Sashe 68
Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
kuwa" "gaskiya banajin lafiya dan Mommy bata kashe wayar ta" zama yayi kan kujera, kallonshi tayi tace "yaka zauna abincinfa nikakeso naje na girka ma" mikewa yayi yanufi kitchen, itakuma taci gaba da gwada wayar, bayan Ammar yadawo masallaci yawuce part dinsa, ya zauna ya bude laptop dinsa yana dubawa, Mamy ce tashigo da sallama, amsasa yayi yana rufe laptop din, zama tayi saman kujera takalleshi tace "Ammar dama inason muyi wata magana ne" "ok Mamy inajinki" yafada tare da maida hankalinsa kanta, "dama inason kamun wani taimako ne" "taimako kuma Mamy kina matsayin mahaifiyata" "Ammar kasan Ahmad yasaki Zuhura, kuma harga Allah banajin dadin ganinta matsayin bazawara, inka duba yarinya ce karama, a karancin shekarunta be kamata ace tana a matsayin bazawara ba, ina son Zuhura saboda kyawawan halinta, tanada nutsuwa da hankali, mahaifiyar ta ta barta hannuna saboda tasan zan kula da ita, se gashi daga aurenta Ahmad ya watsa mana kasa a ido, duk da munson ba laifin sa bane" "to Mamy ni miye hadina da wannan" "Ammar nasan a baya nace bazan kara cewa ka auri wata ba, hakan yasa yanzu nake neman alfarma bama amatsayin mahaifiyar ka ba, dan Allah Ammar kataimaka kamun wannan alfarmar" "Mamy wacce alfarma" "banson yarinyar nan tafuta daga family dinmu, nafuson ta zauna cikin family dinmu, yarinyar nada tarbiyya da hankali duk namijin daya aureta to tabbas yazabawa yaransa uwa tagari" shidai kallonta kawai yake, hannunsa takama tace "dan Allah Ammar kataimaka kamun alfarmar nan ka auri Zuhura Please" dago kai yayi ya kalleta cike da mamaki dan be taba tunanin alfarmar datake nema kenan ba, shi yama dauka cazatayi yadawo da Ilham, farin ciki ne ya mamaye zuciyarsa, amma sam yaki yanuna ko a fuska, dankar Mamy ta gane dama yanason Zuhura, hakan ne ma yasa yace "amma Mamy ni sam bana ra'ayin auren yarinya musamman ma Zuhura" "karkai abunda baka so danka faranta mun rai, ba dole bane sakamun alfarmar dana nema gurinka ba, zan nema gurin wani" zuciyarsa ce tace 'Ammar karka bari damar nan ta kubce maka, dama kanason yarinyar nan' hakan yasa da sauri yakamo hannun Mamy yana fa in "ah ah Mamy bazeyiwu ba farin cikin ki shine nawa, kuma nasan bazaki zabamun abunda baki da tabbaci akansa ba, dan haka Mamy na amince indai hakan zesaki farin ciki, to na amince" ringumeshi tayi tana fadin "Nagode Ammar Allah yamaka albarka kaima Allah yabaka yaran dazasuyi maka biyyaya kamar yadda kake mana" ameen ya amsa dashi yana jin wani farin ciki aransa burinsa ze cika, yasamu Zuhura matsayin matarsa, Ilham tamance komai aranta, dan harta fara shirye-shiryen biki, dan gobe za'a daura aure, dan haka tanata shirye-shiryen, tanata shan magunguna, ta kudurcewa aranta zata zauna dashi, amatsayin mijinta, ko tasamu aljanna, duk ta rabu da kawayenta tun lokacin da aurenta ya mutu, ta karya layin nata, tayi sabo, bayan sungama abincin dare suka shirya a dining, Ammar Mamy tahadama nashi, tace Zuhura ta mikamai, haka ta karba ba'ason ranta ba, dan ita batason abunda ze hadata da shi, tana zuwa ta tura kofar tashiga, yana zaune kan kujera ya dora kafarsa kan centre table, sallama tayi, acikin zuciyarsa ya amsa, wanda zakai tunanin be amsa bane, karasawa tayi, ta ajiye tire din a kasa, tafara zuba mai, seda tazuba mai, tamika mai, ya karba, tamike tanufi hanyar futa, "ke" juyowa tayi, tana kallonsa, tamkar bashi yayi maganar ba, tace "na'am" "dawo ki zauna inason magana dake" dawowa tayi ta zauna, tana kallonsa fuskar nan a hade, abincin yafaraci, kana yace "me kikayiwa aboki na yasakeki" wani iri taji tambayar tamata, hakan yasa kawai tace "bakomai" girgiza kai kawai yayi yaci gaba da kallonsa yanacin abinci, "kifadamun nasan haka kawai Ahmad baze sake kiba dole da abunda kikaimai" "ni banyi mai komai ba, kawai ranar da Hajiya zataje ne nake cemai Hajiya zatazo, se be kukaniba basake fada mai, shine kawai yafara mun fada yana cewa wai na dameshi na takurawa rayuwarsa, nima nafara mai nace meyasa yakemun haka, kawai seya dau hannu ya mareni, itakuma Hajiya lokacin tashigo, shine ta dinga mai fada, tace tafiya zamuyi, shine muka tafi gidansu, Hajiya ta fafadamasu abunda yafaru, suka kirashi yazo, dayazo sukaimai fada sukace amana sulhu, se yace shi baya bukata, yabani takardar saki, abunda yafaru kenan ina ganin fadan da Hajiya tamai akainane ya fusata shi" shiru yayi yanacin abincinsa yana kallo, tamkar badashi take ba, seda yakusa 15mnt bece komai ba, itakam takaici ne yafara cikata, ganin kamar ma yamanta da ita a gurin, "har yanzu kina sonsa ne"? tambayar ta doke ta, 'idan nace eh, watakila yace ze kira yaya Ahmad yadaidaitamu na koma, kuma idan nakoma, dai wulakantani zasu cigaba dayi shida Nafeesa, kuma Hajiya zataga na watsa mata kasa a ido ganin yadda taketa hakilon sama mata yanci' hakan yasa tace "ah ah" wani murmushi yasaki wanda shikadai yasan yayi dan ko ita datake kallonsa bata gani ba, "ok daukomun ruwa a fridge" mikewa tayi ta dauko mai tazuba mai , bayan yasha ya ajiye cup din kan tire, yace tadauke yagama, dauka tayi tafuce, tana mita kasa kasa "mutum se izza da girman kan tsiya, kafun yayi magana se ya kai awa guda"