da Hijab din,sai gidan Umma,Suna zuwa Abba ya dawo daga masallaci,yaga Naila mamaki ya kamashi Naila tana sauka a machine ta durkusa a gaban Abba tace Ina Kwana Abba,da mamaki Abba ya amsa da lafiya Naila tayi kasa da Kai wai tayi hankali a gidan yari, tace mun same ku lafiya ya akaji da rashe rashe da bama nan,Abba Dolo yace ei wlh nan rannan ko sati ba ayi ba Magajiya ta rasu,Magajiya Babar Sani Takwashe,na manta ma Alhaji me kosan sadaka da watan Ramadan shima ai ya rasu,haka ladi me abinci ma,Naila tace Allah yaji kansu,Abba ya su Debora,Abba yace suna Nan suna fama da kallon Maza yanda kika sansu basu daina ba ni yanzu ma kullum sai na karanta Hasbinallahu kafa Dari sabo da gubar da ke cikin idanuwansu Allah kareni dasu gashi nan duk da haka ramewa nakeyi gubar idon su Debora ce kawai tayi min yawa,Mohsin yace Abba ka rufa mata asiri muje Dan Allah gudowa fa tayi.

Abba ya saki salati yace gudowa? Duk tsaron Dake gidan yari kika iya gudowa Naila, Gwara tun wuri ki koma ciki kafin su damke ki,wannan ai cin amanar kasa ce,cin amanar hukuma ce, duk da naji dadin ganinki gwara ace su suka sallameki da kansu, Mohsin yaga abin na Abba ya zarce saninsa yace Kinga muje ciki,Naila ta mike zasu shiga Abba yace Allah ya tsare Naila amma Ina jiye miki,Umma kuwa da katon cikinta Wanda ya girma suka sameta ta kafa wutar gas a hancinta tana Kona wata takarda wacce take nannade da tabar Wiwi,tana shakar warin da sassafe,Mohsin yace Umma Zafa tayiwa Dan cikinki Illa wallahi,to kawai sai na kashe kaina akansa? ku rabu Dani,Naila ce ta shiga ta kwace wiwin ta take da kafa tace Yar kanwar mu ko kanin mu zai iya zuwa da nakasa,Umma tace laaaa Naila ta rungume Naila tana murna tace ta ya hakan ta faru,Naila tace irin tserewar,Umma tace tsugunu bata kare ba,ai wucewa zanyi,zuwa nayi na ganku dama ,kina da wajen zuwa ne? Naila tace Inshaallah akwai mafita ku dai kuyi min addua,Umma tace to shike nan Allah ya tsare a Kuma tsare mutunci a kiyaye,Banda taurin Kai,Naila tace to ayi a bani shayi na Sha,Mummy ta duba flask tace akwai ruwa,da sauri Naila ta hada tea ta shanye tace idan su Hidaya sun tashi ku fada musu na fita daga gidan yari Umma,My love zan wuce ina da number Dinka a kaina zaka jini Inshaallah,Mohsin yace to Ina jira,leda ta dauka tare da zuba kayan data dakko na Hanan dalayin wayar Hidaya ta karba

Naila ta nufi kofa tace to sai kunji ni,Mohsin Tausayin Naila ya kamashi,da sauri ta fice tana ficewa da hijab din Hanan har kasa ta tsaya a zaure tayi kuka sosai ta goge hawayenta,sannan ta nufi titi da sauri ta shige Napep tana barin layin yaran Dan Indo suna zuwa gidan su Naila,su Umma sai hani suka yi Yan daba sun fado musu gida suna bincike,basu kula kowa ba Kuma ba Wanda ya kulasu suka gama dube dubensu sannan suka fice suna duba wayarsu har gidan Mohsin suna zuwa sai Hanan kawai,Naila a Napep ta saka layin Hidaya a wayar Hanan data dauka,ta zauna tana tuna number Spark ko wacce ta kira sai dai taji wani ko wata ya dauka tayi missing number a ciki ba daidai take hadawa ba,tsaki ta ja ta hada number Beauty ta kira Allah ya taimaka wannan daidai ta hada bugu biyu aka dauka,Beauty cikin Muryar bacci tace na'am waye? Naila tace Jamilu ne,na gudo daga gidan yari bani address na gidanku,Zumbur Beauty ta mike tace ka bawa me napep din waya,Me Napep ya karba Beauty ta Masa kwatance sosai sannan ya mikawa Naila wayarta,GRA ya shiga da ita wata katafariyar unguwar,hadadden gida na mamaki a nan yayi parking yace ga gidan Nan nasan ma me gidan ai yayi fice,Naila Hijab dinta ta cire ta dawo namijinta sak,Beauty ta kira a waya tace muna kofar gidan,da sauri Beauty ta fito ta biya me napep kudi ya tafi,Naila ta gyara p-cap tace muje ciki suka shige,bangaren Baki ta Kai Jamilu ta bashi daki sannan ta koma wajen me aikinsu tace ta hada mata lafiyayyen Kari.

Naila kuwa sai kallon gida take faman yi tace umm Aljannar duniya bari nayi wanka,ta mike ta bude toilet da komai da komai a ciki ta sake wanka na musamman ta wanke gashinta sosai ta fito,body lotion ta Gani a mudubi ta shafa tana kallon kanta a mudubi tana taje gashin nata Wanda ta warware daadaa din dake kanta,ta dinga duba tarkacen Dake mudubin harda mayukan gashi da Kuma powder da abubuwa kayan Hanan ta saka a jikinta har sun so suyi mata kadan sabo da Naila ta fita kiba ta cika kayan fam fam,ta zauna ta shafa powder harda saka maroon jambaki tayi kyau kuwa sosai kuma tayi daurin ture kaga tsiya ta tsaya a mudubi tana kallon kanta tace amma fa Allah yayi halitta haka nake dama....bayanta ta juya tace wai wai gaskiya Alhmdllh better thing,Ashe haka Allah ya halicceni, Allah na gode Maka dole in godewa Allah ahhh kalleni Naila,Jamilu, Tantiriya dariya tayi tana shafa fuskarta a haka Beauty ta shugo ta isketa,wani wawan birki taci da tire a hannunta tace me zan gani Jamilu?
Naila hankali kwance ta juyo ta bankaro mata kirji tace Kalli kirjina me kika gani? Beauty tace nono,tace mashaallah to Allah ya albarkace ni da su gasu Nan mashaallah,Kinga kina da su kema,bani bra na saka ma,Beauty tace dama Kai mace ne Jamilu? Naila tace wlh haka Allah ya nufa ko na cire wando ki gani? Beauty da mamaki tace ya akayi kika zauna a gidan Maza.

Ni mamakin ma da nake da ka iya kallo na ba kunya ba komai kace macece,wai baki ji nauyi na ba? tsakani da Allah daukanki nayi da har zanji wani nauyinki,Beauty murmushi tayi tana kallon Jamilu mace kyakyawa tace wai yanzu yaudarata da kayi baki ji komai ba irin kunya? mene haka da suna Kunya? Menene ma'anarta, Beauty a ranta tace wannan ta fini iya iskanci,a fili tace amma kinci amanata,Kinga ki kawo min bra da abincin kawai,Beauty ta ajiye tire ta fice ranta na suya ta dakko bra ta dawo sannan ta kawo abincin Naila ta kwashi girki sannan ta cire rigarta ta saka bra ta Maida kayanta, ta shiga bawa Beauty tarihin rayuwarta da shiga gidan yari har fitowarta yau,Beauty ta tausaya tace kin bani tausayi Kuma na miki uzuri a abinda kike yi,yanzu ita Mummy din ya za ayi da ita? Naila tace wata zan samu na turata a matsayin Yar aiki gidan asalin wacce ta haifi Ashraf ni ta kansa zan fara,so nake shima ayi Masa sharrin kisa a kaishi prison,tare zamu je Abujar ni Kuma gidan ogar zanje Mummy,wannan Dan nata sai na sumar Masa da Hallare dinsa ta daina amfani zai ci ubansa,Beauty ta sheke da dariya harda shewa tace baki San ma me zaki Masa ba,Naila tace abin ne yayi min yawa sai dai naje Abuja tukun sai naji tarihinsu sai nasan ta Ina zan fara ramawa,Beauty tace to a kira Chikar gayu mana kuje tare,fitsararriya ce bata tsoron uban kowa, Naila tace nima shegiyar kaina ce fitsarriyarce,ke bani da mutunci,ni kadai ma na ishi kowannensu amma duk da haka a kira Chikar Gayun Nan da kwana biyu mu wuce idan zata yarda,amma ke zaki bamu tallafin kudi,Beauty tace babanmu Yana da gida acan da masu aiki da masu gadi kawai ku zauna a nan ba mace a ciki a banza ake gyara shi,kawai dai a samu kudi ayi miki dinki na manyan yara,sannan ya kamata ki koyi mota a can akwai na Daddy na ki dinga ara idan ta kama,Naila tace godiya nake sabo da ni kaina ban san me zanyi ba ma sai na je tukun,na fara Jin tsoron kaina Beauty Ashraf bazai ga da kyau ba,to kije musu a me kudi,Kinga baza su taba ganeki a shigar mata ba,sannan kina daukan wanka kinga kin canja salo kenan da an sanki a namiji yanzu a mace zaki fito Kuma ki boye kanki kar a gane kece,Naila tace tab ai Murya zan makale wlh ko Spark sai yayi da gaske zai gane ni,yanzu ni Kuma ya za ayi dani yaudarar da kika min? Har kuka nayi a kanka Jamilu wlh Ina hangoka a namiji me damatsa da faddan kirji, Kuma yanzu Daddy ya bani 2weeks cikin masoyana na fito da wani,Naila tace to ba sai ki zaba ba,ai Banda Wanda nake so,kiyi hakuri ki jira Kiga zabin Daddy idan bai miki ba ki fada min master planner ce ni sai an rushe auren.
Chapter 41 · 0% Book details