Sashe 65
Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
SOYAYYA DA IZZA
Story and writing by Hadizatu
Mrs (KD)
Ina masu bibiyar books dina
to ina muku albishir da sabon book dina
dana fara rubutawa
me suna YAN BIYU NE ina baku shawara ku bibiye book din nan
dan akwai chakwakwa kiya kala kala zaku nishadantu
zakuma ku wa'azantusosai kudai kawai ku bibiye kafun free page yakare ku biya kan naira
300 kacal ba tsauwalawa
ina alfahari daku
masoyana
kune kwarin gwuiwa ta
i love you so much
my pans
ina godiya da addu'o'in ku
dayacce kuke yabon book dina
duk da shine nafarko, gudiya buhu buhu
nice taku har kullum Hadizatu wacce kukafi sani da (MRS K D) kucika da bibiyata nukuma zanci gaba da nishadantan daku
DOMIN SHIGA GROUP DIN SOYAYYA DA IZZA KA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA
https://chat.whatsapp.com/FPb99RjggTbAcCFg1aFrVx
DUK ME BUKATAR SOYAYYA DA IZZA YA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA
https://whatsapp.com/channel/0029VahPZYb6WaKlZQvivt0J
page 55
_______________________________________________________________________
_____________________________
________________bayan dawowar Zuhura da sati guda, ba laifi ta , ta dawo kamar da, dan yadda su Hajiya da Mamy harma da Abba, suna nuna mata kulawa sosai, kuma suna cigaba da mata addu'a, haka ma Jummai, tana kula da ita, ka Muhsin ga Nadra, suna zama suyi ta hirarsu, tana zuwa gidan Inna, ta wuni, susha hira ita dasu Inna Amira, hakama Yasmeen idan taji Zuhura zataje, itama seta dage tace se taje, haka Jawad ke kyale ta taje,
bangaren Ahmad kuwa, ba acewa komai, dan Nafeesa ta mayar dashi, tamkar ma'aikacin ta, haka yake bin umarninta, ita kuma tana wahalar dashi, ko gidan su ta hanashi zuwa, harta office ma wani zubin ca take ya zauna baze jeba, sedai idan zata hadu da maza a hotel, seta ce yaje, sakary dinsa kuwa, duk ta karbe, da anturo mai, zata cire, ta rike a gurinta, komai na bankinsa yana gurinta, dan haka duk sanda taso take cire kudi cikin account dinsa, kuma baya cewa komai, Mommy dinta kuwa bata kasar ma, tabi wani dadironta sun tafi kasar waje, hakan yasa sedai ta tura mata kudin, ganin lamarin ya
aci yasa Daddy, ya bada kudi ayiwa Ahmad saukar Kur'ani, dakuma addu'ar Allah ya karya sihirin datayi mai, dan yanzu sun tabbatar asiri Nafeesa tayiwa Ahmad, kuma suma sunta addu'a, dan addu'ar iyaye itace gaba da komai,
soyayya tsakanin, Amira da yaya Mahmud tafara kulluwa, kullum Amira ke kaiwa Mahmud abinci, idan yadawo daga office, idan taje seya bata wayarsa tayi ta chat da yan ajinsu, yanacin abincin suna hira, harta kai yanzu dakansa yake kaita school inze tafi office, itama yanzu ta dena mai rashin kunya, dan itama acewarta yana burge ta, yanzu soyayyar su nakara karfi, dan tabbas yanason yarinyar,
yau Friday, suna zaune a falour sunata hira, Zuhura Nadra, da Muhsin, "yaya Zuhura wai yaushe kema zaki fara school ne" "inaso nima Abba nake jira yasamamun admission" "semu dinga tafiya tare, kinga dama yanzu anbani mota ina zuwa school" "ni Allah ya sawwake Muhsin na hau driving dinka ban shirya mutuwa ba" dariya Muhsin yayi kana yace "wlh yaya Zuhura na iya driving sosai" "ai sedai kadau wata ba dai niba" "wlh kam idan kika hau driving dina yadda kike da tsoron nan sekin sume" "ai bama zan hau ba" Hajiya ce tazo falourn ta zauna kan kujera, "me ake tattaunawa ne" "Hajiya wai yaya Zuhura ce wai bazata hau driving dina ba" "ah na goyi da bayanki yaje ya hallakaki" "kai Hajiya kuna gani kamar ban iya ba" "aini ko tukin yayana bana hawa balle naka" "Hajiya ai kuma yaya Ammar shi baya gudu da mota" "duda haka bana hawa nashi balle naka" sallamar Jawad ce takatse su suka amsa su duka, Hajiya ya gaisar ta amsa, kana suma su Zuhura suka gaida shi ya amsa, "ina Mamy" "tana bedroom dinta, daga haka ya shige ciki, "Hajiya wai da yaya Zuhura da yaya Muhsin waye babba" Nadra tayi tambayar cike da kuruciya, "sa annine, ai ko zata girmeshi bazata bashi shekara ba" "kenan yaya Zuhura ce babba" "Zuhura shekararki nawa ne"? "18 nake yanzu" "to ai shekarunku daya ma da Muhsin din" "gaskiya daga yanzu sedai mu ringa girmama juna, bani kadai zandinga kiranki da yaya ba har kema" dariya sukai gaba dayansu
Jawad nashiga ya tadda Mamy tana shirya kaya, zama yayi bakin bed din yana fadin "Mamy ina yini" "lafiya lau, ya jikin Yasmeen din" "ai taji sauki dama laulayin ciki ne" "to Allah ya rabata dashi lafiya" "ameen, munyi waya da yaya Ammar nake cemaj ya shirya yakusa zama uba" "gaskiya kam, naso ace shima" sekuma tayi shiru, "karki damu Mamy shima Allah ze bashi mace ta gari ta haifamai" "ina fatan haka" hannun Mamy Jawad ya rike kana yace "Mamy dama inasan nayimaki wata magana" "ok to inajinka" "Mamy ina neman yadda ki, inason na auri Zuhura" ido takura mai, "Mamy ina tausayin Zuhura, ganin abunda yaya Ahmad yamata, dan Allah Mamy ki yarda na aure ta" "Jawad bawai banason ka aureta bane, ina gudun kada taje amaimaita abun yafaru" "Mamy me kenan" "kaga kana da mata, kuma wannan matar kawaye suke, hakan ze lalata zumuncinsu" "Mamy Yasmeen bata da matsala fa" "uhmmm haka kake gani, bakason mata da kishi ba, sanda zata rufe idonta ta cima Zuhura mutunci bata saniba" "amma Mamy" dakatar dasshi tayi dacewa "Jawad kamanta da wannan tunanin naka sam bazeyiwuba" daga haka bekara cewa komai ba, yatashi yafuce, saboda lokacin sallar magaruba yayi, bayan Jawad yafuta, Mamy tayi shiru tana tunanin maganar Jawad, "nasan me zan yi" daga haka tamike tanufi toilet dantai alwala
"akiramun Ilham inason magana da ita" mikewa Mom tayi tanufi dakin Ilham, samun ta tayi tana ninke hijabi alamar ta idar da salla, "Ilham Daddy dinku na kiraki" "tom Mom ganinan" futa Mom tayi, tace mai tana zuwa, ba jinawa tafuto, zama tayi kasan carpet tana fadin "Daddy gani" "yawwa, wata magana ce nazo da ita bansaniba ko zaki amsheta" "inshallah Daddy" "wani abokina yaganta, ya sameni yake cemun idan ba damuwa yanason ya aureta" "aure kuma Daddy" "kwarai kuwa yanason ya aure ki, besonki ba dayake a anan yake zaune ba, yana Paris tareda iyalansa" "wai Alhaji bello kake nufi" Mom tafada "eh shi nake nufi, yace idan ta yarda, da andaura musu aure zasu wuce can, dama kasuwanci ne yakawo shi nan" "ni a ganina Ilham ki amince kawai, dan shine mafita a gareki" "nima shiyasa nazo na sanar da ita ai, kuma matarsa daya da yaransa biyar" wasu hawaye ne suka zubo mata, azuciyar ta tace 'wai yau nice zan auri sa'an baba na, nida samari ma ke bina da nake wulakantasu, yau gashi na rasa yaya Ammar zan auri sa'an baba na, ya Allah ka kara shiryamu, duniya bata tabbas, inyau kaine gobe waninkane' Daddy ne yakatse mata tunainta da cewa "nafadamai kin taba aure" "shikenan Daddy Allah yasa hakan shine mafi alheri a tare dani" "ameen" suka amsa duka,
bayan ta idar da salla tana lazimi, wayarta tadau ruri, hakan yasa ta duba, ganin Yasmeen ce, yasa tayi murmushi tana dauka, "hello me ciki" "kai sis bansan iskanci wai me ciki" "to da mece" "nifa kunya kike bani ma" "tohh yau Yasmeen da kunya" "me kike nufi da banayi" "ah ah nidai banfada ba" "ke yaushe zakizo aunty" "meya faru" "wani tsegumi zan miki" "name kuma" "na Amira da yaya Mahmud mana" "Amirancy tafada love, yar karama da ita" "kece kike mata kallon karama, karma kibari taji dan yacca takejin kanta" "hhhhhh nawa take toma" "kinga nidai dan Allah yaushe zakije" "bani da rana gaskiya" "to ai shikenan" "ki shafamun baby" "Allah yashiryaki" daga haka sukai sallama, mikewa tayi, kitchen tanufa, Jummai ce girki, "aunty Jummai bara natayaki girkin" "kin futo kenan" "eh me kike dafa mana" "shinkafa da miya ne" aikin tafara tayata,
"yaya Mahmud dan Allah kabani" "nifa yau bazan baki wayata ba" "ohh baka da gaskiya kenan" tafada tana nunashi, "da can bakice bani da gaskiya ba se yau danaca bazan bayarba ko" "eh to in bahaka ba kabani mana" matsawa yayi kusa da ita yace "bazan kara baki wayata ba har senason matsayina a gurinki" "kamarya" "eh mana, naga ke kamar baki fahimci ciwo na ba" "baka da lafiya ne dama" "eh nadade ina jinyar cutar sonki a raina" "dan Allah kifadamun kinasona" sunkuyar dakai tayi" dago fuskar ta yayi yace "dan Allah kifadamun kinadona wlh ina matukar sonki" murmushi tayi kana ta fuce da gudu" shima murmushin yayi yana fadin "kenan tana sona"
dinner suke gaba dayansu, kan dining, Abba ne yakalli Hajiya yace "Hajiya dazu Daddy din Ilham yakirani yace, ranar lahadi za a daura auren Ilham" "to aure zatayi" "eh wani abokinmu ne dake zaune a Paris ti ya zo, shine yaganta, yace yanasonta" "to Allah yabada zaman lafiya" "muma zamuje ne"? Mamy ta tambaya tana kallon Abba, "ah ah, daurin aure kawai za ai su wuce, ba yini zasuyi ba" "to Allah ya sanya alheri yabasu zaman Lafiya" suka amsa da ameen, "Zuhura na nema miki admission fa, amma wanne course kike so" murmushi tayi kana tace "aini Abba ko wanne ma inaso" "kidai zaba dakanki" "am inaganin abar admission dinan ba yanzu ba akwai wani abu danake tunani ne" Mamy tafada, "me kenan" "zan fada muku" "to shikenan to" daga haka suka cigaba da cin abinci