← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 97

Sashe 57

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina masu bibiyar books dina to ina muku albishir da sabon book dina dana fara rubutawa me suna YAN BIYU NE ina baku shawara ku bibiye book din nan dan akwai chakwakwa kiya kala kala zaku nishadantu zakuma ku wa'azantusosai kudai kawai ku bibiye kafun free page yakare ku biya kan naira 300 kacal ba tsauwalawa ina alfahari daku masoyana kune kwarin gwuiwa ta i love you so much my pans ina godiya da addu'o'in ku dayacce kuke yabon book dina duk da shine nafarko, gudiya buhu buhu nice taku har kullum Hadizatu wacce kukafi sani da (MRS K D) kucika da bibiyata nukuma zanci gaba da nishadantan daku DOMIN SHIGA GROUP DIN SOYAYYA DA IZZA KA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA https://chat.whatsapp.com/FPb99RjggTbAcCFg1aFrVx DUK ME BUKATAR SOYAYYA DA IZZA YA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA https://whatsapp.com/channel/0029VahPZYb6WaKlZQvivt0J page 53 _______________________________________________________________________ _____________________________ ________________Haka rayuwa taci gaba da tafiya, yau kimanin kwana uku kenan, batasa Ahmad cikin idanunta ba, ko kiranshi tayi a waya baya dauka ma, hakan yasa bata da aikinyi se kuka, idan abun ya ishe ta takira Maryam tafada mata, ita kuma Maryam takara bata hakuri, su Ahmad kam yana can tare da Nafeesa suna wancan club waccen hotel, danko aiki ta hanashi zuwa, ballantana kuma yaje gida gurin su mom, idan taga an dameshi dawaya ma seta karbe wayar tashi gaba daya, shi kuma bashi data cewa, duk abunda tayi dai-dai ne a gurinsa, dan ko catayi ya fada wuta to a shirye yake daya afka, dan asirin yashiga jikinshi sosai, sukansu su Daddy hankalinsu yatashi ganin Ahmad har yayi kwana uku bezo inda suke ba, hakan yasa suka fara kokonton anya kalau kuwa, kuma idan sukai waya da Zuhura se tace suna lafiya, idan akace ina Ahmad se tace yaje office, hakan yasa abun ya daure masu kai, itakam Zuhura har wannan lokacin bata bari kowa yasan halin datake ciki ba, se Maryam kadai, yau Friday yau takama Mahmud yayan Yasmeen ze dawo daga kasar waje, hakan yasa tun safe Yasmeen tana gida, suna shirye-shiryen tarbarsa, itakam Amira bama ta gidan tana school dan yanzu lesson take tsayawa Alhamis da juma'a, se 5:00pm driver ke zuwa yadaukota, karfe 2:00pm jirginsu Mahmud ya sauka a Nigeria, Daddy ne yaje yadauko shi dakansa, yatawo dashi gida, kana ganinsa kaga Yasmeen dansuna kama, sedai kawai ta nuna mai fari, dashi bashida haske, murna kamar me gurin Yasmeen yaya Mahmud yadawo, seda yaje yayi wanka kana yafuto suka nufi dining, abincin dasuka hada mai suka zuba mai, aikam yafaraci dama yayi missing din abincinmu na nan, haka suka dinga ci suna hirar yaushe gamo, harda Inna , Halifa kam yana kusa da yaya Mahmud tamkar dama yasanshi, bayan sun kammala Daddy yace shi ze futa, saboda zasuyi meeting, Inna ce ta rakashi har wajen mota kana ta dawo, Mahmud ne ya kalleta yace "gaskiya aunty kinaji damu harma Daddy" murmushi kawai tayi tace "ai dole naji daku yarana" murmushi sukai su duka kana Mahmud yace bara yadauko musu tsarabar su, haka ya shiga ya yadauko akwati katuwa, yashiga bawa kowa nasa, harda Halifa, seda yagama Yasmeen tace "yaya Mahmud karka manta da kanwar mu mana" "wa kenan" "Amira mana tana school amma 5:00pm tanayi zata dawo" "ok to idan ta dawo se a bata nata" daga haka yashigar da akwatin ciki, yafuto yace zeje wani guri yadawo, "Hajiya ina lafiya fa" "kai Zuhura anya kuwa jikina nabani wani abu" "ayyah Hajiya nifa kalau nake yaushe zakizo keda Nadra" "gobe nakeson zuwa abujan amma ina ganin zan barshi se next week" "dan Allah Hajiya kizo naganku nayi kewarku sosai" "shike nan zamuzo goben" "Hajiya ku taho da Muhsin" "base zezoba Muhsin anzama saurayi" "to Hajiya ina nan ina jiran ku zan shirya muku kayan dadi" "dariya Hajiya tayi kana tace "kinsan ni wannan abincin naku basonshi nake ba" "ai nasan irin wanda kike so" "tom shikenan to" daga haka sukai sallama, knocking taji hakan yasa taji gabanta ya fadi, ko su Ahmad ne suka dawo, jiki a mace ta mike tabude kofar, Ilham ta gani hakan yasa tasaki ajiyar zuciya tana murmushi tace "aunty Ilham sannu da zuwa shigo" shigowa tayi ta zauna, ita kuma Zuhura ta nufi kitchen, ta dauko mata ruwa da lemo, tazo ta ajiye mata, "aunty Ilham ina wuni" "lafiya lau Zuhura ya gida" "lafiya lau" "ya mutan gidan" "duk suna lafiya" lemon tazuba tasha kana takalli Zuhura tace "yanaji gidan shiru ne ina Nafeesar" "am am dama tadan futa unguwa ne" "ya yaya Ahmad din kuma" "yana lafiya" "kwana biyu baya zuwa gida gurin Mom" "Allah sarki dama am dayake dama yadanyi rashin lafiya ne ta kwaan 2 to shi yasa bama yafuta se yau ya samu sauki yafuta office" yacca take maganar kasan bata da gaskiya, ita kanta Ilham din ta gane tana boye mata wani abu, kuma dama tazo ne dantasan halin da ake ciki, gashi kuma Zuhuran taki fadamata komai, hakan yasa tace "bara nawuce dama hanyace ta biyo dani" "kai aunty Ilham bazaki bari sedan anjima ba" "ah ah zandanyi wani abu a gida ne" daga haka tamike, har bakin motarta Zuhura ta rakata, seda ta tafi kana tashigo ciki, tana hamdala da bata gane wani abu ba game da abunda ke faruwa, 5:30pm Amira tashigo cikin gida, a gajiye tayi wani wargajen wargajen da ita, hakan yasa tana dawowa tawuce dakinta danta watsa ruwa, Mahmud ne yashigo shida abokinsa kuma amininsa Adam, bakowa falourn Inna tashiga bedroom dinta ianta dan kwanta, ita kuma Yasmeen jitai gaba daya zuciyar ta na tashi, shine itama ta tafi bedroom din Inna danta huta, Halifa ma yana tare dasu, "to bakowa falourn ma" "toko sun futa ne" "no bazeyuwu su futa ba yau fa nadawo kuma sesu futa su barni" dariya Adam yayi yace "sekace wani jariri da bazasu futa su barka ba" "bara dai nakira aunty ku gaisa nasan suna ciki" wucewa yayi, besan dakinta ba, hakan yasa yatura dakin Amira yashiga, daidai lokacin data futo daga wanka daure da tawul a kirjinta, tsayawa yayi yana kallonta kamar wanda yaga wata aljana, saurin sakin kara tayi tana shigewa cikin labule, dariya tabashi hakan yasa yayi murmushi yakarasa inda take, itakam ta rumtse ido, se ihu take tana fadin "wayyo aunty aljani yaya Yasmeen kizo ki taimake ni aljani" daga cikin labulen ya fincikota, har tawul din jikinta ya zame kasa, aikam takara rusa wani ihun, jin karar yake har cikin dodon kunnensa, hakan yasa yakamota, ya toshe mata baki da hannunsa, yana fadin "ke saurara haka niba aljani ba ne" itakam kiciniyar kwace kanta takeyi danta dau tawul dinta ta rufe jikinta, bakinshi yakai kunnenta yace "idan baki tsaya ba bazan sakeki ba" jin haka yasa ta tsaya, shi kuma ya sausauta rikon daya mata, akam tuni ta kwace, ta duka tadau tawul din tadaura, shikam inbanda aikin kallon ta ba abinda yakeyi, "dan Allah kafutarmun daga daki" kallonta yayi yace "ok zan futa, amma ina ne dakin aunty" "yana can gaba ta hannun dama" "ok" yafada batare daya motsa ba kallonta kawai yake "katafi mana" kallonta yake yana futa da baya da baya, harya fuce, ajiyar zuciya ta sauke, jitai yakara bude kofar, hakan yasa ta zare mai ido tace "meye kuma" "kawai dai zan kara kallon ki ne kadan" harara ta galla mai yayi murmushi kana ya rufo mata kofar, jin muryoyinsu yayi a falour suna hira, hakan yasa yakoma falourn, "aunty ashe kin futo ma" "eh Mahmud" "ina Yasmeen din" "batajin dadi ne tana ciki" "to ai kamata yayi tazo ta tafi asibiti" "Amira take jira tazo ta rakata asibitin" "ok to su shirya sena kaisu" "bara nayima Amiran magana tun dazu ta dawo amma kamar me sauya fata daga cewa bara tayi wanka" Inna tafada tana wucewa, Mahmud ne ya kalli Adam yace "kai abokina nafayi gamo" "wanne irin gamo kuma" "wata yarinya ce" "a ina kuma" "anan gidan kuma yanzu, abokina yarinyar nan karshe ce kallon surarta zesa mutum ya haukace wlh" "au kai jikinta ka tsaya kana kalla" "kai dalla can taya za ai nayi haka kawai mistake ne tafuto daga wanaka tawul din jikinta ya cire" rufe baki Adam yayi yace "wato kaga yar mutane haka" "eh mana gaba daya tasani wani hali" futowar su ce takatse musu hira, cikin magana asa asa yace "Adam kagantacan wacce ta riko Yasmeen" "wow yarinyar kyakyawa ce" karasowa sukai, Inna tace "Mahmud sun shirya ka kaisu" "ok aunty" "aunty wai wannan mutumin ne ze kaimu" Amira tafada tana galla mai harara, "ke bansan shashanci yayanku ne to" zumbura baki tayi gaba, shi kuma se kallonta yake yana murmushi, daga haka suka fuce tana rungume da Yasmeen suka shiga mota, tunda suka tafi yake kallonta ta mirror din motar, dasun hada ido seta galla mai harara, shi kuma yasakar mata murmushi, "abokina nifa yau naga wata yarinya haihuwar uwarta" zuciyarta ce tafara tafasa jin abunda yafada, ta cije baki tana kara falla mai harara, "kai haba abokina bataji kunya ba" "kasan su matan yanzu ai basu da wata kunya, Allah ne ya taimake ta da yau tayi kwanan jinya, kasan nidin akwai tsoron Allah" "gaskiya dai kadaure" "ya isa haka" tafada cikin daga murya, "toh yarinya me akai kuma" "bansaniba kashigo har dakina kaciremun tawul kace wai bani da kunya bayan kaine dan iska" "wai dama kece wadda yaga jikin ki, Allah sarki sannu fa" harara ta galla musu kana tace "aikin banza kawai" sukam dariya suka dinga mata, Yasmeen najinsu amma bata iya gane me suke nufi ba saboda ciwon datake ji, harsuka iso asibitin tana galla musu harara, riko Yasmeen tayi suka shiga ciki, sukuma suka zauna a mota dansu jirasu, LONDON bangaren Ammar kuwa komai na tafiyar mai dai-dai, aikinsa yake tukuru, dan yanzu yafi maida hankalinsa kan aikinsa, lokaci zuwa lokaci, sukan yi waya dasu Abba, da Hajiya, Mamy kam da Jawad kullum sesun kirashi a waya, ba laifi tunanin Zuhura ya ragu a zuciyarsa, duk da haryanzu yanajin sonta, amma daya tuna matar wani ce se ranshi ya baci, hakan yasa yanzu duk ya dena zaman bata lokaci tunaninta, a asibitin dayake aiki, yan mata nata binsa amma sam ko kallo basu ishe shi ba, dan bega wata mace daze so ba, bayan Zuhura, dan ita kanta beson
Chapter 57 · 0% Book details