← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 97

Sashe 36

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

SOYAYYA DA IZZA
Story and writing by Hadizatu
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan
asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau
page 36
________________Karfe 6:30 yadawo gida, bayan yadawo yawuce part dinsa, yayi wanka yadauro alwala, yawuce masallaci, bayan yadawo ne yazauna a falour, inda su Muhsin ne kawai suke buga PS, wayarsa yadauka yahau daddanawa, Mamy ce tafuto, kallonshi tayi tace "ashe kadawo" "eh Mamy nadawo" "ok kana bukatar abinci ne" "no Mamy bara kawai idan lokacin lunch yayi senayi, "ok daga haka tawuce kitchen" Jummai ce keta aikin girki se Zuhura dake yankamata albasa, sunata hira tana bawa Zuhura labarin ya'yan ta, tanata dariya, "ah ah sannunku da aiki" "yawwa Hajiya sannu da futowa" Jummai tafada tana dan russunawa, kallon Zuhura Mamy tayi tace "Zuhura kidan hadawa Ammar coffee kikaimai naga beci komai ba me be yana bukatar cofee din" amsawa tayi da to tafara hadawa tagama tazuba a cup tafuce, afalour tasameshi, gaisheshu tayi ya amsa wanda shikadai yaji, cup din ta ajiye mai, kallonta yayi kamar yamata magana wayace takawo mai, se kuma yayi shiru dan shima yana bukata, bata aune ba taji Nadra ta riko hannunta tana fadin" yaya Zuhura zomuyi game na Ps" "Nadra ban iya bafa" "dan Allah yaya Zuhura kizo muyi" tana maganar tana jan hannunta, ganin tadage yasa tace "to shikenan muje" gaban TV din suka zauna Muhsin yamika mata kallonshi tayi tace "nifa Muhsin ban iya ba" "ai keda Nadra zakuyi nikuma senai ni kadai muga waye zai cinye, duk nasan ma nine" karba tayi suka fara, shima yafara nasa, seyaga zasu wuce sa se yayi maza ya wuce su, hakan suka dinga yi, daka karshe yaga sun wuce shi sosai, se wafce remote din ya tashi, "yaya Muhsin kabamu mana" "nabaku ku wuce ni" se zagaye suke da Nadra tanason karba se ya dageshi sama tayi ta tsalle zata karba, itakam Zuhura dariya take harda rike ciki, kallonta yake yana murmushin da besan ma yanayi ba, dariyar tata tana masa matukar kyau, Mamy ce tazo tana fadin "kai wasan meye haka" se lokacin yadena kallonta yacigaba da kallon wayarsa, "Mamy wai dan yaga zamu cinyeshi game shine ya kwace mana nida yaya Zuhura" Nadra tafada cikin shagwaba, zama Mamy tayi tana fadin "ah to Muhsin baka da gaskiya" "Mamy cinye ni fa zasuyi" "Mamy kuma shine yadinga cika baki wai seya cinyemu" Zuhura tafada tana sasauta dariyar ta, Mamy taji dadin ganin Zuhura cikin walwala, "to ai shikenan seku denayi dashi ai" shikam goganka nunawa yayi bemasan me suke yiba, "kutashi kuyi lunch" Muhsin kakira Jawad Ahmad baya nan ko Zuhura kira Ilham" to suka amsa su duka suna tafiya, kallon Ammar Mamy tayi tace "muje kayi lunch din ko" amsawa yayi yana tashi, knocking tayi , seda aka dan jima Ilham tafuta tabude, "ya akai" abunda tafada kenan tana kallon Zuhura "Mamy ce tace nakiraki" "ok jeki zanzo" wucewa Zuhura tayi kitchen tanufa, lokacin Jummai bata nan, abinci tadiba, ta zauna tafara ci, ba jimawa Jummai tashigo, kallonta tayi tace, "au anan kike ci" "eh" abunda tace kenan tacigaba da cin abincin, zama Jummai tayi itama tazuba tafara ci, "Zuhura inkin gama gana Hajiya nan dan Allah kikai mata" "to ai nama gama" tashi tayi ta wanke hannu tadauka tafuce, da sallama tashiga, ta tarar da ita saman sallaya ta idar da sallar isha, shiga tai ta ajiye kulolin, tana fadin "Hajiya ga abincinki, bara nima nayi alwala nayi sallah" daga haka tashige toilet, alwala tayi tafuto lokacin Hajiya tana zuba abincin, kan sallayar tanufa tadau hijabi tada sallar,
kallonsu Mamy tayi su duka tace, "mahaifiyarta tabarmin ita a hannuna dan Allah ku kula , kasa naji kuna hantarar ta ko kuma kuna kyararta, especially kai Ammar banason wannan tsawar datakeyi, ballantana kamata, kar naji, ku dauke ta matsayin yar uwa" girgiza kai kawai yayi yana ci gaba da cin abincinsa, Mamy ce takara cewa "yawwa kabawa Ilham kudi ranar Alhamis zatai bridal shower" dagowa yayi yakalli Ilham , "ok" yafada, Mamy ce takalle ta tace "Ilham kamar nawa za a baki" "Mamy 1.5 million yayi" kallonta kawai yayi yace "dame dame zakiyi da zan baki har 1.5 million" "haba yaya Ammar ana kashe kudi fa sosai kuma friend dina na abuja zasu zo" Mamy ce takalle shi tace "kaga kabata bakai kace bazatayi dinner ba" "ok shinenan zantura miki" yafada yana tashi, part dinshi yawuce, zama yayi saman kujera yadauko laptop dinsa yafara aiki,Jawad ne takalli Mamy yace "wai Mamy saboda me yaya Ammar baze bari ayi dinner ba" "oho mai haka yazaba, amma gashinan ai zatayi bridal shower" "to ai Mamy maza basu fiye zuwa ba" "no Jawad harda maza mana namu, kowacce ma da boyfriend dinta zata zo shine getpass dinta" "wow yayi kuma kice zamusha casu" ita dai Mamy batace komai ba, Abba ne yashigo, tashi Mamy tayi ta karbi jakar hannunsa, tanamai sannu da zuwa, suma sannu da zuwa sukai mai gaba daya, kana yashige ciki Mamy tabishi, suma bayan sun gama ci duk suka watse kowa yatafi kwanciya, Mamy ce tafuto tahadawa Abba abinci kafun yafuto wanka, Jummai ce kitchen din tana shirya kayan data wanke, "Jummai kina nan kina ta aikin ko kije huta kiyi bacci" "ai Hajiya nagama" "ok nima Abbansu ne yadawo zan hadamai abinci, ina Zuhura ne"? "tana dakin Hajiya dan tundazu datakai mata abinci bata dawo ba" bayan Mamy tagama hadawa tafuce tana fadin "kina gamawa fa kije ki kwanta"
zaune suke suna ta kallo su duka a falour, shikam halifa har yayi bacci, tunda lokacin 9:00pm, wayar Daddy Yasmeen ce tayi kara, dubawa yayi , son Mahmud shike yawo kan screen din, murmushi yayi yace , yaron nan besan mu dare bane, kana yadauka, "hello son ya akai ne" "Daddy kawai fa gaisawa zamuyi" "to shikenan mu gaisa anwuni lafiya" "lafiya lau Daddy ya kowa da kowa" "kowa na lafiya" "Daddy ina auntynmu Yasmeen tafada min munyi aunty" "kace har ta gayama, wannan yarinyar" Daddy yafada yana nunata, "to Daddy meyasa baka fadamunba" "so nai seka dawo seka ganta" "kai Daddy kabani ita mu gaisa" kallon Inna Alhaji Aminu yayi yace "ga danki yanaso ku gaisa" karba tayi tana fadin "Assalamu alaikum" "wa alayki salam aunty ina wuni" "lafiya lau ya karatu" "alhamdulilah ya mutanen gidan" "kowa yana lafiya" "Masha Allah" daga haka tamika wa Alhaji Aminu, "ok son dare yayi kabari se safiya " "to Daddy mu kwana lafiya" daga haka yakashe wayar, kallon Yasmeen yayi yace "Yasmeen kuje ku kwanta amma kifara kai Halifa dakinsu" "tom Daddy" daga haka tamike, tadau Halifa takaishi dakinsu kana tace Amira ta je ta kwanta itama tawuce dakinta, suma su Inna tashi sukai suka shige,
futowa tayi dakin Hajiya tanufi dakinsu, tana shiga tasauya kaya zuwa na bacci, kashe fitilar tayi, a tsorace ta hau kan bed din ta gudun ne ciki, iska aka fara lamar hadari, gaba daya a tsorace take dan dakin yamata girma, ruwa aka fara sosai ga kabulayen dakin sunata kadawa, kara dukun kunewa tayi tana sa kuka, har tana rawar jiki,
bayan yagama aikinsa ya rufe laptop dinsa, yatashi yashige bedroom dinsa, kayan bacci yasa, yakwanta, wata kishirwa yaji, tashi yayi yanufi fridge din dake falour ya bude, se lokacin yatuna ruwan sa yakare kuma besa ashigo mai dashi ba, tashi yayi yafuta dan yaje kitchen yadauko, saboda yasaba tashi cikin dare yasha, gashi kuma yanzu ma yanajin kishin, kitchen yaje ya kunna light din wayarsa, yabude fridge din yadauka yafuto, wata tsawa akai wadda tasata fasa ihu, tana fadin "wayyo Allah Inna ta kitaimakeni" jin ihunta yasa yanufi inda yakejin ihun, tura kofar yayi, ya haska da wayarsa ya nemo switch din fitilar dakin, ya kunna, tana ganin haske cikin idanta yasa takara sa kuka "wayyo Allah Inna zasu kamani" kallonta yatsaya kawai yakeyi, jin shiru yasa ta leko tacikin blanket din, ganinsa tayi, aikam da gudu ta yaye ta diro daga gadon tanufeshi, rungume shi tayi tsam tana fadin "zasu kamani kataimake ni dan Allah tsoro nakeji" kokarin banbareta yake a jikinsa amma ta kamkameshi, ganin bazata sake shiba yasa yakamata suka fuce, ko da suka fara tafiya tana kankame dashi, har suka isa part dinsa, kan kujera yazauna, still dai tana jikinshi bata cika shiba, kallonta yayi , sekuma yayi shiru da tsawa zeyi mata se kuma ya tuna maganar Mamy, yace "Please cikani dan Allah kije wacce kujerar ki kwanta kiyi bacci" yafada yana nunamata kujera 3st kallonshi tayi yakara cewa "ba inda zani ina nan ba abunda ze kamaki" mikewa tayi tanufi kujerar ta kwanta, shikuma yana zaune nan, tun tana bude ido taga ko yanan har barawo bacci yasaceta, shima se can bacci yasace shi a zaune,
kiran sallar farko a kunnensa, bude ido yayi, jiyayi wuyanshi ya kage, dakyar yamike yanufi toilet, yayi alwala yafuto yawucd masallaci, seda yayi nafilfilinsa kana aka tada sallah, bayan yadawo, still tanata bacci ga rigar baccin tata duk ta yaye, matsawa yayi yagyramata kana ya wuce daninshi ya rufe dan yayi bacci, seda gari ya waye, ta farka, ganinta tayi dakinsa, tuna abunda yafaru tayi, kana ta tashi tabude kofa tafuce, daninsu tanufa tayi alwala tayi sallah tayi brush, futowa tayi kitchen, Jummai ce keta hada breakfast na masu zuwa makaranta, kallonta tayi tace "ai na dauka kin shirya makarantar" "ah ah yanzu dai zan shirya" "ok kiyi maza kinga 7 saura nayiwa Nadra wanka" "tom bara naje na shirya" daga haka tafuce
Chapter 36 · 0% Book details