← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 97

Sashe 32

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

SOYAYYA DA IZZA
Story and writing by Hadizatu
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan
asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau
page 32
________________Su Mamy ne cikin mota, Mamy ce ke tuki, sunsha kunshi da lalle, ga kai nata kyalli, jikinsu su nata sheki , musamman na Inna wacce akafi gyarata sosai dan Mamy ta gayamusu amarya ce, wayar Mamy ce tayi kara, ganin my husband tasa ta murmushi tana dauke, tace "angwaye ya hidima" "gashin nan muna ta fama, wai baku dawo ba haryanzu"? "ka ganmu muna hanya ma yanzu munkusa gida" "todai yakamata ku hanzarta dan mu har an daura" "har an daura to masha allah, Allah dai yasanya alkhairi" "ammeen kudai hanzarta dan yace ana magariba zezo ya dauketa" au shi zezo ma yadauketa"? "eh yace baze wani turo abokai ba dakanshi zezo yadauketa" "lallai to ai shikenan kaga ba batun rakiya" "ah ai ba rakiya" "to dai kuyi maza ku dawo" "tom kaga ma munzo bakin gate" "to shikenan sena dawo ni" gate aka bude musu, shiga sukai , parking Mamy tayi, "maman Zuhura amfa daura" "murmushi Inna kawai tayi tana bude motar tafuta, itama Mamy futa tayi suka nufi ciki, suna shiga Hajiya ce kawai a falourn dan haka suna shiga, Mamy tazube saman kujera, tana fadin "washh Allah nagaji" "sannunku " "Hajiya sannu ya gida" "lafiya lau maman Zuhura sannuku" "maman Zuhura kije ki huta kiyi wanka kiyi sallah kici abinci" "tom" daga haka Inna tawuce, itama Mamy wucewa tayi dakinta, Inna nashiga taga Zuhura kwance saman gado tanata bacci, bata bi takanta ba tashige toilet dantai wanka, bayan tayi ta dau hijabi ta tada sallah, seda ta idar ta kara kallon Zuhura tana tace, "Zuhura tashi na dawo" tasan Zuhura da shegen bacci, hakan yasa tamike ta daka mata duka "kinfiye jarabar bacci" tashi tayi tana mutsuka ido, "au Inna kin dawo"? "kinata bacci ina zakisan nadawo" ta zare tana fadin, "kai Inna naga kamar bake ba" "to da wace, ina ya'ya na " "Inna biki tambayi yanake ba kike tambayar wadancan yaran" "to ai ke kin girma, jeki zubo mun abinci" "tom nimafa banci ba" "to nina hanaki ci" "Inna ankawo sabuwar me aiki kuma ta ita girki sosai" "to maza jeki kawomun" fucewa tayi, tana zuwa tahada musu abinci, kana tacewa dasu Amira Inna ta dawo, aikam dagudu Halifa yatafi, abincin takai musu, zama sukai suka fara ci a plate daya ita da Inna , kallon ta Inna tayi tace "Zuhura yau zantafj, inaso ki kula sakanki kisan meya dace kiyi, kinga yanzu kun girma , kulamun sa yaranan kafun nazo na daukesu" "to Inna amma ganina nake bazan iya zama ni kadai ba batare dake ba" kafadarta Inna tadafa tace "yazama dole ki koyi rayuwa ke kadai saboda ko yaushe zan kasance dake ba" hawaye ne zuka zubo a idon Zuhura tana fadin "wlh Inna bazan iya zama ni kadai ba" "aikam dole ne ki zauna" kuka take sosai ,lallashinta Inna keyi tana bata hakuri, dahaka dai har tai shiru, Mamy tana shiga bedroom dinta ta watsa ruwa tayi sallah, kana tafuto falour, zama kan kujera tayi kana takalli Muhsin tace "yima Zuhura magana takawomun abinci" "dazu ankawo sabuwar me aiki dakika nema" Hajiya tafada tana kallonta "oh tazo kenan tun waccan satin nacefa akawomun amma se yau" "ita ce na tayi gurki yau, wai sunanta Jummai" "to Allah yasa tanada tsafta kai cene takawomun abinci kaduba kitchen" "tom yafada yana mikewa, abincin Jummai ta kawo wa Mamy, kan table tadora mata kana ta gaishe ta, amsawa Mamy tayi cikin fara'a, tashi Jummai tayi tana wucewa, abincin Mamy tafara ci, "ba laifi ta iya girki, kuma da alama tana da tsafta" "ah dan abinci ai ta iya nima yanzu nagama cin burabusko da miyan taushe, Ahmad yashigo da sallama, amsawa sukai su duka "sannunku da hutawa" "yawwa Ahmad kadawo" Mamy tafada "eh Mamy nadawo" "to sannunka" Hajiya tafada, "akawoma abinci ko se kayi wanka" "ah bara nafara cin abincin dai" "ok bara nasa akawoma" Jummai takira, bata dade ba tazo, "ki kawo mai abinci" da to ta amsa tawuce, kallon Mamy Ahmad yayi yace "Mamy kinyi me aiki ne" "eh mana yau tazo" daga haka be kara magana ba, abincin takawo mai kana tawuce ta tafi, ci yafarayi, sannan ita kuma Mamy ta kammala, 6:00pm yafuto daga theater room, yana dawowa office dinsa yazauna danya huta, wayarsa ce tayi kara alamar shigowar message, dauka yayi yaduba, yana karan tawa kamar haka,
Assalamu alaikum ina magana ne da Ammar, inasan nafada ma wani abu game da yarinyar dazaka aura Ilham, ba yarinyar kirki bace, lala tacciya ce, nasan cewa yar uwarkace, bazaka so laifin taba, amma ina sanar dakai ba yarinyar aure bace, idan kanason sanin komai to kazo 2 star park, yanzu zan sanar dakai komai
yana gama karan tawa yashiga, bibiyar number, amma yajita akashe, tashi yayi yafuta, ko magana beyiwa nurses dinba yafuce, motarsa yashiga, yanufi 2 Star park, bayan ya isa yayi parking, yafuto, number yashiga kira yayi sa'a kuwa tashiga, seda yakira har sau uku ba'a daukaba, seda takatse, aka turo message kamar haka,
kayi hakuri ka koma gida , tanzu na shiga wani uzurin, gobe kadawo karfe 6:00pm, zan sanar dakai komai,
yana gama karantawa yaja tsaki, yayi blocking number, yashiga mota tawuce gida, anayin sallar magariba, Mamy tasa Inna tayi wanka tayi sallah, kana tashiryata, cikin lifaya me adon fulawoyi, tayi kyau sosai se zuba gamshi take, Ammar nadawowa , be tsaya neman Mamy ba yashige part dinsa, 7:40 su Abba da Alhaji Aminu suka iso, Abba ne yakalli Alhaji Aminu yace "wai kuwa kasanar da Mahmud batun auran ka" "ban sanar dashi ba , kaga baya kasar yanacan yana karatunsa ,in ya dawo se tagani," "ok amma dai autarka tasani ko" "ah Yasmeen tasani ai, tana ta doki ma za'a kawo mata aunty" "to masha Allah bara namusu magana se ta futo" "ok kayi maza dan Allah" "dokin me kake yaudai ai a gidan ka zata kwana" murmushi kawai Alhaji Aminu yayi, Abba yashige ciki, yana shiga yanufi bedroom din Mamy dan acan suke shiryawa, yana shiga tace, "abokina fa yana jira" "ai mun gama yanzu zata fita ai" "yawwa to kuyi maza ku fita" tashi sukai suka futa, gurin Hajiya takaita, yayinda Zuhura tana dakin, sallama tayi ma Hajiya, Hajiya tamata fatan zaman lafiya, kwanciya Zuhura tayi saman bed din Hajiya tana kukan zuci, dahaka su Inna suka fuce, har bakin mota Mamy da Abba suka rakata, kana tashiga mota suka tafi, suma su Mamy suka koma ciki, shashshekar kukanta Hajiya taji, "ah ah Zuhura kuka kike"? "Hajiya Inna ta tafi fa" tafada cikin kuka "kiyi hakuri ai zaki dinga zuwa gurinta, kuma gamu zaki zo ai mu dunga hira" dakyar dai tashawo kanta tayi shiru, Mamy ce tashigo dakin, "suntafi" Hajiya tafada tana kallon Mamy "eh Hajiya sun tafi, Zuhura yadai" "kin ganta nan tana rigima wai Inna ta tafi" dafa kafadarta Mamy tayi tana cewa "haba Zuhura ta ai muna tare dake, ga kannenki su Nadra da Muhsin, zasu debe miki kewa idansu Amira sun tafi, kuma duk abunda kike so kisanar damu, ko ni ko Hajiya ko yaynki su Ammar da Ahmad harda Ilham ma ke harda Abba, duk abunda kike so zamuyi miki kinji" daga kai tayi alamar to, "yawwa Zuhura ta" wayar Mamy ce tadau kara, dauka tayi tana fadin "hello my son ya akai" "Mamy nadawo tun dazu ina bukatar abinci" "to ai bakace kadawo ba se yanzu bara nasa Zuhura takawo ma" "ok Mamy" kashe wayar tayi tace "yata ki kaiwa yayanku abinci kinji" "to tace tana mikewa, kitchen tashiga , Jummai ce kitchen din tana shirya abincin dare "sannu da aiki aunty" "yawwa Zuhura sannu" abincin tahada mai kana tahadamai coffee, tanufi part dinshi, tana zuwa tayi knocking, jin shiru yasata tura tashiga, yana zaune kan kujera yana waya, 'au dama yanaji yayi shiru mutuminnan yafiye izza' tafada cikin zuciyarta, karasawa tayi ta ajiye mai kan Centre tables, kallonta yake sosai, kamar bata walwala, kuma idonta ya kumbura alamar tayi kuka, katse wayar yayi yace anjima ze kira, bata kalle shiba tafara zuba mai, kura mata ido yayi yana kallonta, seda tagama zuba mai tasa mai spoon, takoma gefe ta tsaya, saboda tasan idan ta tafi zece waye ze futar da kayan inya gama, hakan yasa ta tsaya batare data kalle shiba, kasa cin abincin yayi,yaji yama futa aransa, besan meyasa, yadamu da yarinyar ba kwana biyu, so yake yamata magana amma bayasan taga kamar yadamu sa ita ne, kuma shi yanaji da izzar shi, kafa tafara dagawa alamar tagaji da tsaiwar, kallonta yayi yace, "zaki iya tafiya in kin gaji" cikin mamaki kuwa yaga takama hanya zata tafi, dasauri yace "sorry sekin dawo namanta ba wanda ze tafi da kayan inna gama" wani takaici ne ya turnuko mata, ba yadda ta iya haka ta dawo, ta tsaya, "Please zauna karki samun ciwon kai" se lokacin ta kalle shi, shima ita take kallo, zama tayi kasan carpet, 'wai Mamy wannan mutumin take cewa nafadawa matsalara' katseta yayi tare da cewa "zoki zuba mun ruwa" mikewa tayi batare da ta amsaba, tazuba mai kana ta tsaya taga ko ya gama tadauka tafuta, shan ruwan yake kamar meshan abu me zafi, ganin haka yasa tadau tire din abincin ta tsaya, ganin haka yasa yace "zaki iya tafiya" kafun yakarasa tafuce, da ido kawai ya bita, futa tayi tanufi kitchen, cin karo tayi da Ahmad, "yawwa my queen kefa nake ta nema" batai magana ba, kallonta yakarayi, ganin fuskarta ba annushuwa yasa yace "my queen meyafaru wanene" kallon tire din hannunta yayi yakara cewa "Ammar ne"? kallonshi tayi kana tawuce, dasauri yasha gabanta yana fadin "Please kifadamun meke damunki bazan iya bacci ba ganinki cikin halin nan" jin haka yasata cewa "bana jin dadi ne yanzuma kwanciya zanje nadanyi" "ok kinsha magani" daga mai kai tayi tana wucewa, gudun kada ya takura mata yasa be kara magana ba, tana kai kayan kitchen tanufi daki, kwanciya tayi saman gado tana fashewa da kuka, Amira ce tashigo, jin kukan yayar tata yasa, tayi saurin matsawa kusa da ita, tana fadin "yaya Zuhura meke damunki kike kuka " saurin goge hawayenta tayi tana kakalo murmushi, "ba kuka nake ba" kallonta Amira kawai tayi tashige toilet
Chapter 32 · 0% Book details