← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 97

Sashe 9

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suwaye zanma bayani yanzu ina aikine tom yafada yafuce Tunda yaje hospital yaketa aiki saboda yasamu marasa lafiya dayawa dan haka be zauna yauba seda yayi threater har biyu ga duba pesion se da yagama aikinshi na ranar sannan yawuce gida lokacin magaruba tayi dan haka be shiga gidaba seda yayi sallah a masallacin gidansu bayan ya idarne yashiga gida parking yayi yafuto, motar jawad yagani yace yau ya dawo dawuri falon yashiga time din duk suna falo mamy ce keta fadin nadra kije kicire uniform din islamiyyannan to mamy zancire bara agama tom and Jerry shigowa yayi ilham ce ta tashi tanufeshi yaya sannu da zuwa karbar rigar hannunshi tayi tasaman mamy sannu da gida yawwa sannu son part dunshi yanufa binshi tayi abaya mamy da kallo tabita azuciyarta tana fadin Allah yasa ki samu karbuwa , a falo yatsaya yana fadin ke wayace kibiyoni to mene dan mata tabiyo mijinta kallon baki da hankali yamata yashige bedroom ya rufe yabarta a falo Se bayan magariba ta tashi tayi mamakin baccin datai alwala tashiga tayi tafuto ta tada sallah seda ta idarne ta kalli su amera dake wasa tace ina inna sunfuta itada iya lami tashitayi tanufi kitchen din tarar dasu tayi sunata aikin girki sannunku da aiki yawwa, kasa kintashi kai iya nice kasar tafada a shagwabe to inba kasaba mece tun la asar kike bacci se yanzu wlh iya nagajine shiyasa ah nagani kuwa kinyi gyaran kitchen sosai Bayan yashigane ya fada toilet ruwa me zafi yahada na wanka ya shiga kafin yashiga ne yakirawo mamy tasa akawo masa copie ko ze warwaremai gajiya, mamy ce tace muhsin jeka kitchen kakirawomun zuhura oh mamy sunanta zuhura dama eh mana haka suke fada mata tom yatashi kitchen yanufa yana shiga yace aunty zuhura wai kizo inji mamy tom tafada tana bin bayansa gudu yafarayi tace ka tsayani mana aunty zuhura za a wuce gurin danakeso a tom and Jerry oh kallo kukeyi eh to muyi sauri nan suka fara sauri tana zuwa ta tsugunna tace mamy gani yawwa zuhura kinga waccar yar tanuna nadra dake gaban tv kidauketa kikaita dakinta kicanja mata kaya tunda tafiya taurinkai tom tafada gurin nadra taje hannunta takamo tirjewa tayi a lallai ita seta gama kallo to inna cire miki zaki dawo ai ki tayi idan kikazo nacire miki zansamomiki sabobun kawayen dazaku dinga wasa kullum ta radamata akunne dagaske kadamata kai tayi alamar eh tashi tayi mamy na kallonsu setaji yarinyar ta birgeta zuhura idan kinciremata kicewa iya lami ta hada copie kikaiwa amar tom tace suka wuce wai ina ilham ne muhsinne yace tana dakinta me bi ma bacci takeyi aida itace yakamata takaimai, jawad ne yafuto daga dakinsa sanye da riga t shert da da tree quater mamy kuna falo kenan munanan abba be dawoba be dawoba kai canzamana channel yaya dan Allah kabari mugama kalla to kalli yafada yana daukar wayarsa Seda takaita dakin taciremata uniform tasa mata kaya sannan tace muje inkaiki Aunty zuhura inasanki sosai nima inasanki nadrata tadauketa dakinsu suka wuce suna shiga taga su amera da halifa suna zaune to nadra wannan itace amera wannan kuma halifa wow tafada kamar wata babba nadra ta gabatarwa dasu amera baranayi fitsari inzo mutafi toilet tashiga bayan tafutone ta taddasu sunata wasa nadra mutafi ah ah nidai anan zan zauna to ai shikenan futa tayi tabatta kitchen takoma iya mamy tace ki hada copie kibani nakaiwa setai shiru tana tunani kai harna manta sunan amar ko iya lami tafada eh shi to ai shine kawai me nacin copies agidannan copie din tashiga hadawa bayan tagama tabata tamata kwatancen part din nashi futa tayi tanufi part din da iya lami ta kwatanta mata Seda yakusan minti 30 a toilet sannan yafuto daure da tawul a kugunsa gaban madubi yanufa lotion dinsa yadauka yafara shafawa. falon tashiga sallama tayi taji shiru ganin wata kofa tayi kofar tanufa murdawa tayi dama abude take saboda yasan yasa akawomai copie shiyasa yabude saboda kar a kawomai yana wanka shiga tayi bakin kofa ta tsaya hangoshi tayi yana taje kanshi ta rasa me zata cema takasa magana se idonta data rintse wai dan taganshi ba riga siffar kirjinshi tafuto sosai gashi yanada fadi, harya taje kanshi yafeshe jikinshi da tararukanshi juyowa yayi ze nufi wadrope ganin mutum yayi abakin kofa atsaye ido arufe ga hannunta rike da farantin da aka dauromata copie din matsawa yayi daf da ita kuramata ido yayi haryanzu idonta a rufe yake iska ya huramata bude idonta tayi Dan taga daga ina iskar take, tana budewa taga mutum daf da ita ba riga ajinkinshi copie din hannunta ne ya bare ajikinshi zafi yaji sosai itakuma tasa tafukakan hannunta ta rufe fuskarta ashh yafada a hankali wata wawar tsawa yadakamata wacce tasata firgita ke mahaukaciyar inace bakida hankali zaki watsamun copie ajikina bakintane yafara rawa dan Allah kayi hakuri bansaniba tafada tana kinkina tashi kifutarmun daga daki kasa tashi tayi saboda firgitar datai dan kadanne bata saki fitsariba i say get aut of side ganin bata da niyyar tashi yasashi dagota daga durkushen datayi damtsenta yakama yafutar da itah yarufe kofar Futowa tayi tana hawaye kitchen tanufa tarar da iya lami tayi tana shirya kayan abinci zata futar kan dining yawwa zuhura kindawo zomu futar da kayannan ganinta tayi fuskarta ajike da hawaye tace meya faru kike kuka kardai ya marekine gyada mata kai tayi alamar ah ah to me yamiki tsawa yayimun ajiyar zuciya tayi tace kinga share hawayenki goge mata hawayen tayi tace daukamun wannan to tace dauka sukai suka nufi dining ajiyewa sukai suka koma kitchen din suka debo sauran yawwa to jeki cemusu mungama shirya abinci to tace tanufi falon gabadaya suna zaune banda amar dake can dakinshi sallama tayi mamy ce da muhsin ne kawai suka amsa tsugunnawa tayi gaban mamy, mamy angama shirya abincin dare ok sannu zuhura yawwa jeki part din amar kifadamai yafuto muyi lunch shiru tayi saboda tagane watake nufi bakinsan part dinba dazu ai kinkaimai copie ko kadakai tayi alamar eh tashi tayi zuciyarta na dukan uku uku dan ita tsoronshima takeji yanzu yazatayi ilham ce takatseta dacewa ke barshi kawai zan fadamai ajiyar zuciya ta sauke tace tom, takoma kitchen , ilhamce tamike tanufi part din amar falon tashiga kwankwasa bedroom din tayi tashi yayi daga kwancen dayake bude kofar yayi am yaya dama angama lunch ne tafada tana juya ido ok ganinan ciki yakoma copie tagani a kasa ga cup din ya fashe yaya amar wannanfa bansaniba yafada yana bi tagefenta yawuce to meyakawo fasashen cup nan ganin bata da amsa yasata fucewa itama, son wai me kake tayi a dakine ko abincifa bakaciba mamy nagajine shine na kwanta na huta takawoma copie din eh takawo ta barar barar wa kuma eh yanacanma harda cup din ya fashe garin yaya nima bansaniba mamy kisata taje ta sharemun, ok tashi sukai sukanufi dining din ina nadra ne muhsin duba kitchen tom yafada mikewa yayi yanufi kitchen dubawa yayi yaga be gantaba aunty zuhura ina nadra tana cikin dakinmu dubata to, dakin yatafi nan ya taddasu sunata wasa harda kayan wasanta nadra kizo inayini ya gaishe da inna lpy lau dannan nadra ce tace anjima zandawo kunji to suka fada, futa tayi da gudu, futowa tayi daga kitchen din dan tayi saving dinsu iya lami tana sallah, dukansu sun hadu suna jira azo ayi saving dinsu abba ne kawai babu shibe dawoba, karasawa tayi saving dinsu tafarayi kowa tamikamai mamy ce tacemata sannu zuhura kinji murmushi tayi, tafiya tayi taji muryarshi nafadin kijeki sharemun cup din dakika fasa mamy ce tace zuhura dan Allah jeki sharemai cup din kinji yar albarka tom tafada tayi hanyar part din, nasan kunata san kusan wace itah ko jawad ne yadago yana kallon mamy din datake maganar anan tabasu labarin abinda yafaru jin juna kai amar yayi aranshi yace tabbas yarinyarce , kuma kunga iya lami ko gobe ko jibi zata tafi kauye to dan haka su zasu dinga yimana aiki mamanta zatai girki itakuma gyaran gida da sauran dakuna , shigatayi falon tsayawa tayi tana tunanin a ina tsintsiya take dubawa tayi bata ganiba hakan yasa dole ta koma kitchen tadauko, share gurin tayi taje ta zubar a ashara ta dawo tadau Mopar tayi moping din gurin sannan tafuto, se da suka gama cin abincin tas sannan suka koma falo suna hira, se kusan 10:00pm abba yadawo sannu da zuwa sukaimai sannan yawuce dakinshi mamy ce tabisa , se da takoma daki sannan taci abinci tayi sallah nifa wata kila gobe zan tafi dan bansan halin dayake cikiba to gobe kuma eh wlh seku dora da aikin dana tsaya ke kidinga girki itakuma tadinga saving dinsu kuma dakunana su da safe duk sekun share tab aini yau iya kinji yadda nagaji daga farawa tab to ai akwai aiki dahaka har suka kwanta Se 10:30 duk auka watse daga falon shima part dinsa yanufa wayarshi yadauka yayi dialing number Ahmad saboda da rana yaga miss call dinshi be biba bugu biyu yadauka kai abokina ya gida nakiraka baka daukaba bana kusane ya aiki alhamdulilah nima kagannu inata fama wlh nima yau kaji gajiyar danayi kuwa ai yanzuma aka fara kai haba hira sukai daga karshe yacemai zeyi bacci yakashe wayar ya kwanta nan da nan bacci barawo yasaceshi Jawad na tunanin taya ze samu zuhura da bukatarsa saboda gaskiya tayimasa irin matan dayake so cikakku ai ita iya kallon surarta ma ya isa yasa mutum a feeling wai dan ma da hijabi yafada afili dahaka yagama tunane tunane har yayi bacci
Chapter 9 · 0% Book details