← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 97

Sashe 80

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

ko" yafada yana kallonta, data fara hawaye, murmushi yayi dan yaga bil hakki da gaskiya kuka take, "shikenan ya isa bazan taba ba bara namaki wankan ko" kallonshi tayi irin bangane ba "eh wanka zamuyi yanzu mana" yayi maganar yana cire rigar jikinsa, "wanka tare zamu yi" "tomeye ba mijinki bane ni" yakarashe maganar yana yacire komai na jikinsa, juyawa tayi tana rufe ido da hannayenta, dagata yayi cak yasata cikin bahon wankan, bude ido tayi ganonsa ciki shima yasa tamaida idonta ta rufe, dan yau taga alama yaya Ammar soyake ya kasheta da kunyarsa, a haka dai sukai wankan idonta a rufe, bayan sun futo har la'asar tayi, hakan yasa yabata hijabi sukai salla, bayan sun idar suka shirya, tasa doguwar riga abaya maroon colour se mayafinta, shima yashirya cikin kanan kaya, wayarsa yadauka da makullin mota, kana ya kamo hannunta suka wuce, aunty Aisha na zaune a falour taga sinfuto rike da hannun juna, Zuhura taso ta kwace hannunta kafun su shigo falourn amma ya hanata, "ah ah ina zakuje kuma" murmushi Ammar yayi kana yace "tanason tadan zaga garine" "ah gaskiya ya kamata jikin yayi sauki ko" "eh ai dama ni lafiyata kalau" "to Allah yakaro wata, sekun dawo" daga haka suka wuce yana rike da hannunta, murmushin jin dadi aunty Aisha tabisu dashi, Seda Ahmad yaje har inda Maryam tayimai kwatance kana yayi parking, wayarsa yadauko yashiga kiran number ta, seda takatse yakara kira kana tadauko, yace mata gashi a inda tamasa kwatance, bata jimaba ta futo, aikam ta hango motarsa a kofar gidansu, karasawa tayi, tunda ta tawo yake kallonta, tafiyarta ma kana gani kasan nitsatstsiya ce, "ai nasamu matar aure" Ahmad yafada afili, seda takaraso kusa da motar kana yabude yafuto yana mata murmushin da bata gane manufarsa ba, gaidashi tayi ya amsa, yana kallonta, itakam kanta a kasa, "mushiga mota muyi magana" saurin dagowa tayi tana kallonsa, shima kallonta yake ganin yadda ta kafeshi da ido kamar wanda yace tashiga wuta, "ah ah baya cikin tsari na" tafada kanta a kasa "to shikenan, nasan kinsan komai daya faru tsakanina da Zuhura basena fada maki ba" kaita kada mai almar eh, "daga kan aurenmu har rabuwarmu harzuwa aurenta da Ammar da akayi" "nasani" "yawwa, bazan boye maki ba inason Zuhura fiye da kowacce mace, naso muyi rayuwa da ita, har takai ina bibiyar Ammar daya saketa tadawo gare ni" dagowa tayi ta kalleshi kana tace "saki kuma" "idona ya rufe burina kawai naga Zuhura tadawo gareni, amma yanzu naga hakan bazeyiwuba tunda Zuhura da bakinta tace mun ita matar aure ce" "ni ina ganin ai gaskiya tafada maka ita matar aure ce bekamata kamatsa seta tafuto daga gidanta tadawo naka ba" murmushi yayi jin yadda tayi magana cikin hikima "gaskiya kam nima yanzu ai na hakura da ita duk son danake mata zan barta tayi zaman aure" "Zuhura ma tanasonka ba kadanba, amma haka Allah yatsara ba dakai zatayi rayuwa ba" "gaskiya kam, haka Allah yatsara, Maryam zaki aure ni" taji maganar a sama, ta dago tana kallonsa "nayi tunanin bazan taba samun kamun Zuhura ba, amma yanzu nasamu halayenku yazo daya da Zuhura dan Allah kitaimaka ki aure ni" gabadaya takasa cewa komai dan batayi tunanin maganar daze mata kenan ba, "dan Allah karkicemun ah ah Maryam kibari kawai naturo iyayena ayi magana muyi aure kawai" "to..to ai..sena fadawa Umma na" "kin tabbata bazaki ce ah ah ba" kadamai kai kawai tayi alamar eh, "Nagode Maryam Allah ya tabbatar mana da alheri" "bara natafi gida" "ok to zankiraki an jima" bata bashi amsa ba tajuya tawuce, seda tashige gida kana ya shige mota yaja yawuce,
Chapter 80 · 0% Book details