← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 97

Sashe 58

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

lokacin da soyayyar ta tashi ga zuciyarsa ba, NIGERIA 8:00pm, Zuhura na zaune a falour tana kallo, tana hamma dan ta fara jin bacci, kawai dai film din yana debe mata kewa, knocking taji, hakan yasa ta mike tana fa in, "ko waye da daddren nan" bude kofar tayi, su Ahmad ta gani da Nafeesa, "sannu da zuwa" tace kana tashige, suma shiga sukai ciki, Nafeesa ce ta kalleshi tace "sweet muje ciki banson ka zauna gurin yarinyar nan" daga haka ta shige shima yabita zugui zugui, kallonsu tayi cikin takaici, tace "nima bason zama daku nake ba" tunda suka shige basu sauko ba, Zuhura kam tana gama kallon film dinta ta mike tawuce bedroom dinta, tana zuwa tayi addu'a ta kwanta, zaune suke a falour gaba dayansu, Yasmeen ma tana nan saboda jikin ta, Jawad ne zezo yadauketa, dasuka je asibitin aka sanar dasu tana dauke da ciki, aikam sunyi murna sosai musamman Amira tanata murna tasamu da, kin fadawa Jawad sukai wai zasuyi mai surprise, aikam yana zuwa daukanta, bayan yashigo sun gaisa dasu Inna Amira tace mai "yaya Jawad albishirinka" "goro yafada yana dariya" "yaya Yasmeen nada ciki" kasa boye farin cikin sa yayi ya matsa kusa da ita ya riko hannayenta yana fadin "thank you Yasmeen" ba kunyar su Daddy da Inna, itakam murmushi kawai tayi mai, "to su Jawad za a zama baba" Mahmud yafada yana murmushi "kaidai ka tsaya harsena fara jikoki" "fada mashi dai Jawad" Daddy yafada yana nuna Mahmud, "haba dai Daddy ainima nasamu matar auren" yafada yana kallon Amira, suna hada ido ta galla mai harara, Jawad ne ya rungumi Yasmeen suka fuce, har wajen mota Mahmud ya rakashi sukai sallama, amota koya Yasmeen tace ashhh se ya gigice yana fadin, meya faru meke damunki ina yake miki ciwo, bayan Mahmud yakoma ciki, ya tarar da Daddy yashiga ciki, daga aunty se Halifa se Amira dasuke kallo, wayarsa ya hau dannawa lokaci lokaci yana kallon Amira ta kasan ido, wayarsa ce tayi kara hakan yasa yamike ze wuce, Halifa yayi saurin cewa, "yaya Mahmud baka bawa yaya Amira tsarabar ta ba" "ok ta biyo ni ta karba, kizo ki karba yanzu" daga haka yashige ciki, wata uwar harara ta balla ma Halifa wanda shibemasan tanayi ba, "bazanje na karba dinba" tafada ashe Inna tajita, "ke Amira na lurafa bakya girmama yayan nan naku ko, kamar yadda kike girmama Yasmeen to shima haka zaki girmama shi fiye da yadda kike mata" "nifa aunty ba abunda nace" "tashi kije ki karba kamar yadda yace" mikewa tayi rai a hade, ta wuce, tana zuwa ta tura kofar, yana zaune bakin gado yana waya, hannu ya nuna mata inda akawatin take, hakan yasa taje tadauko ta ajiye mai a gabansa, hannunsa yakai ya janyota ya zaunar da ita kan gadon, ta bata fuska tana zumbura baki gaba, seda yakusa 15mint yana wayar, har ta gaji, seda yakashe wayar ya kalleta yace "na bayar bazakizo ba ai" "aunty ce tace nazo" "ok ba zuwan kanki bane" "eh" murmushi yayi ganin yadda ta hade fuska, mikewa yayi yasawa kofar key, kallonshi tayi tace "meye hakan" "bakomai" yafada yana shigewa toilet, zuciyar tace ta harzuko tace "wai wannan wanne irin abu ne kazo ka bude mun na tafi" yanajinta daga toilet din, murmushi kawai yadinga saki shi kadai, bayan ya gama wankan yafuto, daure da tawul a kugunsa, tayi niyyar daya futo ta balbaleshi da fada, ganin shi haka yasa ta saurin juya baya tana rintse idonta, "wannan wanne irin iskanci ne" matsawa yayi kusa da ita, yakai bakinshi saitin kunnenta yace "meyasa kike mun masifa ne ko duk saboda naganki ba kaya ne" fusace tajuya tana fuskantarsa tace "ina ruwana kaida Allah nika budemun kofa nafuta" "oh baki yafemun ba kenan ganinki danai" "eh ban yafeba se akai yaya" "ok zaki iya ramawa ai" "ni haka nacema zan rama" fincikota yayi tafada kirjinsa, ya matseta tsam, kana yace "to kice kin yafemun" ta tsorata hakan yasa tace "naji nayafema cikani" cikata yayi ya nufi akwatin ya bude, yadauko mata turarurruka da maya mayay, ya bata, "na gode" "nine da godiya" "budemun natafi" inda key din yake yanuna mata , ta dauka ta bude ta fuce, murmushi kawai yakeyi, danjin shi yake cikin farin ciki, soyayyar yarinyar ta kamashi sosai, haka ya kwana da tunaninta a ransa,
Chapter 58 · 0% Book details