← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 97

Sashe 82

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina masu bibiyar books dina to ina muku albishir da sabon book dina dana fara rubutawa me suna YAN BIYU NE ina baku shawara ku bibiye book din nan dan akwai chakwakwa kiya kala kala zaku nishadantu zakuma ku wa'azantusosai kudai kawai ku bibiye kafun free page yakare ku biya kan naira 300 kacal ba tsauwalawa ina alfahari daku masoyana kune kwarin gwuiwa ta i love you so much my pans ina godiya da addu'o'in ku dayacce kuke yabon book dina duk da shine nafarko, gudiya buhu buhu nice taku har kullum Hadizatu wacce kukafi sani da (MRS K D) kucika da bibiyata nukuma zanci gaba da nishadantan daku DOMIN SHIGA GROUP DIN SOYAYYA DA IZZA KA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA https://chat.whatsapp.com/FPb99RjggTbAcCFg1aFrVx DUK ME BUKATAR SOYAYYA DA IZZA YA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA https://whatsapp.com/channel/0029VahPZYb6WaKlZQvivt0J page 66 ______________________________________________________________________ _____________________________ _________________________________________________Suna futa gurin mota suka nufa, ya bude mota dakansa tashiga kana ya rufe shima ya zaga yashiga, ya tayar da motar suka fuce, suka fuce daga gidan, tafiya suke ba wanda yace kala cikinsu, ita dai Zuhura jin zuciyarta take fess tafuto zata shakata, shikam tunanin Ahmad ne fal a zuciyarsa, yana tunanin taya zesa Ahmad ya manta da Zuhura, gaba daya kyawun garin ya tafi da tunanin Zuhura ko ina an kawatashi da futulu masu matukar haske, kai kyawun kasar baze faduba se kunje kwa gani , tana tsaka da kalle kallenta taji ya ruko hannunta cikin nashi yana murzawa, da sauri tajuyo tana kallonsa, murmushi ya sakar mata, itakuma tabishi da kallon mamaki, irin kamanta tuki kake, kokarin cire hannunta takeyi, ya kalleta yana hade rai ya dawo asalin Ammar dinsa, hakan yasa ta sunkuyar dakanta, shikuma yayi murmushi yacigaba da tukinsa da hannu daya, ita dai kanta ta kawar gefe, wayarsa ce tadau kara hakan yasa ya saki hannunta yana daga wayar, tanajin ya saketa ta matsa can jikin window din motar, "hello doctor Johnson" daga cikin wayar akace "Ammar muna bukatar ka yanzu kazo ankawo pesion ne kuma theater room bazata iya haihuwa ba" "to amma doctor ba wani wanda zeyi aikin seni" "doctor Ammar aikin ba na kowa bane ba wanda ze iya sekai, saboda munyi mata skining munga cibiyar yaron ta nannade wuyan yaron so any mistake zamu iya kashe dan, kaine kadai kwararren likitan daze iya wannan aikin" "to amma..." ya katse maganar lokacin dayaji hannun zuhura kan nashi, ya kalleta tamai alamar yace to, hakan yasa yace "shikenan gani nan zanzo" "ok ka hanzarta dan tana wani hali" daga haka ya kashe wayar, "kiyi hakuri futarmu bazata yiwuba kinsan halin aiki na" yafada batare daya kalleta ba, hannunsa ta rike, tana fadin "haba yaya Ammar ai taimako zakayi kuma ni kaina zanyi alfahari da hakan naga mijina ya taimaki macen datake cikin mawuyacin hali" kallonta yake kamar ba daga bakinta maganar ke futowa ba, ganin ya kureta da ido yasa tace "yaya Ammar kayi sauri mana kaji fa me akace" tafada da an karfi, hakan yasa ya maida hankalinsa gurin tukin ya kara sauri, ba jimawa suka isa hospital din, bayan sunfuto daga cikin motar suka wuce cikin asibitin, duk inda yawuce gaidashi ake cikin girmamawa, be amsa gaisuwar kowa ba, direct tawuce office dinsa, itama tana binsa abaya, bayan yashiga, yafara cire rigarsa ta sam, lokacin wata nurse ta turo kofa, magana yamata tadauko mai kayan daze shiga theater, hakan yasa tanufi wata drower tadauko, tazo tafara taimaka mai yana sawa dayake duk cikin aikin nurses dinne, itakam Zuhura daure fuska tayi ta kauda kai, batasan sanda taji wani kishi ba, haka yakarasa sa sa kayan, ya kai dubansa kanta data hade rai ta kawar da kai gefe, ganin haka yasa ya matsa kusa da ita yana tsugunnawa gabanta, yana juyo da fuskarta tana kallonsa, ganinshi a tsugunne gaban ta yasa tamike dasauri tana dan kallon nurse din dake tsaye tana kallonsu, ganin tamike yasa shima ya mike yana kallonta "lokaci fa na tafiya ya kamata kayi sauri kaje" tafada fuskarta a hade, janyota yayi jikinsa yana matseta a kirjinsa yana fadin "meya faru wifey naga fuskarki ta sauya" ita dai nurse din dake tsaye tana jiransa tasaki baki tana kallonsu a zuciyarta tana fadin 'kai dama doctor yana soyayya shida dariya ma bayi yake ba kullum fuskarsa a daure' "bakomai kaje kayi sauri ka gama mu wuce gida bacci nakeji" tafada tana tureshi daga jikinta, "yallabai lokaci yayi" nurse din tafada tana kallonsa, shi sam yama manta da wata a gurin ya bayar su kadai ne, aikam tuni ya hade fuskarsa yadawo asalin Ammar dinsa ba wasa, yace "ok muje" yafada cike da izza, yawuce gaba tabishi a baya, itakam Zuhura dariya ma yaso yabata, ganin yadda ya sauya Lokaci guda, "Maryam meye laifi dankin auri tsohon mijin Zuhura ai sun rabu, kuma tunda shi da kansa ya furta yace yana sonki ai ba komai" "amma Umma ina ganin kamar abun yaya banbarakwai ace su rabu da Zuhura nina aureshi" "Maryam kinsan halin Zuhura ita farin ciki ma zatayi idan taji zaki auri tsohon mijinta indai tana sonshi sedai idan wani mugun hali ne dashi batason kiyi rayuwa dashi, amma indai ba hakaba ninasan Zuhura bata matsala" "Umma nima nasani kuma nasan farin ciki zatayi, amma inajin lamarin wani iri araina" "kicire komai aranki kiyi addu'a idan alheri Allah ya tabbatar, zan sanar da babanku idan yadawo" "kai Umma da sauri haka mudan jira mana" "jiran me kuma ai gara inzaai zaai idan baza ayi ba to shikenan" wayar dake kan cinyar Maryam ce tadau kara keypad kirar Airtel, dubawa tayi taga Ahmad ke kiranta, kasa daukan wayar tayi tazuba ma wayar ido harta katse wani kiran yakara shigowa, kallonta Umma tayi tace "ah ah kidau wayar mana ko ni ake kira" "ah ah Umma kira nane kuma yaya Ahmad ne" "toba seki dauka ba" "Umma bansan mezan cemai ba idan nadauka" "kicemai kinyi magana da iyayenki sun amince maza ki dauka" wayar tadauka takara a kunnenta, tare dayin sallama, ajiyar zuciya ya sauke yana amsa mata sallmarta tare dacewa "harna tsorata ganin baki dauka ba" "akan me zaka tsorata kuma" "kar inje baki na'am dani ba mana" shiru tayi batace komai ba, yakara cewa "a wanne matsayi nake yanzu" "munyi magana da umma tace zata sanarwa baba" "alhamdulilah nasameki" "tukunna dai" "meya rage kuma, nida zasu yadda ma gobe a daura kawai muwuce abuja tare" "rufamun asiri gaggawar me ake" "gaggawar aurenmu mana" "yaya Ahmad kana ganin auren nan namu baze jawo magana ba" "kamarya magana kuma" "baka ganin za'ayi tacewa na auri tsohon mijin kawata" dariya sosai saboda harga Allah tabashi dariya "haba Maryam tsoho fa kikace ba sabo ba kinga kuwa ina ruwan wani tunda ba kishiya da kishiya kuke ba" "bazan boyema ba inajin wani iri game da lamarin" "dan Allah ki kwantar da hankalinki kimana addu'a,kuma zankira Zuhura nasanar da ita game da auren nasan zataso" "shikenan to, bara naje nayi sallar Isha naji ana kira" "shikenan anjima zan iya kiranki" "ah ah dare yayi lokacin kuma baba yadawo" "shikenan to ki kula seda safe" daga haka sukai sallama, yana kashe wayar yamike ya fuce falour dan yaji muryar Abba, yana futa kuwa ya tarar dashi yadawo, bayan yayi mai sannu da zuwa yasamu guri zauna yana sosa kai alamar yanason yin magana, Hajiya ce ta kalleshi tace "Ahmadu wai kan naka kaikayi yake ne" "kema dai kyafada Hajiya ashe bani kadai nagani ba" Mamy tafada tana dariya "ah ah kunsan dai halinmu mu maza indai kaga haka to akwai magana, Ahmad fadamun ya akayi" "am...dama Abba nasamo matar dazan aura ne" "alhamdulilahi a ina take" suka fada a tare "dama.. Maryam ce kawar Zuhura naga itama tanada hankali kamar Zuhura" "ah indai Maryam ce tayi akwai hankali da nutsuwa" Mommy tafada "koba wannan yarinyar datake zuwa gurin Zuhura ba kafun tayi aure" "ita Hajiya" "ah wannan batada aibu akwai ladabi" "ah da alama yarinyar bata da matsala tunda gashinan kowa yanata yabonta" "eh Abba bata da matsala, mungama magana da ita inason dan Allah aje anemamun aurenta" "shikenan karka damu zamuje zanfadawa Daddy din su Yasmeen ya shirya semuje ka sanar da ita" "tom Abba nagode" "amma naji da in lamarin nan kaima kaga hankalinka ya kwanta" "to Allah dai ya tabbatar mana da alheri" suka amsa da ameen su duka LONDON Zuhura na nan zaune harta fara gyangyadi, dan 10:00pm har tayi, gashi shiru Ammar basu futo daga theater dinba, ita dai nan ta kwantar da kanta kan kujerar tafara bacci, basu futo ba se 10:30pm, yashigo office din, nurses biyu na biye dashi, jin motsi yasa Zuhura tabude idanun ta ta saukesu akansa, dayake kokarin cire hular kansa, ganin haka nurses din suka taimaka mai yacire rigar aikin, toilet yashiga ya wanke hannayensa, duk da yasa handglob amma hakan besa yaki wankewa ba, kallon nurses din yayi yace "shikenan zaku iya tafiya, amma ku tabbata kunbawa matar kulawa ita da abunda ta haifa" "ok sir" suka fada atare kana suka fuce, "masha Allah da alama ansamu nasarar aikin" Zuhura tafada batare data kalleshi ba "eh wifey tasauka lafiya" "to Allah yakara bata lafiya, semu wuce gida ko" kallon ta kawai yake cike da mamaki yaga gaba daya ta sauya, "shikenan muwuce" daga haka yadau rigarsa ta sama, ya rike a hannu kana yadau key din mota suka fuce, tunda suka shiga mota bata kalli side dinsa ba, ta juyar dakanta gefe, koda yamata magana sama sama take amsa mai batare data kalleshiba, mamaki abun yabashi yafara tunanin toko raini ne yafara shiga tsakaninsu, dantaga kwana biyu yana sakar mata fuska, a haka har suka isa gida, yanayin parking tafuto tana wucewa cikin gida, shima futowa yayi, yawuce, bakowa a falourn duk sun kwanta, hakan yasa kai tsaye tawuce bedroom dinsu, tana shiga toilet tawuce ta watsa ruwa kana tayi alwala tafuto, shima kayan jikin nasa ya shiga ragewa, ita dai bata kalleshi ba, tawuce tadau hijabi ta tayar da sallar Isha dabasu samu sun yi ba, tana idarwa tasa kayan bacci doguwar riga mara nauyi me tsantsi kalar purple, kan kujera ta kwanta, ta rufe idanunta, tana hango yadda nurses dinnan ke tayashi wai yana sa kaya da cirewa, wannan ai karuwanci ne' tafada cikin zuciyarta, nidai MRS KD nace "kai
Chapter 82 · 0% Book details