← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 97

Sashe 46

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ina masu bibiyar books dina
to ina muku albishir da sabon book dina
dana fara rubutawa
me suna YAN BIYU NE ina baku shawara ku bibiye book din nan
dan akwai chakwakwa kiya kala kala zaku nishadantu
zakuma ku wa'azantusosai kudai kawai ku bibiye kafun free page yakare ku biya kan naira
300 kacal ba tsauwalawa
ina alfahari daku
masoyana
kune kwarin gwuiwa ta
i love you so much
my pans
ina godiya da addu'o'in ku
dayacce kuke yabon book dina
duk da shine nafarko, gudiya buhu buhu
nice taku har kullum Hadizatu wacce kukafi sani da (MRS K D) kucika da bibiyata nukuma zanci gaba da nishadantan daku
https://chat.whatsapp.com/FPb99RjggTbAcCFg1aFrVx
page 45
_______________________________________________________________________
_____________________________
_________________Sati guda da kwana daya kenan da bikin Ammar, tun ranar daya kusanci Ilham, be kara bi takan ta ba, hasalima kafun ta tashi yafuce office, idan yadawo kuma tayi bacci, Ilham ta damu rashin ganinsa, dan ita bazata iya jure rashin ganinsa ba, hakan yasa tafara gyara gidan du da bata iya gyaran ba amma tadanyi bakin kokarinta, shikam kullum yana gida, ko bayan ya dawo daga hospital gida yake wucewa, se sun yi dinner tare kana yatafi gidansa, Mamy bata hanashi ba duba da yanzu bata aika musu da abinci, dama na sati ne taci amarci kafun tafara girki, tasan Ilham bata iya komai ba, hakan yasa take kyaleshi yazo suyi breakfast suyi dinner,
soyayyar su Jawad da Yasmeen na kara karfi kullum, dan Jawad har ya yanke shawara ze samu Abba yafada mai, a nema mai auran Yasmeen
Ahmad kam yana nan akan bakanshi na auren Zuhura duk da Mom dinsa ta nuna mai ba ruwanta dashi, dan ko gaishe ta yayi sedai ta amsa mai ciki ciki, hakan na damunsa, amma baze iya hakura da auren Zuhura,
yau asabar , yau su Zuhura da Muhsin ke sauka, tun safe Mamy tasa ake ta shirye shirye, su Inna
kam tun safe suka zo suda su Yasmeen, bayan sun karbo allo sun dawo, aka cigaba da hidimar suka, har Ilham ma Mamy takira tace tazo, ba a son ranta ba haka tazo,
Zuhura ce tasamu Muhsin tare da abokansa daya gayyato, tace "Muhsin Please aran wayarka" "ok" zarota yayi daga aljihu ya mikamata, tana karba tawuce, tafuto, ta nufi garden din dake gidan, seda ta zauna, tashiga sa number Ahmad, tana fara sawa suna yafuto, hakan yasa ta danna kira, ringing biyu yadaga, "hello yaya Ahmad" mikewa yayi daga kwanciyar dayake saman kujera, yace "queen kinance dani" "yaya Ahmad ina yini" "lafiya lau kina lafiya" "lafiya ta kalau" "queen kwana biyu ko nemana bakeyi" "yaya Ahmad bana da lokaci ne, muna exam" "ok kunfara exam ko" "eh mun fara" "amm dai kun kusa gamawa ko" "eh mun kusa befi mu kara one week ba" "kice kin kusa zama matata in dinga ganinki kullum" rufe fuska tayi kamar yana ganinta, "yaya Ahmad bakazo saukar mu ba" "ayyah kiyi hakuri inada pesion ne a asibiti shiyasa amma ina baki hakuri" "to shikenan na hakura" "yawwa nasan zakima mijinki uzuri ai" "bara naje na mayar mai da wayarsa ko" "tun yanzu bangaji da jin muryar ki ba fa" "to ai ze nema" "to shikenan hakan ma na gode ki kulamun dakanki" "tom se anjima" daga haka takashe wayar, bayan ta mayar mai da wayar ta nufi gurin Inna ta zauna, kallonta Inna tayi tace "gobe fa nakeso zamuje gidan yaya asabe" "Inna da gaske" harara Inna ta galla mata tace "ina miki wasa ne" "yawwa Inna dan Allah zamuje gidansu Maryam" "se muje ai" Yasmeen ce tazo tana fadin "amaryar sauka koma ince amarya tund sati nawa ne ya rage, aunty yama kai sati biyu kuwa" duka Zuhura takai mata tana fadin "bansan tsokana" haka suka cigaba da hirarsu,
se 7:00pm Ammar yashigo gida, tarar da mutane yayi, du da ba mutane ne dayawa ba, bayan yashigo, ya tarar dasu a falour a zaune, idansa ne ya sauka kanta, datake ta hira ita dasu Yasmeen, gaishe dasu yayi kana ya wuce part dinsa, yana shiga yanemi kujera ya zauna, yana tunanin meyasa har yanzu soyayyar yarinyar nan taki raguwa daga zuciyarsa ba sema karuwa da tai, duk da addu'ar dayake na Allah yacire mai soyayyar ta a zuciyarsa, yana tsaka da tunanin nan Ilham tashigo, dauke da tire a hannunta, bayan ta ajiye ta zauna kusa dashi, beko kalleta ba, tace "yaya Ammar ina son magana dakai" "ina jinki" "meyasa baka bani kulawa amatsayina na matarka" kallon ta yayi, kana takara cewa "yaushe rabon dana saka a idona kuma wai muna zaune gida daya matsayin mata da miji" "stop Ilham bansan korafi" "eh zakace bakasan korafi mana, saboda kasan ina sonka bazan iya jure rashin ganin kaba" "Please Ilham ki kyaleni kifita" "yaya Ammar idan muka cigaba a haka zan sanar da Mamy komai" "kinga kije zamuyi magana idan nakoma gida" mikewa tayi ta fuce, bayasan abunda ran Mamy ze baci, danya tabbata idan ta fadawa Mamy ranta ze baci,
Bayan sallar isha su Inna suka fara shirin tafiya, bayan sun gama tsaf sukai sallama da Mamy Inna takara tuna mata gobe zasuje gidan yaya Asabe, amsa mata Mamy tayi, suka rakasu har gurin mota, Yasmeen ce tajasu suka tafi,
suna komawa ciki, Zuhura tashige dakinta, wanka tayi tasa kayan bacci, kana tadauko littafanta tafara karatun exam din dazasuyi monday,
sai karfe 10:30pm Ammar yadau Ilham suka wuce gida, koda sukaje gida, tayi tunanin ze sake mata fuska su zauna suyi hira tare, se taga suna zuwa yace, "kije ki kwanta" yana fadin haka yawuce bedroom dinsa ya rufe, takaicine ya ishe ta itama ta wuce ta banko kofar, tana shiga tadau waya ta danna kiran Feenat, tana dagawa ta fashe mata da kuka, tana fadin "Feenat ina cikin matsala" "nasan za a rina" "Feenat yazanyi nasamu drugs ko na rage takaicin danake ji" "so ki futo mana" "kema kinsan sena tambaye shi kuma kona tambaye shi baze barni ba" "tab haka zaki ta zama, to ina ganin kije masa da bukatar ki mana ki rage zafi" "Feenat baya sakar mun fuska fa tun randa yaneme ni sau daya be kara ba, kuma kinsan maza ma ni ba burge ni suke ba" "to kijira za a kawo wasu yara 18 years zakiji dadin harka dasu, se kiga lokacin da baya nan se suzo kiyi abunda zakiyi dasu ki sallame su" "yawwa yaushe ne zasu zo" "gaskiya bansani ba sena tambaya" "ok ki tambaya kimin booking dinsu kar wata ta riga ni" "ok sai na bada drugs din a kawo miki" "ok" daga haka sukai sallama takashe wayar, takwanta, dakyar tasamu bacci yadauke ta,
dawuri ta tashi saboda Inna tagaya mata dawuri zasuje su dawo, hakan yasa tana tashi tayi wanka ta shirya, kana tafuto kitchen dan ta taya su Jummai hada breakfast, haka tasame su kamar kullum ita da aunty A'isha, tagaishe su su duka, kana suka fara aiki, bayan sun kammala suka jera a dining, kana suka sanar da kowa an kammala breakfast,
yana tashi yayi wanka yashirya cikin kananan kaya, yayi kyau matuka, sakkowa kasa yayi, kan dining yaduba be ga breakfast ba, hakan yasa yakoma sama, dakinta yatura, tana kwance kan bed tanata bacci, ba alamar tayi sallar asuba, karasawa yayi yadaki fuskar gadon da karfi, a firgice tamike, tana murza ido, kallonta yayi yace "kinsan zan fita amma banga breakfast dina a kan dining ba" "oh sorry namanta bara nayi maza nayi sallah sena futo na hada ma" "what baki sallah ba duba fa lokaci kiga 10:30am fa" shiru tayi tana kallonsa, juyawa yayi ze fuce tace "yanzu zanzo nama karka futa" beko saurare ta ba yafuce, yana saukowa yafuce, be je gida ba yawuce hospital kawai,
se 12:00pm Inna tazo da driver tadauki Zuhura suka wuce, gidan yaya Asabe suka fara zuwa, sallama suka fara tun daga soron gidan amma ba wanda ya amsa musu, hakan yasa suka karasa taskar gidan, ba kowa, dan Asabe tana daki dan dan Jummai da matarsa sun hanata futowa yanzu kullum tana daki, abinci ma se sun ga damar bata, sallama Inna tasake kwadawa, jin muryar Asabe tayi kamar ta Habiba amma tsoro ya hanata fitowa, hakan yasa tadan bude labulen ta dayagaji da dauda ta leko, karaf kuwa taga Habiba, da sauri ta futo tana ihu tana fadin "Habiba kece ko kuma mafarki nake" matsawa Inna tayi ta dafa ta tace "kwarai yaya nice gama Zuhura nan gasu Amira ga Halifa" "ina kuka shiga haka iye Zuhura kune Amira kin girma" "yaya labarin da tsayi" "naga kunyi kyau haka bara dai na dauko tabarma" daga haka tashiga daki tafuto da tabarma ta baza musu suka zauna, labarin Inna tashiga bawa yaya Asabe tun daga farko har karshe, jinjina kai Asabe tayi, kana tace "kwanaki gwoggwo Larai tazo" labari Asabe tabasu, Inna tace "kai gwaggo Larai bazata canza ba, yanzu tana nan kuwa" "naji labarin bata da lafiya tasamu ciwon mutuwar barin jiki bata iya komai, "yakamata muje mu duba ta

SOYAYYA DA IZZA
Story and writing by Hadizatu
Mrs (KD)
Chapter 46 · 0% Book details