← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 98

Sashe 67

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rafeeq Yana ta kallo dama abinda ya kawo shi kenan,Su Dije suna ganin Rafeeq sun zaci irin Spark ne,shima Spark din basu San sabo da Naila ya saurare su ba,Kanin mijin Tantiriya ga kanin mijin Tantiriya, Rafeeq ya wani bata rai wai kar wata ma ta so shi,ya tsani mace tace tana sonsa shi,Spark yace Kai kawayen mu ne na kauye wlh karka Raina mana kawaye zan karbe jarin Dana baka,Rafeeq dariya yayi kadan yace ai Kai yanzu Yaya sai an Maka uzuri,gaishe da su suka yi,Rafeeq ya Kalli Rayya Dake ta kallonsu tace wannan shi dai Yana da da talatu ne fura,ta nuna Rafeeq,Spark murmushi ya saki,to naga Yana ta wani yanga kamar mace,Rafeeq ya daure fuska tam, Spark shi Naila ta dauke Masa hankali tazo tana Masa rada kayi kyau ko Jin abinda Rayya kewa Rafeeq baya yi.

Rafeeq kuwa Naila ya tambaya yaushe za ayi walimar ne taku? Naila tace 3pm to 5pm sai a wuce Kai amarya,Kamal yace na taba Jin walima mata da Maza a hade,Rafeeq yace haka tafi dadi.

Bayan sun tafi zuwa karfe uku Rafeeq harda canja Jallabiya da carbi a hannu na tafiya walima,Spark ya dinga dariya yace ai Kai ka fi Angon ma,idan iskancin Nan kake sha'awa kayi mana kaima,wannan masifar son mata haka Kuma kace Kai kar wacce ta soka,Rafeeq yace ai ni Yaya nafi so na kallesu daga nesa sunfi birgeni,3pm mutane suka cika a Inda aka kama za ayi wa'azi,Misam maye sai da yazo,Rafeeq ya ganshi yace Misam kana birgeni Kai kawai mata kaji dadinka,baka da control ba komai,zanci uwarka wlh sa'anka ne ni,kaima idan kana so ka fara mana sai son mata a baki da Ido, Malama ce ta shugo.

Bata fi Naila ba Yar kyakyawa da ita me Dan haske amma ba can ba,ta Sha hijab har kasa,idonta tar a kan kowa,Spark baki ya tabe yace wannan ce zata min wa'azi naji Allah bazan batawa kaina time ba ya mike ya fice, dake a ciki bangaren mata daban na Maza ma daban.
Matan su Naila duk an Sha Abaya,Maza yawanci da jallabiya,Amarya da Ango ana zaune a high table anyi shigar larabawa ta Amarya da Ango.

Malama Speaker ta dauka suka hada Ido da Misam ya kashe mata Ido daya tayi sauri ta dauke kanta dama shi da Rafeeq duk suna gaba gaba,Kuskure Malama ta sake yi na kallon Misam ya daga mata gira tare da kashe mata Ido,ya radawa Rafeeq na samu Daya yanzu Malama,Rafeeq yace cikin rada ga Chikar Gayu nan ta shugo,Misam ya basar sai bayan Dan seconds ya kalleta,Chika ta kalle shi suka hada Ido gwalo ta Masa ta zaro harshe,dariya yayi ya sake kallonta ta turo kirji gaba tayi girgiza kadan,dariya yayi a boye yace ta sake yi wai,kanta ta dauke,yace Ina Amaryar Yaya Spark ne? ,Rafeeq yace gata can mana ai wannan tafi karfin kanka sai dai Spark na sallama mata,gata can a gaba Inda Chika take.

Malama ce tayi gyaran Murya tare da sallama,sannan ta bude da adduoi,Misam Allahu Akbar ya furta sai da kowa yaji,Malama Ikhram ta gaji da iskanci su Misam magana daya tayi sai sunyi Kabbara,sun gama Raina mata hankali,Misam tayiwa magana siiiiii....siiiiii...hey ..hey....siiiiii,dagowa yayi daga danna wayar da yake suka hada Ido, fito tayi Masa ta nuna kofa da bakinta wai ya fita,Malama da fito,ko kulata baiyi ba yaci gaba da danna wayarsa,Mohsin ya radawa Amarya su Spark duk gasu da Kamala kyawawan gaske gasu da aji sai iskanci fal ciki,Beauty tace naga alama kuma kamar basu suke yi ba,sai su Fadi Abu su fuske,su Rafeeq basa saurarar Malama waya suke dannawa amma ko ya tayi magana sai sunyi Kabbara Allahu Akbar.

Malama tana Jan Aya da hadisi tana wa'azinta sosai da sosai,ta Fadi mene ma auren gaba daya,da sharudan Dake ciki,sannan ta dawo kan yanda ake zaman Aure,ake tattalin me gida da kula da shi,tazo tana koyawa Amarya yanda ake tarairayar miji dama duk irin malaman Nan fitsara sukeyi su fake da wa'azi,da Allah Amarya ayi dinkunan zaman Palo Banda zuwa a dinga manne jiki a gidan miji,ki dinga saukaka Masa yanda zai cire su cikin sauki,Rafeeq kasa kasa yace wannan fadakarwa ce me kyau dole na dakko malamar Nan har Abuja ta koyawa su Mima rayuwa,akan kula da yara da musu tarbiyya,Misam yace maulidi zamu ce zamu hada sai mu dakkota.

Chikar gayu tace wannan gaskiya ne ke Beauty kinji dai a saki a Palo su Sha iska,Malama tace ashe Kuna ganewa Alhmdllh Alhmdllh,ba ruwanki da kishiya kiyi ta kanki Amarya,me gida idan ya dawo yasha aiki ya gaji ya kamata ki tayashi cire kaya,idan ya hada zufa ki tanaji handkerchief dinki me kamshi ki goge masa gumi,sannan ki tarbe shi da ruwa me Sanyi,ko wani dan zobo haka me Sanyi,Maza suna son girmamawa,karki zo ki wani tsaya Masa kerere kamar namiji,da karairaya da kissa cike da girmamawa zaki bashi zobonki me Sanyi,idan ta kama ma ki bashi a baki,Maza suna son kulawa,Rafeeq yace haka muke Malama musamman ni,Malama ta Harare shi.

Tace shimfidar aure Amarya, Chikar gayu tace a tafawa Malama anzo Inda muke jira a bata darasi,Naila tace bari na bude kunne Malama nima Amarya ce anzo Inda muka fi wayo,yeeeee suka saki shewa mata.

Kamal yace ni dai wajen Nan Ina da mutuncina bazan iya zama ba ya tashi ya fice,Misam yace mu mun zubar da namu wlh sai naji komai,Maza matasa duk sun zuba kunne,wani har cewa yake Malama mu ba a zo kan Maza ba,tace zanzo ne ku saurareni.
Sanda ta fara bayanin kwanciyar aure Mohsin kunya ce ta lullube shi,Rafeeq yace ni dai na kamu da son Malama ta San harkar irinta nake so,Misam yace idan ka aureta zaka Sha dadi ko Mai ta iya,yace musamman idan aka fada bedroom.

Naila kuwa cewa take an gode Malama Allah ya biya da Aljanna Munji mun dauka zamu yi,Rafeeq yace Kai nima na tashi daga wajen Nan kar a rainani Chikar gayu sai raini take kawo min,Misam yace dani za a kare sai an rufe addua da Dani,Rafeeq ma ya tashi ya fece,Maza duk masu Yar kunya arcewa suka yi,Mohsin ya gaji shima badan dole ba Ina zai zauna sai dai su Tantiriya irin wajen sune,da kyar ya daure aka gama wa'azin Nan,Misam ana shafa addua yace har an gama gaskiya anyi sauri,Malama ta gasa Masa harara.

Suna fitowa aka Maida Amarya gidan Ubanta dangi aka mata nasiha sosai Daddy ma sai da yayi nasiha sosai,yace wlh idan naji watarana ko da wasa kin Masa gori na bashi gida da jari ko wani Abu ko kika yiwa kishiya gori wallahi Beauty sai Kinga fushina,na fada miki banza son gori a rayuwa,kayiwa mutum Abu tsakani da Allah mace tazo tana yiwa miji gori shi yasa Maza basa son zama a gidan mace ko gidan Baban mace,badan ke na bashi wani Abu ba,karki sake naji gori ko kiyuwa kishiya gori,Beauty tace to ko kuka itama sabo da sun Saba da gidan yari akan aure Kuma wanne kuka zasu yi,yayi mata fada Sosai sannan ya sata a mota da kansa,ga Yan uwa da kawaye,Naila har da ita a Yan Kai amarya suna gefe suna yiwa Amarya rada,Beauty tace karku damu fa ni kishiya Bata gabana,bana tsoron kishiya, gidan ta tarar sai na bata littafina dictionary na duk wani iskanci sai ta haddace shi tsaf.

Hanan Kuma daga ita sai Yan uwanta a Palo suna zaune suna jiran Amarya,Hanan tace a yau ana watsawa zan mata dukan tsiya wallahi,yau sai na daki banza,Kuma ba uwar da zai iya yi min,ai nasan lagonsa ko me nayi Ina bude Masa Nono sai Kiga yayi mukus,sabo da haka yau ma haka zanyi baza kuji komai ba,shi da nono ai Inda kisan asiri.
Dariya suka yi da shewa,suna habaici habaice tun kafin Amarya tazo.

Naila suna mota tace babu fa wata Amana da zamu bawa Hanan,kawai a wuce da ita part dinta,Chika tace Amanar Beauty ita ta isa ma mu Bata Amana har wani a fara Kai mata Amarya ita din banza,Beauty tace muna zuwa ku wuce Dani part dina,kar muje ma ta fada mana magana bazan iya kyaleta ba.
Suna zuwa manya dangi suka yi suka yi a fara Kai Amarya wajen uwargida a bata Amana,Beauty tace ku nuna min hanyar bangarena akan a bata amanata gwara na Kai kaina dakin miji wlh bazan yarda a bata Amana ta ba.

Su Naila suka ce muje ke suka tafi da Amarya bangarenta Wanda ya gaji da haduwa,suna kaita,sai ga Hanan da sauri tace ko ba a kawota wajena ba zata fito ne a banza na ganta,Dan ba a kawota ba sai me ko ance muku Ina son a bani amanarta,ko an bani Amana sai na ci,Shewa kawayen Amarya suka saki da guda,Naila tace 2+2 ga sabo ga tsoho wlh sai dai Yaya ya dauki sabo.

Amarya yau akwai harka a sakarwa Yaya jiki so nake da safe naga bakinsa kamar gonar auduka a shayar dashi zumar da ai taba Sha ba,wata Maryam itama daga gidan yari ta fito tace gobe Dan Allah Beauty idan munzo mu iske gadon nan a balle,karki ji komai ko an balla Daddy a ranar zai iya siyi miki sabo.
Chikar gayu tace an taho da ruwan zafin ne kizo ki Kara gasa wajen Nan,yau akwai Kwalbewa,Zaiji sabon ihu.

Hanan ba shiri ta bar dakin ta koma bangarenta tana huci,suna ta shewa sun cika dakin Amarya, Dattijai sai barin dakin suka yi,ba a dade ba aka kwashe Yan kawo Amarya kaf daga Naila sai Chikar gayu aka bari a gidan suna zuba iya shege.
Spark Naila ya kira yace sun wuce Abuja,tace ko sallama ai shike nan ka kyauta,to ba yanga kike min ba,ai jibi za a kawoki ne yan mata Ina Nan Ina jira,Hallare ce bana tsoronta ni,dariya yayi yace hmmmm Allah ya kaimu.

Bangaren Mummy kuwa ta samu Chikar gayu tayi tafiya sai soyayya suke zubawa da Basiru har an fara maganar aure,Mummy tace ni Alhaji zaka iya dinga zuwa gidana ma idan munyi auren nayi zamana a gidana,Basiru yace a'a a gidana zaki zauna bangarenki daban na Suhailat daban,Mummy sai murna take yi tace daga Nan sai mu wuce kasar waje,yace ba Inda bazan kaiki ba,Mummy farin ciki ya mamayeta.

Masu Sharhi Ina godiya
Chapter 67 · 0% Book details