Sashe 34
Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
SOYAYYA DA IZZA
Story and writing by Hadizatu
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan
asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau
page 34
_________________Yau Inna tayi kwana uku 3 gidan Alhaji Aminu, bata da wata damuwa yana bata kulawa yana mata duk abinda takeso, hakama diyarsa tana girmama ta tana nuna mata so, breakfast Inna take shiryawa saman dining, bayan tagama shirya komai ta nufi daki danta kira abban Yasmeen, tana shiga taganshi ya kammala shirya wa tsaf tace "nagama shirya karin kumallo" kallonta yayi cikin kauna yace "yawwa sannunki muje tunda nagama" fucewa sukai tare, kan dining din ya zauna, ita kuma ta shiga zuba mai, bayan yafara ci, itama ta nemi guri tazauna, itama zubawa tayi tafara ci, kallon ta abban Yasmeen yayi yace "nace wai yaushe za a kawo yarannan ne"? "senayiwa Mamy magana" "ki aika driver yau ya daukosu , saboda kinga nagama musu komai na makaranta su kawai ake jira" "tom insha Allah yau zansa akawo su next week se su fara zuwa" "yawwa ko ke fa" murmushi kawai tayi, Yasmeen ce tafuto daga dakin tana fadin "la Daddy shine kuka fara breakfast bani ko" "naje dakinki naga kina bacci shiyasa" karasowa gurin tayi tare da gaidasu, amsawa sukai su duka, kana Inna tazuba mata abinci tafara ci, Alhaji Aminu ne yamike yana fadin "zantafi office naga har na kusa makara ma" mikewa inna tayi tana daukan jakar shi, futa yayi tabishi abaya, har bakin mota ta rakashi sukai sallama yatafi, dawowa ciki tayi tare da zama taci gaba da cin abincin, "aunty wai yaushe Zuhura zatazo kince itama kamar ni take ko" "eh maan kamar ke take wata kila ma shekarunku daya" "to aunty dan Allah ta dawo nan da zama mana" "ah ah baze yiwu ba kinga tana gurin Mamyn ta ita ma" "aunty dan allah tazo ko ta kwana inason nasamu yar uwa" "karki samu sedai idan anyi hutu yanzu kinga makaranta" "aunty bata gama school ba" "eh saura jekara daya ai" "to aunty tazo ko weekend ne mana" "yau kannen tane zasu zo Amira da Halifa zasu zauna tare damu anan" "Inna dagaske" "eh mana kuma kinga Amira ma da girmanta, dan ina tunanin yanzu zatai shekara 10 ko 11" "yawwa aunty shikenan yanzu nasamu wacce zamu dinga hira" hakane kam"
" sir excuse" Zuhura tafada, "ok wakike nema" "nazo gurin kanina Muhsin" magana malamin yayiwa Muhsin, mikewa Muhsin yayi yaje, "Please Muhsin calculator dinka zaka aramaun tawa taki kamawa kuma muna math" "ok bara na dauko miki" komawa yayi yadauko yamika mata" tafiya tayi shikuma yakoma ya zauna abikin shine sake kusa dashi ya kalle shi yace "Muhsin dama wannan sister din kace" "eh" "to ai itace rannan nake cema su fahad sun takura mata" saurin kallonshi yayi "eh ita ce" malamin ne ya katse su dacewa, "ya baku fara note din ba" farawa sukai, shikuma yayi gaba
"amarya ya gida ya amarci" "kai Mamy amarci kuma" "eh mana" gaisawa sukai kana Inna tace "dama alhaji ne yace yau akawo su Amira saboda ya kammala musu komai na makaranta" "ok ai ba matsala yanzu se nasa Bala driver yakawosu" "yau ina Hajiya" "Hajiya na dakinta tana hutawa, biki tambayi Zuhura ba" "ai nasan yanzu tana makaranta shi yasa" "gaskiya kam kinga ranan da kika tafi dakyar na lallashe ta" "Zuhura ai bata da dama kawai shagwaba ce irin tata" "yanzu bara nasa Jummai tamusu wanka se a kawo su" "tom shikenan se anjima" daga haka sukai sallama, Mamy ce takira Jummai tace tayiwa Halifa wanka ta shirya sa tasa Amira ma tayi wanka ta shirya, amsawa tayi tana wucewa, wankan tamusu ta shieyasu tsaf, futowa sukai, rayiwa Bala driver kwatance dan ya kaisu, yagane kwantancen nata dan haka suka tafi,
Zaune yake kan kujerar sa, tuanin yarinyar kawai yakeyi, shikansa yanzu besan meyasa yake tunanin taba, 'ka damu da ita ne shi yasa kake tunaninta' wata zuciyar kuma tace mai 'taya za ai kadamu da wata mace kai da mata ma basa gabanka' haka dai kowanne sashe na zuciyarsa da abunda yake saka mai, yau ko aikin kirki be yiba,
su Amira na shiga falourn suka tarar da Inna zaune tana kallo, aikam da gudu suka isa gurin ta, rungume su tayi tana murmushin jin dadi, "Inna kin tafi kin barmu" Halifa yafada yana kallon Inna "ba tafiya nayi nabarku ba kuma ai yaya Zuhura tana tare daku" "eh Mamy amma yaya Zuhura kullum da daddare se tayi kuka" Amira tafada kawar da zancen Mamy tayi tana fadin "me zaku ci" dai dai lokacin Yasmeen tafuto, tana ganin su ta washe baki tana karasowa inda suke tace "ashe kannena sun iso" "kin gansunan sun zo harsun fara takuramun" "ah habadai aunty ai bazasu takura miki ba" "baku gaishe taba itace Yaya Yasmeen" gaishe ta sukai ta amsa tare da fadar sunan kowannen su "kai Inna taya tasan sunan mu" Amira tafada cike da mamaki " kamar yadda yaya Zuhura tasanku to haka itama tasanku" murmushi tayi tana fadin "me kuke so yanzu" "bakomai" suka fada atare, tashi Inna tayi dan ta duba girkin data dora, sukuma suka cigaba da hira suna dariya.
Jawad ne zaune a falour shi da Hajiya, dayake yau beje school ba, Mamy ce tashigo falourn tana cewa "Jawad zokaje kadauko su Muhsin a school" "Mamy ina Bala driver"? "na aikeshi" tashi yayi yafuce motarsa yashiga yanufi school din , yana shiga yasamu guri yayi parking, yajima kafun a tashe yan secondary, su Nadra kawai aka tasa 1:30pm dan haka Nadra har ta shige mota tana zaune , karfe 2:00 dai dai aka tashesu , kallon mutanen yake dasuke futowa daga class, su uku suka futa tana tsakiyarsu, suna tafe suna hira banda ita da dariya kawai take, kallonta yake yana wasafa abubuwa dayawa, wanda shi kadai yasan meyake tunani, bata ankara ba taga fu'ad yasha gabanta, wata uwar harara tabishi da ita, saurin dago kai Jawad yayi daga jinginar da da yayi, "ke wai ke wacce irin yarinya ce ai ta binki kina share mutane" "Please dan Allah ka kyaleni katakurawa rayuwa ta" tana kaiwa nan ta bi ta gefenshi zata wuce, hanzarin shan gabanta yayi yace "ke dallah ta ishe ki ban taba dadewa ina bin yarinya haka ba seke" bata kula shi ba takara ratsawa zata shige yakara shan gaban, tayi tayi tabata hanya tashige yaki, abunne ya fusata Jawad ya balle murfin motar yafuto, fu'ad jiyay an dafa shi, batare daya juyo ba ya dauke hannun Jawad daga kafadarsa, yana kara tare ta, sake dafa shi Jawad yayi jin ankara dafashi yasa yajuyo cike da bala'i, waani wawan mari Jawad ya sauke mai, dai-dai lokacin Muhsin yakaraso gurin, dasauri yakarasa inda suke , rufe baki Zuhura tayi da tafun hannunta, "kai kasan waye ni ka daga hannu ka mare ni" "kawaye kai namare ka kuma idan kasake maimaita abunda kayi ba iya marima zanma ba hatta jikinka se yayi tsami" "zaka ga waka nara* yafada yana barin gurin, figo hannun Zuhura Jawad yayi yakaita har gurin mota yabude mota yasata ya shiga Muhsin ma yashiga , tayar da motar yayi suka bar makarantar, kallonshi Zuhura take tanaso tamai magana amma ganin yanayinsa yasa takasa, daurewa tayi tace "yaya Jawad meyesa kayi haka" daga mata hannu yayi alamar ta dakata kana yace "kinsan kina fuskantar wannan matsalar a school amma kikai shiru" shiru tayi batai magana ba, yakara cewa "Muhsin kaine babban me laifi idan ita bazata iya fada ba aikai seka fada" "wlh yaya Jawad nima bansani ba se yau" "ke kuma duk ranar daya sake miki makamancin wannan ki sanar dani wlh senamai tabo" saurin kallonshi tayi kana ta sunkuyar dakai, bayan sun isa gida yayi parking, suka futo suka shige ciki, Mamy ce da Hajiya se Ahmad daya dawo yanzu yake cin abinci, shigowa sukai, Jawad be tsaya a falour ba yawuce dakinshi, "mun dawo" Muhsin yafada , Ahmad ne yakalli Zuhura gani yayi fuskarta ba walwala Hajiya ce takalle ta tace "Zuhura yadai naganki jiki ba gwari" "bakomai Hajiya" "ko kina bukatar wani abunne Zuhura" Mamy tafada tana kallonta, a sanyaye tace "bakomai Mamy" Mamy ce takalli Muhsin tace "kai meke faruwa" "Mamy zancen gaskiya wanine yatakuea mata a school shine yau yaya Jawad ya gani ya tsawatar mai" da sauri Ahmad yadago yana kallonta, itakam mamakin Muhsin take dabe fadi marin da Jawad yayiwa fu'ad ba, "to amma in banda ke ai seki fada ai" Hajiya tafada tana kallonta, "Muhsin din ma kai ai ya kamata yafada" "Mamy nima banasaniba fa se yau" kallonra Ahmad yake tayinda itama shi take kallo, "kuje kucire uniform kuzo kuci abinci, ke kuma Nadra jeki gurin jummai tacire miki" to suka amsa su duka suna wucewa.