← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 97

Sashe 54

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Ina masu bibiyar books dina
to ina muku albishir da sabon book dina
dana fara rubutawa
me suna YAN BIYU NE ina baku shawara ku bibiye book din nan
dan akwai chakwakwa kiya kala kala zaku nishadantu
zakuma ku wa'azantusosai kudai kawai ku bibiye kafun free page yakare ku biya kan naira
300 kacal ba tsauwalawa
ina alfahari daku
masoyana
kune kwarin gwuiwa ta
i love you so much
my pans
ina godiya da addu'o'in ku
dayacce kuke yabon book dina
duk da shine nafarko, gudiya buhu buhu
nice taku har kullum Hadizatu wacce kukafi sani da (MRS K D) kucika da bibiyata nukuma zanci gaba da nishadantan daku
DOMIN SHIGA GROUP DIN SOYAYYA DA IZZA KA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA
https://chat.whatsapp.com/FPb99RjggTbAcCFg1aFrVx
DUK ME BUKATAR SOYAYYA DA IZZA YA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA
https://whatsapp.com/channel/0029VahPZYb6WaKlZQvivt0J
page 51
_______________________________________________________________________
_____________________________
________________Inna ce ke shirya breakfast kan dining, wayartace ta dau kara, hakan yasa tadauka tana fadin "yaya ina kwana" daga cikin wayar yaya Asabe tace "Habiba Allah yayi wa gwaggo Larai rasuwa jiya da daddare" "inalillahi wainnailaihi rajiun" abunda Inna tafada kenan, yayin da su Amira suka futo cikin shirin makaranta, Amira ce takalleta tace "aunty meya faru" "to yanzu zantafi na sameki a can" daga haka takashe wayar, Daddy ne yafuto cikin shirin futa, Inna ce tace mai "yanzu yaya Asabe takirani take fadamin Allah yayi wa gwaggo Larai rasuwa" "subuhannallahi yaushe kuma" "jiya da daddare, yanzu inason naje tunda bama a kaita ba" "to semu tafi tare ai" "aunty muma zamuje" "ah ah ku wuce school driver yakaiku" daga haka tashige ciki, shirya wa tayi kana tafuto, suka wuce, sukuma su Amira suka wuce school, a mota ta takira Zuhura, riging har uku bata dauka ba, seta kara gwadawa ko zata dauka
bayan tafuto daga wanka taji wayarta na kara, hakan yasa ta nufi gurin wayar, ganin Inna ce ke kiranta yasa tadauka da sauri tana fadin "aunty ina kwana" "lafiya lau Zuhura, gwaggo Larai ce ta rasu" "inalillahi wainna ilaihi rajiun aunty yaushe" "jiya da daddare, amma ko kaita ma ba'ayi ba yanzu nima natafi" "Allah yajikanta, bara yaya Ahmad yatashi nafadamai ko ze kawoni" "ko kuma kibari kawai se uku kya zo" "ah ah aunty nasan baze hanani ba, kuma aunty inason nazo dan muyi magana" "kinga indai maganar auren mijinki ne nasani" "oh aunty kinsani" "to menene akanki akafara kara aure" "to anty amma" katseta Inna tayi tace "kinga dan Allah ki kyale ni, sekinzo kawai" daga haka Inna takashe wayar, a gaggauce tashirya sanadiyar yau ta makara bata tashi dawuri ba, gashi har 8:00pm tayi, tana gama shirya wa tafuce, danta hadamusu breakfast kafun su tashi, saukowa tayi falourn, tsayawa tayi cak tana kallon su, Ahmad ne ke breakfast, itakuma Nafeesa tana zaune tana kallonshi, suna hira, karasawa tayi tace "ina kwanan ku" Ahmad ne kawai ya amsa yace "lafiya kintashi" "eh" tafada tana wucewa kitchen, kanta tashiga hadawa breakfast, bayan tagama taci abinta a kitchen din, seda tagama kana tafuto, basa falourn da alama yagama sun shige ciki, zama tayi kan kujera tana kallo, ba jimawa Ahmad ya sauko cikin shirin futa office, itakuma tana rike da hannunsa, kallo daya tamusu ta dauke kai, "kai Sweet kayi kyau dayawa fa" kallonta yayi yace "to ai duk kece kika sa" dariya tayi me sauti kana tace "kasan ai inaji dakai" tafada suna kokarin fucewa, mikewa Zuhura tayi tace "yaya Ahmad inason zuwa kaduna" juyowa yayi rai a hade yace "me akeyi acan din" "dazu aunty takirani take fadamun gwaggo Larai ta rasu jiya" "to se akai yaya inkinje dawo da ita zakiyi" "yaya Ahmad kaine kuwa" "oh to waye, nidai nace ba inda zaki" daga haka yafuce, Nafeesa tabishi abaya, mamaki ne yacika Zuhura tayi mutuwar tsaye, tana tunanin anya yaya Ahmad dinta ne,
LONDON
9:30pm juyi kawai yake yakasa bacci, tunanin Zuhura kawai yake, dana auren Ahmad da aka ce yayi, kenan dama soyayyar dayake ma Zuhura karya ne, haka yadinga tunane tunane tuanane, dahaka har bacci yadaukeshi,
*********************
seda aka gama aka kai gwaggo Larai sannan driver yazo yadauki Inna, kowa mamaki ne yacikashi, ganin yadda suka koma, harda ma yaya Asabe, kuma ga yadda suke futo da kudi, da ance babu kaza sesu bada kudi, hakama Alhaji Aminu bayan ankaita an dawo, yabada dubu 50 ayi abincin zaman makoki, suma su Inna sun bayar da ku
i, karfe 4:30pm Inna ta dawo gida, lokacin su Amira na shirin islamiyya, "aunty sannu da zuwa ya hakuri" Amira tafada lokacin da Inna ke zama saman kujera, "yawwa Amira da godiya" "aunty bara muwuce islamiyya lokaci har ya kure ma" "to sekun dawo aunta na" "to aunty" Halifa yafada suna fucewa,
komawa tayi ta zauna, saman kujera tana tunanin sauyawar yaya Ahmad dinta, Nafeesa ce tashigo flourn, ta nemi guri ta zauna tana daukan remote, ta canja tasha, takai ta wakokin naija, ita dai Zuhura shiru tayi batace komai ba, kallonta Nafeesa tayi tace "ke tashi kije ki dora abincin rana" "ai na dauka ke zakiyi tunda naga ke kikayi na safe" "ke ina magana kina magana dallah malama tashi kiyi abinda nace ko yanzu nan ranki ya baci" tashi Zuhura tayi tanufi kitchen, tsayawa kawai tayi takaici duk ya isheta, haka dai tayi girkin ba'a son ranta ba, bayan tagama tajera a dining, kana tawuce bedroom dinta, tana zuwa dakinta ta dau wayarta takira Inna, "hello aunty ya hakuri" "da godiya" "aunty na tambayi yaya Ahmad yace wai bazanzo ba" "to shikenan ai basekin zoba" "to amma dan Allah" "dan Allah bansan korafi tunda yace bazakizo ba to ki hakura" "shikenan" tafada ba ason ronta ba, bayan sungama waya, ta kwanta kawai, wayarta ce tayi kara, tajanyo ta, ganin sis Yasmeen yasa tayi saurin dauka, "hello Yasmeen ykk" "lafiya lau sister ya jin dadi" "komai Lafiya ya yaya Jawad" "yananan yanzu ma yafuta" "Muhsin yazo miki kuwa" "ai Muhsin bezo ba, kinsan yafara zuwa school shiyasa anzama manya" "ah ah lallai kam nima naso nakoma school dinnan" "ke kina amarya zaki fara school" "to ai angama amarci" "ah haba dai, ke kinsan kuwa yaya Ammar yatafi London " "London kuma aunty Aisha ta tafi ne" "eh ai tare suka tafi" "harda aunty Ilham din kenan" "ah ah aisun rabu" "me tayaya" "wlh tsautsayi yakamata tana lesbian" "what Yasmeen lesbian fa" "wlh kuwa ai ta cuci kanta dai" "tab Allah ya sawwake, kuma munyi waya da Mamy harda ma Hajiya amma duk basuyimin zancen ba" "to ai kinsan ba abunda za a dinga yaya dawa bane, ina amaryarki" "amarya kuma" "eh mana ba ance yaya Ahmad yayi aure ba" "tana nan tana falour" "oh manta ban yimiki ya hakuri ba naji anyimuku mutuwa" "oh da godiya" "yaushe zakizo kuwa" "kai gaskiya banajin zanzo" "toko dai angamu ne" "me din" "ciki mana" "ohh ni fadima rufamun asiri" "bakyaso ne" "uhmm ke dai kya haifa mana" "to ai shikenan" daga haka sukai sallama
bayan Ahmad yatashi daga office, yawuce gida, dan yaji labarin Ilham na gida, koda yaje samunta yayi, tana mopping, tsayawa kawai yayi yana kallonta dan yasan ko bedroom dinta sedai a gyara mata, "yaya Ahmad ina wuni" "lafiya lau zauna muyi magana" zama tayi ya kalleta yace "yanzu dan Allah Ilham me kikayi kenan" "dan Allah yaya Ahmad kabar maganar nan, wlh bansan ana fada ni kaina inajin kunyar abunda na aikata" "shikenan ai tunda har kin gane kuskuren ki" Mom ce tafuto, "ah Ahmad kaine" "eh Mom ina wuni" lafiya lau ta amsa tana zama, "ya matan naka" "sunanan kalau Mom" "nace yaushe zaka kawomun Zuhura ne nan ta wuni" "Mom ai zasuzo harda Nafeesa ma" "kaji nama zancen Nafeesa" "toh Mom ai dole tare zasuzo" "kaga nidai kawai ka kawomun Zuhura gobe ta wuni" "to Mom zansa driver yakawo ta" "au kai bazaka kawo taba" "Mom banda lokacin kawota ne" "yaya nima inason naganta don na muzguna mata lokacin muna gidan Mamy" "Mom bara na wuce kawai" "to a sauka lafiya" daga haka yamike yafuce, kallon Ilham Mom tayi tace "nikam se nake ga kamar Ahmad ya sauya ko" "saboda me kika ce haka Mom" "naga yacca yakeson yarinyar nan Zuhura amma har ince yakawota, yace bashi da lokaci" "to Mom watakila dagaske bashi da lokaci" "to Allah ya sawwake"
bayan tayi sallar magariba, ta sauko, bakowa a falourn, amma yayi kaca kaca, ledojin alawa da chocolate birjik a falourn, gyaran falourn tashigayi, yayi tsaf ta kunna turaren wuta, bayan tagama ta nemi guri ta zauna, Ahmad ne yashigo falourn, tana ganinshi, ta mike tana nufarsa, saurin dakatar da ita yayi dacewa "kinga bana bukata" yafada fuskarsa a hade, Nafeesa ce ta futo, sanye da riga da wando, kanta ko dan kwali babu, yasha gashin doki, tanufo Ahmad tana fadin "sweet ashe kadawo" janyo ta yayi jikinsa yana fadin "nayi kewarki fa" "nima haka, muje nama wanka" "gaskiya kam ina bukata" daga haka suka wuce rungume da juna, baki sake Zuhura tabisu da ido, batai aune ba taji hawaye yafara wanke mata fuska, kukan bakin ciki tafara, tana rokon Allah ya kawo mata mafita, dan tabbas yaya Ahmad ya sauya, tananan zaune taji dariyarsu suna saukowa, da sauri tayi maza ta goge hawayenta, "yakamata kaci abinci yanzu" "duk yadda kika ce gimbiya ta haka za'ayi" dining suka nufa, tazuba mai abincin, yafara ci kallonta yayi yace "bazakici abincin bane" "no bana sha'awar abincin, bara nasa yarinyar can tamun sakwara da miyan ganye ita nake sha'awa" "ok kisa tamiki mana ai gata can a zaune" "Zuhura kike ko meye zonan" ba musu Zuhura tamike tanufi inda suke, a yatsine Nafeesa ta kalleta tace "jeki dafamun sakwara da miyan ganye, yanzu ina jiran ki" kallonta Zuhura tayi kana tace "gaskiya yanzu bazan iya ba dare yayi" "to Sweet kaji kaime cewa tayimun gashinan ta nunama ban isa da ita ba" kallonta yayi fuska a hade yace "jeki yimata abunda tasaki" "amma yaya ahm" bata kai maganar ba ya daka mata uban tsawa da cewa "dallah bansan dogon surutu kije kiyi abinda aka saki" kitchen din tanufa, tana shiga tafashe da wani kuka, me ban tausayi, seda taci kukanta takoshi kana tafara girkin, yana gama cin abincin, suka koma falour, suna kallo, bayan tagama tazuba, tafuto, suna zaune a kujera daya, tanakan cinyarsa, karasawa tayi ta ajiye kan centre table tajuya zata wuce, "nikikeso nazuba dakaina" dawowa tayi ta zubamata kana tamika mata, bayan ta karba tace "zauna nagama kikai kitchen" ba musu tanemi guri ta zauna, kallon Ahmad tayi tace "sweet kabani naci" "ok to kawo" ya karba yafara bata abaki, bata wani ci sosai ba tace ta koshi "ki kara mana kinga fa baki ci abinci ba" "ah ah nidai nakoshi" "ok to, ke dauko mata ruwa" yafada yana kallon Zuhura, mikewa tayi tadauko ruwa a fridge ta bashi, yabude yabata tasha kana ya ajiye, "dauke kikai kitchen" mikewa tayi tadauka tanufi kitchen din, tana kaiwa ta wuce bedroom dinta, tana zuwa ta kwanta saman bed tana kuka kamar ranta ze futa, tana fadin "yaya Ahmad mena maka meyasa ka sauya" maganar Maryam ce tafado mata, hakan yasa tamike tashi ga toilet tayo alwala, ta tadawo ta tada salla, sallah ta dinga jerawa, harseda taji kafarta na neman rikewa, ta bingire a gurin, bacci yadauketa,
Ahmad kam tamkar rakumi da akala Nafeesa ta maida shi, koda suka nufi bedroom dinta, ko tabata be isa yayi ba se ta bashu umarni, haka kuma yake bin umarnin nata, se yadda tace nan yake tabawa, data gajima, hankadeshi tayi tana fadin "nika kyaleni haka bacci nakeji" ba musu kuwa ya zame jikinsa, yakoma gefe, wayar Nafeesa ce tadau kara cikin dare, tana dubawa taga Mommy, dauka tayi tana fadin "Mommy lafiya kika kirani cikin daren nan" "ke Nafeesa, boka fa yace kije gobe da sassafe" "Mommy saboda me" "au tambayata kike, karkije zauna, tunda bakyason zama sarauniya a gidanki" "to Mommy zanje, ammafa dan naga aikinsa yana ci ne shi yasa dan wlh Mommy se yadda nayi da Ahmad yanzu" "to kin gani seki daure kema kije kamar yadda ya bukata" "to shikenan Mommy seda safe" daga haka sukai sallama,
Chapter 54 · 0% Book details