← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 98

Sashe 36

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ruwa ta ebo me dan dumi a bowl na roba ta saka towel din karami a ciki ta matse kadan tace cire rigar a goge Jikin nan ko zaiyi Sanyi,Yace kana namiji gardi zaka taba min jiki naki ya furta ,Yana lulluba da bargo a Saman bed din,Naila ta fisge bargon tare da haurawa Saman bed din ,a zuciyar Spark dadi yake ji,a zahiri Kuma da kyar ya yarda,ya cire rigarsa daga shi sai boxers,jikinsa me tsananin kyau Wanda ya tafi da imanin Naila,shi kanshi wani farin ciki yake ji a ransa marar misaltuwa,kansa ya dora a Saman pillow ya juya mata baya gaba daya,gashi da kwailo baida juriya a cuta, ya dinga dishi uhmm...uhm...wash....Naila a hankali ta shiga goge Masa jikinsa, Hallare tuni ta mike sai da ta gama bayan nasa tace juyo gaba,Yana Jin kunya taga yanda ya mike,yace ai haka ma ya isa thanks,ka juyo in zaka juyo,bargon ya ja ya rufe daga kugunsa sannan ya juyo,Naila jikinta har rawa yake itakam bata taba ganin namiji haka ba,da sauri ta rufe idonta a haka take yi Ido a rufe,shi kuwa Spark fuskarta yake kallo kawai kamar maye ya lashi lips dinsa a hankali Yana wani kallonta ba ko kyaftawa kamar wani wawa, har ta gama Ido a rufe,da sauri ta dauke Bowl din ta zubar da ruwan ta wanke towel din tare da shanyawa kafin ta dawo yayi bacci ma.

Bangaren nasa ta gyara ta fice abinta ta koma dakinsu na malamai,tana shiga suka ce wai yanzu Jamilu Ina kake zuwa ne? ga budurwarka ta ishemu da nemanka ta jikin bango Beauty, Naila tace Ina wajen Budurwata ta number one a raina Spark muna zuba love,kasan ni both side ce in buga da mata in buga da Maza,Malam Sharu yace Muna addua Allah ya shiryeka Jamilu, gobe fa akwai maulidi muna gayyatarka Jamilu,Jamilu yace wai dama watan ya tsaya ne? Suka ce ae baka ga ana ta yanka shanu ba a gidan nan zamu ci dadi, kazo kaima a baka sura ka karanta,Jamilu yace idan dai Yan Mandiri sunzo masu kida zan shiga na chashe sabo da haka ba wani gardi da zaiji Muryata ni Jamilu Tantiriya,Malam Sharu yace Allah ya shiryeka Kai sai dai sai abin shagala ka iya,Jamilu yace sosai ma kuwa ranar akwai dukan kirji inyi rawa itace zata kaini,Malam Jilani ya furta Allah ya shiryeka ka daina harkar Daudu kana bin Maza Yan uwanka, kaima idan kana so mu dan samu waje mu kebe malam,Malam Sharu yace ai gwara mu mutu,Dariya Jamilu yayi harda shewa irin ta Yan Daudu.

Ranar maulidi tun yamma aka fara Maulidi a gidan, Naila bata je ba amma ana saka Mandiri ta tafi wajen,Maza an samu rana sai shagali akeyi suna ta tikar rawa,wurin Spark ta koma yaji sauki suka je asibiti aka bashi magunguna bayan an tabbatar malaria ce, bai fi kwana uku ba ya warke,lokacin Beauty ma ana shirin barin gidan yari domin Daddy dinta ya shiga ya fita shekarar ta biyar a gidan yari, sai yanzu Allah yayi,shi yasa take ta neman Jamilunta ta fada Masa,amma bata same shi ba sai yau,Jamilu Yana daga wayar yace tuba nake gimbiya sarautar mata,kaina bisa wuya,Spark Yana zaune Yana jinta kawai shi bai so yaji Naila da wani ko wata, fushi ya fara ya kwanta kawai Yana jinsu Beauty tace Allah fa yayi nima nan da kwana uku zan fita an gama komai,Jamilu ya furta wow,tace murna nakeyi zanzo Maka ziyara na ganka,Naila tace na miki murna Baby Allah ya samu a danshinku, Beauty tace Ameen .

Naila a ranta tace ni yaushe zan fita ne? Kawai sai hankalinta ya tashi, Spark kuma ana ta kiransa a waya a fada masa labari me dadi yaki dagawa gashi har an fara zama a kotu,Mama zama daya ganin asirinta ya tonu kawai ta Fadi gaskiya bata Musa ba,Yan uwanta da suke uwa daya uba daya da Kuma Wanda ma uba suka hada suna ta jimami har kuka suke ta faman yi,ba kamar Mima da Mummy,Mummy harda refefe baki tace kinyi asara Kaltume,me ke damun mu ne? Mu yanzu mata sabo da son zuciya mune zaluntar yaran kishiya,shi yaro ma me yayi Maka,yaro Amana ne, uwarsa bata gida ko ta mutu sai mata su zauna sabo da son Kai su dinga zaluntar yaran kishiya,wasu su nakasa yaro ko yarinya,wasu Kuma suyi ta gana musu azaba wannan zalunci ne Kuma Allah bazai bar mutum ba,wasu har da kisan Kai a kashe Dan kishiya,kishi hauka ne,kishiyar ma da ta mutu amma baza a hakura ba sai kishin ya koma kan yaranta,yanzu mene ribarki Kaltume dan kin kashe Yar kishiya sabo da ta auri Spark wato yarki kike so ya aura sabo da yana da kudi,tirr da hali irin naki Kaltume,ganin ke kika raineta har ta girma na zaci ta zama Yar uwa,na zaci mun zama daya da Asmau,yarinya tana mutuntamu,Kai Kaltume kuma kin yarda Dan Yar uwarki uwa daya uba daya yayi life in prison,to Allah ya Toni asirinki,Mummy ana ta kallonta a mutuniyar arziki ana cewa gaskiya ne,su kuwa sauran magana ma ta gagara.

Kotu zaman ta dage zuwa sati biyu sannan ta nemi a kawo mata Spark tare da ci gaba da tsare Mama, Mummy harda cewa alkali sati biyu yayi yawa Dan Allah a fito min da Dana dama na gama takaba ni Kam Alhmdllh,alkali ya kalleta yace to da kika gama takabar aurensa zaki yi kema? Dana ne fa yanlabai,yace ai naji kince kin gama takaba a fito miki da shi,zata yi magana alkali ya dakatar da Mummy da ta damu kowa a ciki da surutu.

Abba bayan ya dawo daga zance komai sai da ya kwashe ya fadawa Umma amma yaki fada mata zai mata anko,Yana runfar kayan miyansa Mohsin yazo wajen,bayan ya gaisar da Abba,Abba yace yau ba aiki ne? Yace ae,to madalla dama Batoola ce za ayi mata anko suna da biki ka kawo dubu goma a Kai mata ko kakai mata da kanka,Mohsin yace Abba kasan wata yayi nisa sannan kasuwar ma Bata tafiya yanzu ga me gidan nawa yayi tafiya,Kuma ma daga zuwa sai ace za ayi mata anko har na dubu goma,zagina zaka yi Mohsin? yace haba Abba ni na isa,to kaje ko rance ka samo ka kai mata kaji na fada Maka, Mohsin ba yanda ya iya yace ni na jawa kaina dana hada shi da Fatima.

Naila ce ta kira Mohsin lokacin daya shiga gidan wajen Umma, Mohsin yace na manta ban fada miki ba Abba fa zai kara aure sis,Naila tace na shiga uku kishiya zai wa Umma? Kuma kuka yarda? ya za ayi da shi shi yasa muka yanke hukunci cewar a samo me hankali a aura Masa kar ya kwaso mana jaraba,Naila tace Ina wani me hankali a kishiya,yanzu ma zuwan farko har tace ayi mata anko na dubu goma Kuma yace ni zan biya gashi ni yanzu ma dubu daya ma bani da ita cewar Mohsin,abincin gidana ya kare na su Umman ma ya kare,Naila tace ku rike auren Nan Sweetheart sai Allah yayi na fito ni nasan tuggun da zan hadawa Batoola da kanta ta fasa,sabo da Allah dame zamu ji ana fama da shi da gida, zai Kuma karo mana wani masifar salon tana zuwa ta haifo wasu yaran,Kai Yaya me yasa zaka yiwa Umma haka,duk da tana yiwa Abba masifa amma ai tana kokari tun Kuna yara itace cinku da shanku ta Sha wahala kullum a teaching Dan a rufawa Kai asiri amma kuce yayi wani aure da me za aji, magana ta Allah a nan baka yi tunani ba,ni bana goyon baya wlh kuma ko an aurota na dawo sai ta bar gidan nan kaji na rantse.

Mohsin yace gashi yanzu ashe kaina na nemowa aure ban sani ba,Naila tace yanzu baka da Sisi Yaya? Yace ae sai kayan kyau da wanka? dariya yayi tace Allah gwara ayoka mummuna a baka kudi,turo accnt number Yaya kaga kudin Daddy din Beauty ya bani ban kashe ba Kuma na samu wasu a wajen Spark Yana yawan bani kudi,ko bai bani bama sai nace ya bani rabona,yanzu sai da na Tara 50k,Banda kudin da su Dan Indo ke bani duk Tarawa nake yi,yace ke da zan kawo miki ni zaki bawa kina gidan yari,Naila tace Malam ka karba, ni I can survive macece ana so na a gidan Ina samu ba laifi,mene amfaninsu idan ban baka ba,Mohsin yace to Naila ai naji kunya,idan zaka karba ka karba ni da Kai akwai kunya ne Hallare ma ta kama ganin taka zanyi tsaf,zanci ubanki Naila tam,dariya tayi tace ka turo accnt karka bata min lokaci,ba a dade ba ya turo accnt,a cikin gidan yari suna da komai nasu sai taje Wajen masu POS ta tura Masa 50k din cass sannan ta koma dakinsu na malamai.

Spark yayi baki su Kamal sunzo suna fada Masa labari me dadi,yayi farin ciki matuka sai dai Kuma mummunan labarin Mummy suna fada Masa ta bude cin duniya da tsinke har kana nan kaya take sawa ta tsuke kamar Yar arna ta fice,itace gidan Shan shisha da Kuma yawo da kawayen banza suna cinye mata kudi,kullum suna gidanta sun tare,gefe daya Kuma tunanin Jamilu yake ta ya zai bar gidan ya barta,yace ai ko an yanke hukunci ni ba yanzu zan fito ba,Banga ta tafiya yanzu ba,su Kamal suka bude baki,yace ae ni yanzu banyi niyyar fita ba yanzu dadin gidan nake ji nafi nishadi a nan,Su Kamal haka suka koma gida da mummunan labarin cewar Spark yace Bai shirya barin gidan yari ba shi yafi son can,an Kuma rasa dalili sai Rafeeq ne ya tuna yace ai wlh a uzura Masa ya bar gidan ana yanke hukunci sabo da namiji yake so,kowa bai gane ba Daddy yace kamar ya? Rafeeq yace Gay yake so ya fara wlh wani Dandaudu yake kauna,yace ma shi zai aura,Mima zumbur ta mike tare da furta Yana hauka ne wlh dole sai ya bar gidan nan ana yanke hukunci,Kun san dai halinsa baya Jin magana ku San yanda zakuyi wlh ya bar gidan.
Chapter 36 · 0% Book details