← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 97

Sashe 84

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

SOYAYYA DA IZZA

Story and writing by

Hadizatu
Mrs (KD)

Ina masu bibiyar books dina
to ina muku albishir da sabon book dina
dana fara rubutawa
me suna YAN BIYU NE ina baku shawara ku bibiye book din nan
dan akwai chakwakwa kiya kala kala zaku nishadantu
zakuma ku wa'azantusosai kudai kawai ku bibiye kafun free page yakare ku biya kan naira
300 kacal ba tsauwalawa
ina alfahari daku
masoyana
kune kwarin gwuiwa ta
i love you so much
my pans
ina godiya da addu'o'in ku
dayacce kuke yabon book dina
duk da shine nafarko, gudiya buhu buhu
nice taku har kullum Hadizatu wacce kukafi sani da (MRS K D) kucika da bibiyata nukuma zanci gaba da nishadantan daku
DOMIN SHIGA GROUP DIN SOYAYYA DA IZZA KA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA
https://chat.whatsapp.com/FPb99RjggTbAcCFg1aFrVx
DUK ME BUKATAR SOYAYYA DA IZZA YA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA
https://whatsapp.com/channel/0029VahPZYb6WaKlZQvivt0J
page 67
______________________________________________________________________
_____________________________
_________________________________________________Gaba daya ranar Ahmad kwanan farin ciki yayi, saboda yana ganin lokaci yayi shima da zuciyarsa zata samu nutsuwa ya zauna shida matarsa du haifi yara, yau takama zewuce Abuja saboda aikinsa, dama Mom nata kiransa wai ya taga ya dade be dawo ba, yace mata ze dawo yau, harya fada mata maganar yasamu mata yau su Abba ma zasuje neman masa aurenta, bakaramun farin ciki tayi ba saboda ita kanta ba ta san ganin sa haka, haka ta dinga mai addu'a tana sakamai albarka, suna gama waya da Mom yatashi yashirya, dan lokacin 9:00pm har tayi kuma yanason yabiya gurin Maryam kafun yawuce, bayan yagama shirinsa tsaf yafuto, su Hajiya ya tarar da Mamy zaune a falour, ya karaso ya gaida su suka amsa Mamy na tsokanarsa da ango ango, bece komai ba sedai yayi murmushi, Abba ne yafuto cikin shirinsa nafuta, Ahmad yagaidashi bayan ya zauna, Abba yace "seka sanar da yarinyar tafada ma iyayenta yau zamuzo tambayar auren" "to Abba dama inason kafun nawuce Abuja nabiya ta gidan su" "eh hakan yayi, zankirawo daddy dinka nasanar dashi tunda kaga be saniba" "gaskiya kam yakamata Allah yasa ayi damu" suka amsa da ameen, Jummai ce tazo ta sanar dasu breakfast ya kammala, hakan yasa suka mike gabadaya suka nufi dining din
LONDON
kallonshi takeyi ko kiftawa babu tanajin sonsa nashiga zuciyarta, shikam ya lura da kallon datakeyi mai, yana ganinta ta cikin mirror, seda yagama shiryawa tsaf kana yajuyo yana kallon yace "yadai naga kinata kallona kona sauya ne" murmushi kawai tayi ta sunkuyar dakanta tana fadin "sosaima" inda take zaune yanufa shima ya zauna kusa da ita yana janyota jikinsa, ta kwantar dakanta kan kafadarsa, yace "fadamun mena sauya" "gaba dayanka ka sauya idan kana wani abun senaga kamar ba yaya Ammar din da bayason magana ba bayason raini" dariya yayi sosai kana yace "to ai kece nan kika sauya ni" dagowa tayi ta kalleshi tana fadin "nikuma" "eh mana da ban hadu dake ba toda bazan sauya ba watakila zanta zama ne a yadda nake" "toni taya akai na sauya ka" "ta soyayyar kiana wifey" fuskarta ta boye cikin kirjinsa tana murmushi "wlh Zuhura ina matukar kaunarki, da ban sameki ba da bansan yazanyi ba, ranar da Mamy ta sanar dani kezan aura wlh kwana nayi ina salla ina godewa Allah, dan Allah kema ki daure kisoni" "yaya Ammar ka kai namiji wanda ba macen dazata ganka taji bakai mata ba ba abunda baka hada ba komai kanadashi, dama ni kawai hade fuskar kane banaso kuma tunda kadena ai shikenan" "eh mana ai dama saboda kada ku rainani ne, yanzu kuwa kinga ina zan hadewa matata rai dare yayi tajuyamun baya" dariya tayi sosai kana tace "to kai kuma abunda yademaka kenan" "ah ah idan kina fushi dani ma ai babban tashin hankali ne" shiru tayi tanajin kalamansa har cikin ranta, rigarta ya daga ya dora hannunsa kan cikinta yana kallonta, kana yace "wifey kamarfa hakarmu bata cimma ruwa ba" kallonshi tayi dan bata gane me yake nufi ba "eh mana naji haryanzu shiru baby dinmu bezoba" kunyace ta kamata ta rufe fuskarta da hannayenta, "inga dai sena kara karfin aikin nan" zamewa tayi daga jikinsa tana tureshi tace "ni banaso gaskiya bazaka karamunba ma" janyota yayi yana dariya yace "matsoraciya bansan se yaushe zaki waye ba" tura baki tayi tana fadin "bakasan wahakar da nakeji ba shiyasa" tafada a marairaice "watarana da kanki zaki nema ai" wayarsa ce tadau kara, hakan yasa ydauko ta yana dubawa, sunan Ahmad yagani, kamar baze dauka ba dan besan dame Ahmad din yazo mai ba, ganin Zuhura ta kafeshi da ido yasa yadauka yanasa wayar a speaker, daga cikin wayar Ahmad yace "hello abokina ya kake ya gida ya iyali" da mamaki Ammar ya amsa mai da lafiya lau "inaso nama wani albishir ne" "name kuma" "nasamu matar aure kuma kawar Zuhura ce Maryam" "yaya Ahmad dagaske Maryam zaka aura" Zuhura tafada "ohhh ashe kina kusa, dagaske ita zan aura ta yarda zata aureni, naga itama tanada kalan hakayenki bata da matsala, saboda haka yanzu mu manta da komai mu koma kamar da mucigaba da abotarmu Ammar haka Allah yatsara kowa da matarsa" "alhamdulilah amma naji da
in hakan Allah yasanya alheri yayi jagora" "kai yaya Ahmad wlh naji da
in lamarin nan Maryam mutuniyar kirki ce wlh zata kula da kai sosai Allah yasa dai ayi damu yaushe ne" "badai mu tsayar da lokaci ba tukun" "shikenan idan an tsayar zanzo" kallonta Ammar yayi yace "ohh harkin yanke shawara baki tambayi mijinki ba" "kai yaya Ammar nasan kaima ai zakaje kumafa kaga aminiyata ce banda kawa kamarta, ga Yasmeen ma takusa haihuwa kaga semunje kawai" hancinta yakama yadan ja tasaki yar kara kana yace "shikenan Ahmad zamuyi waya Allah yasanya alheri" "ameen nagode" daga haka yakashe wayar, "kai yaya Ammar naji da
in lamarinan sosai kuma nasan Maryam zata kuka da yaya Ahmad sosai" "kema seki kula danaki mijin ko" yafada yana mata wani irin kallon da takasa fassara shi, da sauri tace "lah yaya Ammar lokaci na tafiya baka tafi office ba muje kayi breakfast kawuce ko" tafada tana mikewa takama hayar futa, shikam da ido yabita yana murmushi kafun shima yatashi yabi bayanta, tana futa ta tarar da aunty Aisha zaune ita kadai a falour dan duk yara sun wuce school hakama mijinta yajima da futa office, gaidata tayi ta amsa, sega Ammar ma yafuto, shima gaida ta yayi ta amsa tana fadin "wai dama baka tafi office ba" "eh aunty tadan rike nine" Zuhura dake hadamai breakfast kan dining tajuyo tana kallonsa jin abinda yace, "atoh yayi " aunty Aisha tafada tana cigaba da danna wayarta, shikam dining din yanufa yana kallonta yana murmushi, itakam ta hade rai tacigaba da abunda takeyi, seda tagama zuba mai ta ajiye mai a gabansa zata wuce ya kamo hannunta, yana zaunar da ita "ina zaki kuma kizauna muyi breakfast mana" "haka kawai ka kara cewa nina rikeka" murmushi yayi yace "to ai dama kece oya bani breakfast naci" "gashinan na ajiye ma" "oh bazaki ciyar daniba, shikenan nafasa breakfast din idan naje office akwai nurses zasu taimamun nayi" yafada yana hade rai, wani takaici ne yakamata batasan sanda tafara debo abincin acokali tana kaimai baki ba, shikam murmushi yayi yana karba, ahaka ta dinga bashi yanaci harya gama, kana yatashi yace tazo ta rakashi yawuce, haka tamike suka fuce, ita dai aunty Aisha tana kallonsu, har bakin mota ta rakashi, fuskarta a hade tanata kumbure kumbure, dariya yayi yana kallonta yace "kisaki fuskarki mana se wani hade rai kike" "nika barni" "to na barki sena dawo" yafada yana kokarin shigewa mota, "katuna da maganar mu tajiya" "wacce kenan" "banason nurses dinan su dinga rabarka" "shikenan aikince bakya so kuma baza a karaba" "yawwa nagode adawo lafiya Allah yatsare" tafada tana murmushi, da ameen ya amsa yana shigewa motar, harya fita tana tsaya, tana daga mai hannu, kana takoma ciki
horn din motar Yasmeen Amira taji, hakan yasa tamike da sauri tana lekawa ta window, hango Yasmeen tayi tabude kofar motar tafuto, ga cikinta yayi girma yazama kato dan ta shiga watan haihuwarta, daker take tafiya, falourn tashigo da sallama, dagudu Amira ta mike ta nufi gurinta tana mata sannu da zuwa, ta karbi back din hannunta, zama Yasmeen tayi tana fadin "Amira ina school din naganki a gida" "yaya Yasmeen ai exam din WAEC muke yau munada interval ne" "yawwa kyama rakani asibiti dan kwana biyu nan ina ciwon baya" "ayyah sannu yaya Yasmeen" "ina aunty take ne" tana kitchen, daidai lokacin Inna tafuto, karasowa tayi tanayiwa Yasmeen sannu, itakuma Yasmeen tafara gaidata, ta amsa tana tambayarta lafiyarta, wayar Amira ce tadau kara, Yasmeen ta kalleta tace "yaushe kikai waya kuma koki sanar dani" "kai yaya Yasmeen jiyafa yaya Mahmud yabani" "jiya yayansu yabata wlh nibanso yabata ba daya bari tagama makarantar" "uhmmm kedai aunty kiyi shiru kawai nan gaba zakisan komai" batare da Inna takawo komai a zuciyarta ba tace ai shikenan, mikewa Amira tayi Yasmeen ta kalleta tace "ina zaki kuma" "yaya Mahmud ke kirana awaya ina zuwa" "nidai ki gama kizo ki rakani muwuce asibitin nan" "asibiti zakuje" "wlh aunty bayana nakeji yanamun ciwo kullum" "ai watan haihuwarki me yayi shiyasa dole kidingajin irin Wadannan ciwu kan, ciwon baya kafa da dai sauransu" "wlh aunty har na matsu na haihu nagaji da cikinnan" "Allah dai yasaukeki lafiya shine kawai kiyi ta addu'a muna tayaki" da ameen Yasmeen ta amsa

SOYAYYA DA IZZA

Story and writing by

Hadizatu
Mrs (KD)
Chapter 84 · 0% Book details