← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 97

Sashe 42

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ammar ga abinci can nakawo ma ka tashi na zubama" wani kallo ya mata kana yace "nafada miki ina bukatar abinci ne" "baka fadamun ba kawai dai naga yadace nakawoma abincin amatsayina na matarka hakinane nakula dakai" wani irin haushinta ne ya cika zuciyarsa, data kira kanta matsayin matarsa "to kwashe bana bukata" "yaya Ammar yakamata ka rage wulakancin nan daka ke yimun, saboda yanzu mu ma aurata ne, zamuyi zama wanda bashi da iyaka" "kinga jeki bana bukatarki" "dole ne ka bukace ni saboda ni matar kace yanzu" tana kaiwa nan tafuce, dafe kansa yayi yanajin wani iri azuciyarsa, Nadra Ahmad yatura takira mai Zuhura, aikam dagudunta taje ta sanar da ita, ba jimawa tafuto tana gyara zaman mayafinta, dubashi tashigayi, bata ganshi ba, jitai anjanyota, tafada jikin mutum, tsam ya rungume ta ajikinsa, itakam tsoro ma yabata, tafara mutsu mutsu, tunawa dayayi ita farin shiga ce yasa yasake ta, yana kallonta yace "queen i miss you, nayi kewarki sosai, ina sonki, ke kam kamar ma baki damu dani ba" "yaya Ahmad nadamu mana" "to meye sa baki kara kirana ba" "namanta ne shi yasa" "ok kin manta dani ko" "no yaya Ahmad ba haka bane" "ok kinci abinci" "ah ah yanzu dai zanci" "ok idan kinci kizo zan hadaki da mom dina ku gaisa" zaro ido tayi tana fadin "yaya Ahmad kabari ba yanzu ba inajin kunya nidai" hanci ya lakace mata kana yace "to aikuwa kidena dan yau dole sekun hadu" baki tabude zata kara magana ya dakatar da ita dacewa "kije kici abinci inajiranki" daga haka yabar gurin, bayan takoma har an kawo musu abinci dayawa, hakan yasa tazauna taci kana tasha lemon, itama Yasmeen din abinci ta dawo ci tana kammalawa takara fucewa, ganin haka yasa Zuhura ma tafuce, yana zaune kan wata kujera, yana hangota yamike, yace "anya kuwa kinci abincin dayawa" dagamai kai tayi, kana yace "to muje" "amma yaya Ahmad kai kaci" "aini ganin kima ya isheni" daga haka yaja hannunta suka wuce, tabaya suka shiga, yanufi bedroom din mom dinsa, ba kowa hakan yasa yadau wayar sa ya danna kiran mom, yace da ita dan Allah ta zo bedroom dinta yanzu, amsa mai tayi kawai, batare da wani tunanin ba, "queen yanzu zatazo" bayan tazo ta tadda su zaune, cikin mamaki take kallon Zuhura kana tace "son wace wannan kuma" karaswa yayi yakamo hannun mom din ya zaunar da ita yace "mom wannan ce Zuhura wacce nabaki labari yarinyar danake so" wani kallo ta watsa mai wanda yasa shi saurin yin shiru, bude baki tayi tace "ok bamu guri zanyi magana da ita" zuciyar sa ce ta fara dukan uku uku, danyasan ba abun arziki zata fada mata ba, baki ya bude zeyi magana , ta galla mai wata uwar harara, jiki a sabule yamike ya fuce, ita kam Zuhura kanta na kasa batasan meke faruwa ba, "ke dago ki kalle ni" maganar ta daki dodon kunnenta, a hankali ta dago batare data kalle taba, "kisani ni dana baze auri yar talakawa ba, musamman ma irinki mara asali wadanda aka tsinta a titi, saboda haka ki kyale mun dana ba sa an aurenki bane, kinzo kin like mai wama yasani ko asiri kikai mai, danku baku da aiki se yiwa ya'yan masu kudi asiri ku aure su, toni dana yafi karfinki, kije can ki koma danginki kiyi aure, ki kyale mun dana, kin wani sunkuyar da kai munafukan banza, tashi kifuce mun daga daki" ita dai Zuhura harta gama hawaye kawai takeyi, jiki a sanyaye tamike tafuce, yana ganinta yayi saurin nufo ta, yana fadin "queen meya faru" hawayen datake rikewa ne ya kufce akaro na ba adadi ya zubo, kara gigicewa yayi yana fadin "queen meye meya faru" "bakomai Please ka barni kawai" daga haka tawuce tabarshi agurin, bedroom din yakoma yasami Mom din tana kokarin futowa, "haba mom me kikayi haka" "abunda yadace" "mom inasonta zaki ki iya rasani idan kika rabani da ita" "dama mana ai nasan ta riga ta asirce ka" daga haka tawuce tabarshi a tsaye, barin gurin yayi, bedroom dinsa yawuce, jin muryoyin mutane dayawa hakan yasa yajuya, yakoma yatafi dakin baki dake gidan ya kulle, zufa ce ke keto masa tako ina, yana tunanin mafutaa, zuciyar sa ce tafara rayama yaje gurin iyayensu maza ya sanar dasu, hakan yasa yatashi yabude yanufi part din Daddy inda gabadaya iyayensu maza suke, dan bayajin ze iya bacci batare daya magance matsalar nan ba, kofar yatura ya shiga, Daddy yana ganinsa yasan ba lafiya yake ba, zama yayi gabansu, kowa ido yazuba mai, yana jiran yaji me zece, Abba ne yakalle shi yace "Ahmad kana lafiya kuwa" "Abba bana lafiya mom tanaso ta rabani da farin ciki na" "kamar yaya kenan" "Daddy mom tace batasan yarinyar dana keso tace bazan aure taba, kuma Daddy indai ban aure taba zaku iya rasani" numfasawa sukai gaadaya yan falourn, "to wacce yarinya kenan kake so" "Abba Zuhura ce Daddy inasanta sosai" "Zuhura kuma" Abba ya tambaya cikin mamaki, "to ita tana sanka" "eh uncle tana sona" "wacece ita Zuhuran " "agidan Abba take" "Alhaji usman wacece ita" labari Abba yashiga basu tun farko har karshe, sun jinjina abun kana Daddy yace "ka kwantar da hankalinka ba ita zata daura ma aure ba mune nan dan haka duk yarinyar daka kawo indai kanasonta tana sonka to zamu daura muku aura" "kwarai kuwa Ahmad ka kwantar da hankalin ka nine guardian dinta, kuma nabaka ita" wani dadi ne ya ziyarci zuciyarsa nan da nan zuciyarsa tamkar an zubamai kankara, "yanzu dan dai bata kammala secondary ba, a yau zamu hada harda kai mu daura muku aure, amma tana kammala secondary da sati guda zamu daura muku aure insha Allah" farin ciki kamar yakashe shi, yadinga godiya yana musu addu'a,
Chapter 42 · 0% Book details