← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 98

Sashe 43

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Batoola kuwa sai da Naila ta Dade da barin gidan sannan ta mike a hankali ta fice fit daga dakin ta fada dakin su Tsohuwa tana cewa aljanu aljanu...zasu kasheni....Dattijon suka tashi suka dinga zazzagawa Batoola fada suna cewa ai kece Azkhar yayi miki karanci ke dai wake wake kawai,ance ki gyara halinki kinki ai gashi nan,ke dai sai waka babu Azkhar da addua sallah ma sai anyi yaki Dake kullum kece hada sallolin hudu a lokaci daya,ai gashi nan,Tsohon ya shiga tofawa Batoola Ayatulkhursiyyu Yana cewa bakya karanta Ayatulkhursiyyu shi yasa,Batoola tace wlh da na ga Aljan din na karanta yafi sau dubu amma ko gezau,wai fada min suke fa kar na sake na auri Hashimu Dolo,wallahi na fasa zan auri Usman din yafi min na hakura da son sai na juya miji,ga dubu gomansa ta anko da dansa ya kawo a Maida Masa abarsa,babu ni ba Hashimu Dolo har abada,aljanuna basa kaunarsa Sam sunce ina aurensa zasu kashe ni wai sune suka kashe tsohon mijina,Dattijon yace wanne irin rashin tsoron Allah ne Batoola ai aljanu ma Allah ne ya halicce su idan Allah ya kaddara sun isa su Hana ne, Batoola da sauri tace nidai nice me auren Kuma ni zan zauna sabo da haka wlh na fasa,ga bulala Aljanin ya dinga zuba min kamar da karfe yake dukana na hakura indai Hashimu dolo ne,sunce kar na wuce 1weeks banyi aure ba,ai Usman ma mutumin kirki ne Kuma Yana da aikin yi duk da matansa biyu ace ya turo,zan fada Masa in ya shirya nan da sati sati,Dattijon yace ai dama na fada miki Hashimu ya miki tsufa kika ce ke Wanda zaki juya kike nema ai gashi Nan,sai ki fadawa Usman din ya turo,ranar Batoola tare da iyayenta ta kwana daki daya.

Da sassafe Batoola ta fito ta nufi gidan Mohsin da dubu gomansa a hannu tayi sallama,Hanan ta danji sauki tana kwance a Palo amma da kyar take gani,Batoola ta shiga ta samu Mohsin Yana hada tea,yace ah Aunty Batoola sannu da zuwa,gaisawa suka yi ta mika Masa 10k din tace gashi ka mayarwa Abbanku ka fada Masa na fitar da miji yayi hakuri na fasa ni dai bazan aure shi ba,Mohsin yace a ransa ko dai Naila ta cika aikin ne,sai ya hau dariya a ransa yace Alhmdllh haka kawai zan sake dakkowa kaina masifa ai sai Naila Allah ya tsare min ke,a fili kuwa yace ba damuwa zan fada Masa amma ki rike kudin an bar miki,Batoola da sauri tana karkada Kai tace a'a la a'a ku rike abinku ta ajiye a Saman kujera ta fice,Hanan ta tabe baki a ranta tace Umma an shiga malamai,ai baza su taba yarda a aureta ba,naji haushi wlh hmmm har naje mun gama hada baki da Batoola yanda za a ganawa Umma azaba a gidan miji ta zama ita da hoto daya amma jarabar shegiyar ta fada malamai zata haukata Batoola Allah yasa Abba ya gano wata,Mohsin ne ya katse mata tunaninta yace kina ganin Batoola har ta tafi ko gaisawa bakuyi ba Kuma naga kwana nan Kun zama kawaye,Hanan a ranta tace dama kawancen namu na yanda za gallazawa uwarku ne idan ta kama ma a saketa kamar yanda nima tasa aka sakeni ashe ta tafi kauye wajen Ubanta ya hada asiri ansa Batoola ta dole ta fasa ba komai bari a samo wata,Mohsin Yana kallonta kamar tana magana a ranta bai dai ce komai ba ya kwashe 10k ya zuba a aljihunsa.

Naila ce ta kira shi ya tashi tsam ya fice daga gidan ya koma kofar gida sabo da Hanan kar taji sirrinsu, kashewa yayi ya kirata back,tace Yaya my love ,yace Na'am ya a Ina kike ne? Naila tace wajen Baby Beauty ta gane gaskiya yanzu tasan ni Macece mun zama kawaye Ina gidansu,Mohsin yace Abu yayi kyau,tace ai na gama aiki jiya a kan Batoola,Mohsin yayi dariya son ransa yace har 10k din ta dawo da ita dazu wai ta tsaida wani ba dai Abba ba,Naila ta sheke da dariya ta dinga bawa Mohsin Labari yanda ta aikata komai,yace in kina Abu kamar ba Yar gidan Hashimu Dolo ba,Naila tace Dolo ya haifi me basira ai Alhmdllh,suna ta hira tace saura Abuja kafin na dawo kanka nayi waje da Hanan,matar tawa ni ban saketa ba ki sakar min mata,Naila tace Kai Yaya baka da zuciya wlh akan Jin dadin Hallare sai ka zauna ana Maka anyhow,wlh bazan yarda ba sai na dauki mataki ni,yace to ai zan gani ya kashe wayarsa.

Ranar Kuma Beauty ta fara koyawa Naila mota,Naila da naci ance an gama na yau ta taho amma ta rike mota tace jeki ni zan kawo motar gida,Beauty tace tab kika fasa min mota Daddy sai yaci ubana idan ya dawo,tun safe suna filin har dare sannan Naila ta bari aka dawo gida,suna zuwa Chikar gayu tace sai nan da sati zata zo an hanata fitowa yanzu.
Naila tana gidan su Beauty ga Daddy baya Nan a nan take cin karenta babu babbaka tana aikin koyon mota ba ji ba gani,Kuma Beauty ta zuba karya ta karbi kudi wajen Daddy dubu dari da hamsim aka samu Dan kaya masu kyau aka siyawa Naila kala biyar,Leshi,biyu,shadda biyu da atamfa,sai takalma da jaka kala uku,harda su agogo da glass na sawa a fuska na Yan gayu, Naila tace akwai tsiya a Abuja,Sati daya Chikar gayu tayi karya a gida tace aiki ta samu a Abuja zata je ta a mata screening,ana ta murna a gidansu sabo da suna cikin talauci ko za a samu su farfado daga talaucin.
Kawai iyaye sabo da talauci hauka ne ba bincike ba komai suka barta ta taho ita kadai gidan su Beauty, ranar Kuma Naila suka karbo dinkunanta,Chikar gayu tayi mamaki ganin me kama da Jamilu mace,Sai da Beauty ta bata labari,Chikar gayu ta dinga shekawa Beauty dariya tace dama na fada miki kika ki yarda,harda kukan soyayya ai gashi Nan,Beauty tace kawai ta bani tausayi da naji labarinta shi yasa na dage zan taimaketa,Naila tana wajen tace a'a a'a ni ba a taimakona ke kiyayi Tantiriya wlh a gidan Maza fa na zauna Dan kin bada Gundunmowa shine zaki ce zaki ce taimakona kike,bara nazo ko maula? shawara kika kawo fa,Chikar gayu tana kallonsu tace to yanzu Munji magana ta wuce a fada min aikina, Beauty tace wallahi Naila kin Allah gareta amma ba komai,Naila tace wannan fa yiwa kaine kika sani ni me zan miki gaba,Chikar gayu tace ku bani aiki na naji please,Beauty labarin Naila ta kwashe ta bata da Kuma aikinta gidan Mima zata je a matsayin Yar aiki kawai ta dakko sirrinsu taji labarinsu shike nan aikin?

Naila tace Wanda ya miki iskanci ki koya Masa hankali ki tabbatar Yan gidan idan basu da tarbiyya to ki koya musu ita kin gane ai,Chikar gayu tace anzo Inda nafi kwazo bawa duk wani marar tarbiyya to ya koma me tarbiyya zan basu tarbiyya.Naila tace an gama zamu dinga waya kina can gidan ni Kuma Ina gidan su Beauty na Abuja zan kula da bangaren Dan Mummy Ashraf kenan,zanci uwarsa daidai gwargwado sai na hada Masa bomb,bala'i,tuggu da sharri na,Ke Kuma Beauty abinda ya kama na kudi kawai ki dinga samo mana,Bafa kyauta ba yawwa bashi kike bani ki dinga rubutawa Spark zai biyaki,ko a Ina idan bukatar kudi ta taso to kawai ki ranto min bashi na dauka a wuyana Spark zai biya karki ji komai nasan dole zai kwakwulo gidanmu za a bashi number ta shike nan zamu hadu a Abuja idan ta kama ma kiji an daura aure ko irin na Yan India ne yanda suke zaga Abu ana mangale.... mangale....mangale....Kuma wlh bazan ce NAHI ba.

Chikar gayu tace ai wlh karki ce Nahi wlh ki aure shi kawai kuyi choreliye dinku a turaka,Naila tace ai har chori merii sai mun yi,Beauty tace ku hada da Tere liye Naila yafi dadi, Shewa suka yi.

Spark kuwa tunda ya koma gidansa yaki zuwa gidan kowa har Mummy din yaci gaba da Uzurinsa,sai da yayi settling komai nasa a wajen aiki sannan yace ni dana daura Shirin aure Ina naga ta zama,Jamilata tana jirana,zan ajiye sarakan bani bani mata,amma Kuma Yana ta kiran number Naila ba dare ba rana shuru,wata Yar karamar hauka ya fara da yaji yayi sati guda Yana kiranta tun wayar tana ringing har ta daina,Bai San wayar Naila ta fada ramin bulo ba wajen haura katanga,har chaji ya kare ta kashe kanta.
Spark yau gidan Mummy ya fara zuwa,Yana shiga Palo yaji kida na tashi ta tara yaran mata kawaye suna ta Shan shisha a palon duk babu suturar arziki a jikinsu,Mummy ta saka wani mini skert da Yar riga me siririn hannu gata tumbur sai katon ciki,samanta sai kayan nono yayi dangangan daga kasa Kuma bata da kibar,Spark Yana kallon Mummy a ransa yace Ashe haka mummy take da mummunar kama gaskiya Alhaji Aliyu yayi hakuri wai wai samodara,a fili Kuma iya sallamarsa basu ji ba sai da ya shiga ciki,Mummy wai ita wayayya ta fito da gudu subu.. subu.. My Son Oyoyo zata rungume shi, Spark ya matsa da sauri ta rungumi iska,saura kadan matan Dake palon su fashe da dariya sai boye dariyarsu suke yi,amma spark kallonsa suke kamar mayu kowacce tana so ya kyasa,kamshinsa duk ya cika palon,Mummy hararar Spark tayi tace baka da kirki wlh na tara friends a gidan Mima anyi girki dangi an cika amma kaki zuwa haba Spark murna fa za a tayaka ka fita daga masifa,Spark dai Yana jinta yace Ina yini ya kuke ai duk na ganku a kotu mun gaisa mene za a Tara min mutane sai kowa yasan naje prison,au kaifa baka San arziki ba Spark murna fa za a tayaka,na hutar daku kowa tace Allah ya tsare gaba amma sai an wani yi min girki da yunwa aka ce muku na dawo?ni dai mun shiga uku da wannan yaro wlh wani auren za a Nemo ayi Maka ko kayi hankali,ai Mima ta shaka dama tace wlh wannan karon da kanta zata samo Maka matar aure,Spark yace tab.... ya juya yayi ficewarsa.
Chapter 43 · 0% Book details