← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 97

Sashe 64

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

sa hannu ka mareta" "Daddy yarinyar nan ta takuramun, wlh Daddy indai naganta se naji raina ya baci, shiyasa nadau Nafeesa ma muka tafi hotel saboda mu huta" "lallai na yadda Ahmad ba kalau kake ba" Mom tafada tana kallonsa "Mom lafiya nake, kawai nidai ta matsa ma matata ne" "Nafeesar kanwar uwarka ce eyee" Mom tafada cikin fada "au yanzu kai ankiraka dan ayi sulhu bazaka kwantar da kai kabada hakuri ba" "ina ze bada hakuri ya saketa kawai, dan ko ta koma bazata ji dadin zama ba" Hajiya tafada "Hajiya kiyi hakuri wlh bamason Ahmad ya rabu da Zuhura yarinya ce me hankali" "Mom nifa ga takardar ta na saketa saki 3" yafada yana zaro takarda daga aljihunsa, salati sukai Mom tace "wlh Alhaji yaro na ba lafiya yake ba, yarinyar can ta gama dashi" Mom tafada tana kuka, takardar ya ajiye musu saman table yafuce, duka da ido suka bishi, shikam Daddy glass din idonsa ya cire yana fadin "inalillahi wa inna ilaihi raji'un" "Mukhtar asaman ticket zanwuce yau" "Hajiya dan Allah kibari se gobe" "eh Hajiya kubari gobe" ganin haka yasa Hajiya tace "dasafe zamu wuce inshallah" Amira na kwance saman bed, ta sato wayar Inna tana game, Mahmud yaturo kofar dakinta, tabayar Inna ce hakan yasa da sauri ta cusa wayar karkashin pillow, tsayawa yayi yana kallonta, itakuma taja uban tsaki tafuto da wayar, kana tace "me ya kawo ka dakina kuma" "nazo ganinki ne" yafada yana zama bakin bed din " wannan wayar wace" "ta aunty ce" "dama naji kamar tana neman phone dinta bara nace mata tana gurinki" yafada yana mikewa, da sauri tamike tana shan gabansa, kallonta yayi yace "menene" "dan Allah karka fadamata zan mayar mata kawai a boye" "ohh batasan kin dauko ba kenan" "eh batasan narika daukan waya" "ok to kizo zan dinga baki tawa kina game din" "dagaske" "eh mana" "am dan Allah zansa number din yan school dinmu dukansu sunada waya kuma suna chat" "da wayata za ai chat din" "dan Allah kaji" yacca ta marairaice ne yasa yayi dariya yace "to shikenan my little sister" murmushi yayi kana yafuce, dad'i ne ya isheta itama tafuce danta mayarwa da Inna wayarta, kwana Zuhura tayi tana kuka, tun Ilham na lalashinta har ta gaji tayi bacci, duk da tasan rabuwa da mijin da kakeso akwai ciwo, amma ita daya mata wulakanci ma ai yakamata ta mance dashi, ita dai Zuhura harga Allah tana son yaya Ahmad, haka ta dinga sallar dare tana rokon Allah yasa hakan ne mafi alheri a tare da ita, safiya nayi Hajiya tace Zuhura tashirya, aikam suna gama breakfast, Hajiya tace Zuhura tazo su wuce, ba yadda su Daddy basuyi ba tabari se yamma, tace masu subari kawai zasu tafi, haka suka wuce, ita dai Zuhura jiki a sanyaye tabi Hajiya suka wuce, ko a cikin jirgi, Zuhura ta kwantar da kanta kafadar Hajiya, tana tunanin ya rayuwar yaya Ahmad dinta zata kasance a hannun Nafeesa, 12:00pm Mamy na zaune a falour tana waya da Ammar, taga Hajiya da Zuhura sun shigo, da sauri tamike tana fadin "Hajiya lafiya kuwa" tafada batare data kashe wayar ba, nufarta Zuhura tayi tafada jikinta, tafashe da kuka, Hajiya kam guri tasamu ta zauna, dagota Mamy tayi daga jikinta, tana fadin "Zuhura meya faru" "Mamy yaya Ahmad ne ya sake ni" daga cikin wayar yajiyo abunda Zuhura tafada, "what saki me kikai mai" "Mamy wlh yaya Ahmad makaryaci ne, ashe ba sona yake ba" zama tayi taan kallon Hajiya tace "Hajiya meya faru ne wai" wayar ta duba taga bata kashe kiranba hakan yasa tace "Ammar kashe waya anjima zamuyi waya" jiki a sanyaye ya katse wayar, "uhmm Khadija yaron nan yabani mamaki" "Hajiya me yayi ne ya akai ya saketa" labarin abunda yafaru Hajiya tabawa Mamy, ita kanta Mamy tayi mamakin abun, "Zuhura Allah yasa haka ne alheri a tare dake, ki manta dashi" "Mamy wlh inason yaya Ahmad" "Zuhura kicire sonsa cikin Zuciyarki, zankira aunty nasanar da ita abunda ya faru" jikin Mamy din ta kwanta tana kuka, Mamy na lallashinta, "Zuhura tashi kije ki wuta" mikewa tayi tanufi dakinta, Jummai ce taga wucewarta hakan yasa tanufi dakinta, "Zuhura ashe kinzo" zama tayi gefen bed tace "aunty Jummai nazo" "Zuhura lafiya kike kuwa" "aunty Jummai kaddara ta hau kaina" "bangane ba" "yaya Ahmad ya sakeni" zama Jummai tayi takamo hannunta tace "ba akanki aka fara saki ba kuma baza a kare a kanki ba, kawai kiyi addu'ar Allah yasa hakan shi yafi alheri, kuma ki dage da addu'a" "tom aunty Jummai nagode" "ki huta bara naje na karasa aiki na" daga haka tafuce, "Hajiya ni banson ma taya zan sanar da mahaifiyar taba" "yazakiyi kuwa haka zaki fadamata" waya Mamy tadauka ta danna kiran Inna, bayan ta dauka suka gaisa, "kaddara ta afka mana auren Zuhura ya mutu" daga ciki wayar Inna tace "subuhannallahi garin yaya" "to kaddara dai" "to Allah yasa hakan shine mafi alheri tare da ita" "ameen dai" "semu dage dayi mata addu'a kawai Allah ya zaba mata abunda yafi alheri" "inshallah" daga haka sukai sallama, "gaskiya mahaifiyar yarinyar nan tana da fahimta" "ai daga gani sunsamu tarbiyyar tun daga tsatstsonsu" "uhmm Allah dai yasa mudace, semu cigaba dayi mata addu'a" LONDON bayan yakashe wayar yashiga tunanin, anya abunda yaji gaskiya ne, indai kuwa gaskiya ne to tabbas burinsa ze cika na soyayyar Zuhura, yanzu yadace ya sanar da Mamy yana sonta, "kai bazeyiwuba bazan taba cewa inasonta ba zan aureta, kimata da izza ta zata zube, yarinyar zata rainani, yazama dole namance da ita kawai a rayuwata" ya fada afili, 'to amma Ammar kada ka zalunci zuciyar ka ta hanyar hanata abunda takeso' zuciyarsa ke masa wannan maganar, "idan kuma ka fada mata zata dau kanta wata, danna ce inasonta, so bazan taba fada ba, sedai idan ita tafada mun" 'to amma taya za ai tace tana sonka hakanma baze yiwuba, sedai kacire ta daga zuciyarka kuma ka hakura da soyayyar ta' "tabbas zan hakura, dan bazan taba cewa ina sonta ba, hakan zesa girma na yazube, tare da izza ta, kuma bazan bari ta rainani ba, tace ninazo nace ina sonta, zan manta dake kawai" haka yadinga maganganu shi kadai
Chapter 64 · 0% Book details