← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 97

Sashe 39

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

SOYAYYA DA IZZA
Story and writing by Hadizatu
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan
asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau
page 39
_________________Jummai ce ke wanke-wanken itakuma Zuhura tana mayar dasu mazauninsu, Nadra ce tashigo kitchen din tana fadin "yaya Zuhura kizo inji Mamy" "to kicd ina zuwa" daga haka Nadra tafuce, "aunty Jummai bara naje Mamy tana kirana" fura tayi tanufi falour, bayan taje ta duka gaban Mamy tace "Mamy gani" "dama maamn kice takira waya tace nabaki" tafada tana mikamata wayar, amsa tayi, Mamy tace kije da wayar idan takira kika gama seki kawo mun, amsawa tayi da to tana shigewa, dakinsu tanufa, kafun takarasa kiran Inna yashigo wayar, dasauri ta dauka, tana fadin "hello Inna" "na'am Zuhura kina jina" "eh Inna ina wuni" "lafiya lau ya mutan gidan" "kowa lafiya Inna , yaushe Inna zakizo dan allah" "kinga ba wannan nake magana ba, inason fadamiki yau su Yasmeen da Amira zasu zo, dan Allah ki kula da ita, tana taso ku hadu" "toke Inna yaushe zakizo namatsu naganki" "zanzo se ranar juma'a, kina da matsala ne" "bani da matsala Inna kawai dai inaso naganki ne" daga cikin wayar taji ana fadin "aunty Zuhura ce" "eh Yasmeen itace" "bani ita mugaisa" daga haka Yasmeen takarbi waya tana fadin "hello sister ya kike" "lafiya lau kefa" "ina lafiya sister yaushe zakizo" "se randa Inna tafada, ina Amira" "kinganta nan , Amira ga sister Zuhura" karba Amira tayi tace "yaya Zuhura ya gida" "lafiya lau yan mata, ko nemana bakya yi" "kai yaya Zuhura nida bani da waya" "nima ai bani da ita amma ke ai gata Inna" "to dai zamuzo yau se muga juna" dariya sukai Inna takarbi wayar "to sesunzo jeki mayar mata wayarta" daga haka takashe wayar, falour takoma , "Mamy ga wayar" "yawwa kingama, bara nazo nakira muku me kwalliya kafun Yasmeen takaraso" karbar wayar tayi, ita kuma tajuya tanufi daki
kirane yashigo wayar sa, yayin da yake kwance saman bed, kanshi nakallon silin, wani kiran ne yashigo, seda yaktse na uku yashigo, kana yadau wayar, Nafeesa ce, batare da yayi magana ba yakara a kunnensa, cikin wata muryar ta yaudara tace "beb najika shiru kuma kasan dai bazan iya zama banji dumin jiika ba ko" yadda tayi maganar ne yasa gaba daya jikinsa ya saki, yace "to yanzu me kike so" "kazo yanzu" tafada cikin shagwaba, "ok bara nayi wanka" "no idan kazo sai muyi" "sai nayi wanka" "ok sekazo" daga haka yakashe wayar, yamike ya shiga toilet, bayan yayi wanka yashirya cikin manyan kaya, yafeshe jiki da turare, yafuto, bakowa falour hakan yasa kawai yafuce, batare daya shiga dakin mom ba,
"aunty munshirya" Yasmeen tafada tana zura kai kitchen din, "oh har kun shirya, amma dai kunyi sallah ko" "eh aunty munyi la'sar" Halifa ne yashigo yana fa
in "aunty dan Allah zan bisu" "ah ah Halifa yara basa zuwa se yan mata shiyasa, amma kaima zamuje se gobe kaji" Yasmeen ce takalli Amira tace "lah Amira namanta wayata kan mirror daukomun" amsawa tayi tana tafiya "bara nayiwa driver magana yakaiku" daga haka Inna tafuce zuwa compound din gidan, "Ado dan Allah zaka kai yarannan unguwa kaji" "to Hajiya su futo" komawa tayi tace musu "kuje yana jiranku" "Amira muje" daga haka suka fuce, ita kuma Inna takoma ciki,
"Zuhura kiyi wanka kizo me kwalliyar ta karaso" "tom Mamy" tafada tana shigewa, tana shiga ta fada toilet tayi wanka, bayan tafuto bata sha komai ba, tazura hijabin ta har
asa, tafuto, falourn tafuto tana fadin "Mamy nayi" "ok jeki cikin Waldrop dina zakiga ledar da muka karbo dinki jiya, zakiga wani material purple sa baki kidauka kisa" "tom Mamy" daga haka tashige part din Mamy, Ammar ne yashigo falourn da sallama, amsawa sukai, kallon Mamy yayi yace "Mamy nadawo" "sannu da zuwa to, yau naga kadawo dawuri" "Mamy nagajine shiyasa kawai nadawo" "ok zansa akawo ma abinci" "daga haka ya shige part dinsa" Jummai Mamy takira tasa takaiwa Ammar abinci,
su Yasmeen ne suka shigo, da sallama, amsawa Mamy tayi, suka karaso falourn, durkusawa sukai suka gaida Mamy ta amsa, kana suka koma kan kujera,
kallon kanta ta tsaya tanayi a mudubi, yadda kayan yazauna mata das ajikinta, street gown ce, tabi jikinta shape dinta ya futo, kayan ya dace da fatar ta, seda tagama kallon kanta, kana tafuto, Yasmeen ce tabita da kallo, aranta tana jinjina kyawun Zuhura, dan ko ba a fada mata ba tasan ita ce Zuhuran Mamy ce ta ce "wow yan matana ta futo, ga su Yasmeen nan sunzo tun dazu" zama tayi kusa da Yasmeen tana fa
in "sannu sister ashe kun karaso" "eh wlh sister tun dazu ma fa" "to sannunku, Amira ya kuke" "lafiya lau yaya Zuhura kinyi kyau sosai" "kai Amira " "dagaske fa sister kinyi kyau" "Zuhura tafara muku make up dinnan 5:00pm har tayi fa" "tom Mamy" tashi tayi takoma kan 1sit kujera tazauna me make up din tafara mata"
Make up ake tayiwa Ilham ana tsatso ta, ta dawo kamar aljanna, saboda kwalliyar da akai mata, ba laifi tayi ktau sosai, gown tasa light blue, me net, kawayenta kuma sukasa, material copee suma sunyi kyau, su Ilham se rawar kai take, sukuma kawayenta su Feena sunata zuga ta,
bayan an kammalawa Zuhura make up, tamike , Yasmeen taje aka fara mata, light make up akaiwa Zuhura ba hayaniya, ta kyau sosai, ga daurin data mata ya zauna, Yasmeen tashigayi yiwa, nan danan tagama mata, itama tayi kyau, dayake ita fara ce tas,
Mamy ce takalli Zuhura ta ce "yan mata na biki sa dankunne ba fa" se lokacin takai hannu kunnenta taji, "jeki part din Ammar shinace yasiyo, bansaniba ko yasiyo, kice injini ya baki sarka da dankunnen" amsawa tayi tana fucewa, Amira aka fara ma make up din, itama tayi kyau dan itama tafara zama yan mata, dan har tafara kirgen danki, dayake tafi Zuhura jiki, ita tanada kiba, knocking ta tsaya tanayi, amma taji shiru, hakan yasa ta tura kofar tashiga, bakowa falourn, bakin kofar bedroom din tayi Knocking, yana toilet yana alwalar magariba zeje masallaci, se ya fito ya tsaya gaban mirror yana gyara hannun rigarsa, knocking dinta yaji, yayi zaton Muhsin ne danyace zezi ya tambayeshi dan Allah yadau mota yau dayake duk key din motocin gidan suna gurinsa, banda na Abba da Mamy da Jawad se na Bala driver da shi dama ba a karba saboda kai yara school, izinin shigowa ya bayar, tura kofar tayi tana shiga, kamshinsa dana dakinne ya doki hancinta, tsayawa tayi bakin kofar taki karasowa, "ina yini" tafada a sanyaye , saurin juyowa yayi, idonshi ne kafe kanta, kamar ita kamar ba ita ba yake tunanin, katse mai tunani tayi tace "Mamy ce ta ce wai kabani sarkokin da dankunnen" "ok" drower ya janyo yadauko wasu yan box guda uku, yatako har inda take yamika mata, hannu takai takarba, ta juya zata fuce, jin muryarsa tayi daga sama yace, "kina nufin da make up dinan zaki futa" bata da amsar dazata bashi hakan yasa tayi shiru "ba magana nake miki ba" kada mai kai tayi alamar eh "ok to shiga toilet ki wanke ta yanzu ina jiranki" marairai ce fuska tayi tace "dan Allah kayi hakuri wlh duk anyiwa su Yasmeen, kuma Mamy bazata ji dadi ba idan na wanke" be kulataba ya ratsa ta kusa da ita ya wuce, itama sauri tayi tabi bayansa, tafuce, massalaci yawuce, itakuma ta kaiwa Mamy box din daya bata, "ok zo in samiki" zuwa tai ta zauna kusa da Mamy , karamin box din tabude, dankune ne da sarka siririya, tayi kyau sosai, Mamy ta makala mata, seda tasa mata, kana tamike, bakin mayafinta tadauka wanda Mamy tabata ta yafa, se 7:00pm Bala driver yadauke su ya tafi kaisu event din,
bayan sunje, mutane sun fara taruwa sosai, amma amaryar batazo ba, guri suka nema suka zauna, gurin ya hadu sosai, kana gani kasan da uwar kudi, gurin zaman amaryar se walwali take ga wani cake a kan table din gaban kujerar amaryar, shi kansa cake din wuta yake yana walwali, yan mata ne a gurin kala kala kuma yayan masu kudi, kowanne table maza hudu mata hudu, sukam basu zauna inda maza suke empty suka samu suka zauna su uku, yan matan nata hotuna, dj na ta sakar sauti, amma sedai wakokin turanci yake sawa, sukam su Zuhura idonsu nakan wayar Yasmeen, suna kallon hotunan Yasmeen dasukaje kasar Paris hutu wancan year din, sunata hirar su, Muhsin ne ya hango su yanufo inda suke, seda yakaraso yace "kai yan matan Mamy kun iso kenan, Yasmeen ya gari" "lafiya lau Muhsin ashe kazo" "wlh nazo, yaya Zuhura kunyi kyau fa" "kai Muhsin kyau ai se ku" dariya sukai yace "bara naje kun wadancan na dawo" daga haka ya tafi, sukuma suka cigaba da kallon wayar su,
"Ahmad inasonka sosai wlh bansan abunda ze rabani dakai" tayi maganar lokacin datake kwance saman kirjin shi, tana shafa gefen fuskarsa, "wayace dama zamu rabu muna tare" yafaa yana kara manna ta jikinshi, yana jamusu blanket, yana kara shafa bayanta, tuni itama tafara shafashi rako ina, basa gajiya da junansu, yanzu suka gama amma har feeling dinsu yakara tashi, daganan suka shiga, mantawa da a wacce duniyar suke
Feenat ce takalli Ilham tace "ke dai ki gwada mana kiga kika sani ko yazo din" "uhmm bakusan halin yaya Ammar ba" "kedai bakya san kiranshine" wayarta tadauko ta danna kiransa tana fadin "bara dai kuji da kunnenku" tasa wayar a amsa kuwa yadda zasuji, seda takatse, kana takara kira, seda takusa katse wa yadauka, "hello yaya Ammar" "inajinkj ya akai" "dama haka zance maka, dan Allah inasan kazo muyi hotuna a gurin bridal shower din" "baki da hankali ko, karki kara sani a haukanki" daga haka yakashe wayar, kallonsu tayi tace "yanzu kunji da kunnenku ai" "tab gaskiya dai kina da babban aiki a gabanki" "kunga kubar wannan zancen mu tafi kunga 8:00pm har ta kusa" daga haka suka fara tafiya, ita kuma Ilham ita da kawayenta guda biyu suka shiga cikin mota,
Zuhura da Yasmeen ne suke ta fada, Yasmeen ta dage setayiwa Zuhura hoto, ita kuma taki, dakyar dai ta tsaya ta mata guda biyu, sanarwa aka fara amarya ta iso, hakan yasa kowa ya maida hankali kan gurin shigowa, waka aka samusu wai ta shigo da amarya, ba jimawa kuwa sega su sun shigo, tana tsakiyarsu, sunata rawa har ita, har suka karaso suna rawa, kana tazauna kan kujerar, tuni kowa yafara yadaukanta hoto, Yasmeen ma mikewa tayi, taje tayimata hoto ta dawo, nan kuma aka fara gudanar da komai yadda yakamata, aka fara raba abinci dasu sancks ba abunda babu, se rawar kai take kamar ba amarya ba, bayan sun kammala cin abinci, suka maida hankalinsu kan amarya dasuke ta rawa ita da kawayenta, magana sukaji ana fadin "yan mata ashe kun iso" kallonshi Zuhura tayi tace "au yaya Jawad ashe kaine" "ita kawar taki bata magana ne Zuhura" "kai yaya Jawad tanayi mana" kallon Yasmeen tayi datake ta daddana waya tace "sister wai dama yaya Jawad be sankiba" "rabu dashi sister hakan yakeson fada" "kardai Yasmeen kanwar Mahmud" "ita mana" tafada tana kallonsa "wai kece kika girma haka, ai muna waya da Mahmud din amma be fadamun kin gurmaba" dariya tayi tace "to yaya Jawad kawai kuma seya ce ma kanwarsa ta girma" "bazaki gane dilili ba yanzu dai inason yin magana dake" kallon Zuhura tayi, itama Zuhura ita ta kalla kana tace "bara naje gaba ko nafi ganin amarya da kyau Amira muje" daga haka suka tashi suka basu gurin, kallon Yasmeen yayi yace "kai gaskiya fa kinyi kyau sosai" "Allah yaya Jawad nagode" "tun daga nesa na hangoki naji bazan iya jurewa ba se nazo, ina bukatar zan samu hadin kanki" "name kuma yaya Jawad"? "kinga Yasmeen bazan boye miki ba har ga Allah inasonki, abaya naso Zuhura amma se yaya Ahmad ya rigani, to ina fata anan ba wanda ya rigani" "yaya Jawad ba a riga ka ba, amma inason kabani lokaci nayi tunani kafun" "so nabaki nan da gobe, dan inasonki sosai wlh" dariya tayi tace "alright ba damuwa zanyi tunani" daga haka suka cigaba da hirara sh, se daga baya yace suzo yamai dasu gida, Zuhura tayima magana da Amira, suka taso suka futo, Yasmeen ce ta hau gaba sukuma suka shiga baya, daga haka suka tafi
Chapter 39 · 0% Book details