← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 98

Sashe 31

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Su Malam Jilani sunyi kasake suna kallo,Sharu yace dakin nan idan muka yi wasa fa muna barin badala irin wannan to za a daina karbar adduar mu,Allah zaiyi fushi damu,muna kallo namiji da namiji suna soyayya Kalli yanda suke magana,Malam Garzali ne ya rufe baki da sauri yace wlh ya tabawa Jamilu fuska,a lokacin Kuma Spark ne ya shafa habar Jamilu yace babu alamun gemu Jamilu fa har yanzu,Jamilu yace ka takura min wlh zan daina kulaka, Spark yace na daina inshaallah daga yau, Naila taji dadi abinta tana murna.

Bayan kwana biyar Naila ta warke sosai Kuma tana ci gaba da maganin Infection dinta a lokacin Kuma ta fara period,Allah yasa da pad dinta ta dinga abinta ba Wanda ya sani ba Wanda ya gane ta, Kuma suna waya da Beauty sosai da Yan gidansu musamman Mohsin gashi suna ta Shirin sake zuwar mata Ziyara,Spark kuwa anzo masa yafi sau biyar ma su Kamal, ga Abinci yanzu kawo Masa akeyi kullum na dare Dana rana daga eatery, ranar Ziyara Mohsin da Umma tare da Hidaya ne suka zo ba Abba,Naila ranar Baki har kunne,wannan karon ba a zowa Spark ba sabo da shi har sanda ba ranar Ziyara ba duk Wanda yake son Gani Yana ganinsa musamman da babban shugaban gidan yari yaji Spark ya fitar da kwangilar aikin da za ayi musu na gyara gidan yari kowa murna suke ma'aikatan sosai suke girmamashi sai abinda yake so ake Masa.
Naila Kuma ganin ya sa mata ido sai ta rage shige Masa idan taje aikinta zata yi Masa kawai ta gama ta fito,Spark bai Jin dadin Hakan Jamilu Yana sa shi nishadi sai ya daina sa idon ma.

Da wayar Samsung a kwali ta fita wajen su Mohsin tana zuwa tace Yaya wayar Nan zata Kai nawa? Mohsin ya karba ya duba yace ai wayar manya ce wajen dubu Dari biyu ce,tace taka ta hannunka nawa ce? yace dubu tamanin tace to bani taka na baka wannan,Mohsin yace Kai sis ni da zan siya miki ke zaki bani, tace to mene a ciki kaji Yaya amma karka sake wlh ka Bawa Hanan ko pics idan tayi ban yafe ba, Umma tayi dariya tace Kai ke fa halina dake ruko, Amal kawai za a dauka itama Dan kawai 'yata ce shi yasa amma da tunda ta hada jini da Hanan baza a dauke ta ba, yarinya tayi kama damu taki duk tayi kama da uwarta hanci kamar tulu,Mohsin yace bana son sharri Amal dince me hanci kamar tulu,Spark ne ya fito, kawai Naila taga ma'aikatan sai wani girmamashi suke yi kamar wani me Mulki.

Ta kalle su tace mu wato anga talakawa ne shi yasa ba a kaunar mu,idan baka da kudi shike nan sai duniya tabi ta tsaneka,wallahi abinda kuke bakwa kyautawa a kasar nan, talaka shine abin tausayi amma Banda ku,ni da nazo munafunci na kuka dinga yi amma yanzu Kunga me kudi har cewa kuke barka da fitowa ranka ya Dade ana wani matsa Masa hanya ni waye yayi min sannu da zuwa,wani Ma'aikaci yayi dariya yace to Kai ai Kafi kowa ma farin jini tunda ka fito mutane suke Maka magana,wani yace Jamilu,wani yace Terror,wasu suce Tantiriya,yanzu naga malamai sun wuce sun kiraka da Malam Kuma,ga Yan Daudu suna cewa Dahara,to mu me zamu ce Kuma,Naila tace uhm ku dai Kunga kudi,Spark kudi ya zaro ya rarrabawa ma'aikatan wajen har na bakin gate sunzo sun karba,Naila ta kalle shi tace neman suna ne badan Allah bane,Spark ya juyo ya kalleta ya mata gwalo,dariya tayi tace wlh nima sai ka bani,takowa yayi yazo ya gaida Umma sosai harda surunawa ya mikawa Mohsin hannu suka gaisa, Hidaya sai kallonsa take kamar mayya,Naila duk sai taji haushi ta harari Hidaya tace ni ban san ma me yasa aka zo dake ba Hidaya, ki ta kallon mutane da anyi magana kice kin waye ke Yar birni.

Hidaya ce ta Kalli Naila ta harareta taci gaba da kallon Spark, Naila ta dauki tsinke ta nuna idon Hidaya da shi kamar zata zokale mata ido,Hidaya ta janye idonta da sauri,Spark ma bai San me suke yi ba Yana can Yana magana da Mohsin,Naila ta mike tace Yaya Mohsin bani wayar mana,ya zaro wayar tasa Yana zaune Yana kokarin cire layinkansa Naila ta rungumo kafadunsa tare da Dora kanta a Kafadar Mohsin tace Sweetheart,yace matsa Dan Allah,Naila tace sai na Dana nima yanda Hanan ke yi,Spark baki ya tsuke ya Kalli Naila wani haushin Jamilu yaji kamar ya shake shi, fuska ya daure sosai kamar an aiko Masa da mutuwa ya juya tare da Jan tsaki ya bar wajen ya koma ciki.

Bayan su Mohsin sun tafi ta dawo ciki da abincin da suka kawo mata da tarkace,bangaren Spark ta nufa direct a Palo ta same shi zaune yayi shuru Yana tunani fuskar nan ba Rahma,Ledojin ta ajiye tana murmushi tace sun tafi abokina,Spark yayi banza da Jamilu,Naila tace ga abincin yace bana ci bazan ci ba,tace Okay fine ta zauna a wata kujerar, lemo ya dauko Wanda nasa ne Yana Sha Yana cin biscuits,tana kallonsa kawai cin abinsa yake Yana Shan lemon yaki kulata, tashi tayi ta fisge robar lemon ta zari biscuits din ta gudu can wata kusurwa a dakin tana Sha,Yaji haushi yace Oh bani lemona bana son irin wannan,yaje ya tsaya a bayanta sosai zai kwace,ta sake kurba ya rirrke Jamilu ta baya yace bani Ohhh I don't like this yaja tsaki,Jamilu ta tirje a Jikin kujera tana Sha,ya manta ma ba mace bane ya rungumo jimilu cikinsa ya riketa sosai ya kwace lemonsa,amma me sai yaji Hallare ta mike lemon ya saki a kasa ya koma kujera ya fada Saman kujera Yana salati a ransa, Yana cewa na shiga uku ni ko addua zanje ayi min ne,na rasa gane me nake ji game da Jamilu,why? Sai ya bawa kansa amsa kabarin me tatsinensa ne ya taba min jiki shine na mike haka,Oh God wannan fa ya wuce kabarin me tatsine ma ya koma Jakin babangida, Naila bata San me yake tunani ba ta zauna a gefen kafarsa tace na dai Sha nima,ka tashi Dan Allah muci abincin ko sai dare ko na bayar?

Yanzu sabo da ana kawo maka abinci me dadi shine kake min gani gani,idonsa ya dago ya zuba su a kan Jamilu gaba daya ya koma wani ja harda kwalla a ciki,Naila tace wai zazzabi kake yi ne? idonka yayi ja fa,Spark Bai iya cewa komai ba gashi idan yace Jamilu ya fada Masa gaskiya sai masifa,shuru yayi ya Dan kokarta ya dawo hayyacinsa ya mike zaune ya jawo abincin yace muci,ya firfito dasu abinci masu rai da lafiya,suka zauna a kasa tare suna ci suna satar kallon juna,kowa da abinda yake tunani a ransa.

Hanan kuwa abinda Naila tayi mata waccen ziyarar taji haushi ta dauki alwashin sai taje gidan yari ta tonawa Naila asiri ba tare da kowa ya sani ba,shiryawa tayi ta wuce gidan Umma sabo da Mohsin ya damu lallai sai taje ta gaida Umma da Abba,tana shiri sai ga Mohsin ya shugo yace ga Abba Nan da abokinsa zasu zo ki fasa zuwa yau gobe sai kije,Hanan wani takaici ya kamata tace ai kasan dai nace zan biya gidanmu Kanwata tana zazzabi zan duba ta,yace nace baza kije ba Abba zaizo kanwarki tafi Ubana nane? Hanan mayafin ta cire tana kunkuni tana furta duk an bi an takura min sabo da Ina da aure ta zauna a Palo tana fushi.

Abba ne yayi Sallama ya shugo tare da abokinsa Isa,Hanan ta wani bata rai ta amsa,sai Mohsin ne yace su shugo Palo,bayan sun shugo sun zauna da kyar Hanan tace Ina yini,Abba yace lafiya Lau ya gidan? tace Alhmdllh ta mike ta shige daki ta barsu a Nan tare da Mohsin bata ko sake lekowa ba,Mohsin ya bita bedroom yace ki fito ki kawo musu lemo da ruwa da abinci, dama basu ci abinci ba suka fito to ni abincin yau kadan nayi me yasa baka ce na dafa da su ba,Mohsin yace wai Ina zuwa ubanki ne ya kawo min abincin ne ko kuwa? Ubana guda zaki wa wannan wulakancin? Kuka ta saki harda kururuwa,Abba suka ji kukanta yace Kai Mohsin lafiya?

Ya fito Yana cewa wannan yarinyar bata da mutunci wallahi nayi danasanin aurenta,Abba yace a'a indai akan mu ne mu tafiya ma zamuyi muje ka raka mu gidan su Fatiman shike nan mu babu matsala ma ka kyaleta, su Abba suka mike Malam Isa yace ka rabu da ita Dan Allah Mata sai hakuri,Mohsin ransa in yayi dubu to ya Baci,haka yaje ya kira musu Fatima tace su shiga,shi Kuma Mohsin ya koma gidansa Yana zuwa ko magana baiyi ba ya dakko biro da takarda ya rubuta mata saki daya ya jefa mata Inda take kwance yace gashi Nan kije daga dubiyar ki zamanki a gidanku na sakeki saki daya.
Chapter 31 · 0% Book details