← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 97

Sashe 25

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

SOYAYYA DA IZZA
Story and writing by Hadizatu
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan
asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau
page 25
__________________Su Inna ne suke ta shirya abincin dare, ita kam Zuhura tana can tana bacci, karfe 6:30 da bakon abba yazo, dukansu suna falour , gaggaisawa suke yi, Abba nata tsokanarsa baya zuwa amma dan Hajiya ta dawo yazo, hajiya tace "kasamuma yazo din danni ko usman" wlh kuwa Hajiya" Aminu wai haryanzu bakai aureba ne" Hajiya haryanzu dai banyiba " Aminu badai kai niyyar yi ba ace tunda Hafsa ta rasu ka kasayin aure" Hajiya zanyine" za kai to se yaushe" dariya yayi yace hajiya nan kusa" Abba ne yacemai su wuce masallaci anyi magaruba, daga haka suka fuce gaba dayansu harsu Ahmad, dasu Ammar dayake kowa yana gida, itama Hajiya dakinta tanufa dantai sallah, bayan sunyi sallah sun dawo ne, Mamy tace musu , su taso anshirya abinci, tashi sukai suka nufi dining, kitchen Mamy tawue danta debo sauran kayan, Inna tagama hadasu , shigowatai tana cewa, Inna Zuhura tayani diban kayannan mukaisu sunyimin yawa" diban kayan sukai, a dining suka samesu a zaune, gaishe da kowa Inna tayi tayiwa Hajiya sannu da zuwa, amsawa tayi tana cewa " mahaifiyar Zuhura ko" eh" Allah sarki munta ganin girke- girke sannu da kokari" murmushi tayi kawai ta tashi tashige ciki, shikam alhaji Aminu ya tsura mata ido kamar me, be dauke idonsa ba harseda takulemai, saving dinsu Mamy tayi, sannan itama ta nemi kujara ta zauna, se 7:30 ta tashi , ita kanta tayi mamkin baccin datai , toilet tashiga tai wanka tayi alwala, kana tafuto tayi sallah, bayan ta idar da Sallah ne Inna tashigo, "kardai se yanzu kika tashi" wlh Inna nima bansan anyi magaruba ba" toni banasan baccin la'asar dinan karki karayi" tom" ga abinci can kije ki zuba" tom" daga haka tamike , abincin tazuba tafara ci, bayan sun kammala cin abinci suka taba hira kadan kana yace ze wuce gida, sallama sukai da Hajiya da Mamy, kana Abba yatafi rakashi, parking space yarakashi, kallon Abba yayi yace, " nikam usman naga wata agidanka" wa kenan" wacce suka zo da uwargida kawo abinci" oho ai a gidan take a zaune" to nifa gaskiya tayimun na yaba da hankalinta" to ai ba komai zan sa matar gidan tamata magana" yawwa dan Allah kataimakamun ni ko gobema ashirye nake" dariya Abba yayi sosai yace"kai mutumina kaida ake tacewa kayi aure kaki" bansamu wacce tayimun ba se yanzu" yo ka kwantar da hankalinka kamar kasameta" Allah abokina "kwarai kuwa"to nagode" daga haka sukai musabaha , motarsa yashiga megadi yabude mai gate yafuta, seda yafuta Sannan Abba yadawo, su Hajiya ya tarar a falour shima zama yayi "kallonshi Hajiya tayi tace "Usman yadai naga kadawo cikin farin ciki" Hajiya abun farin ciki ne yasaamemu" to me kenan" Mamy tafada tana gyara zama " Alhaji Aminu ne yaga mahaifiyar Zuhura yanaso" me alhamdulillah" Mamy tafada tana washe baki "kai mu gode Allah" wlh kuwa Hajiya naji dadin maganar nan" yanzu ke yakamata kisameta kuyi magana" hakane yanzu makuwa" daga haka tamike tanufi dakin su Inna, tana shiga tagansu sunata hira sukuma su Amira da Halifa sunata bacci, sallama tayi, suka amsa su duka "ah hira ake tasha ne"dariya sukai yi, Mamy ce tace " Zuhura kikaima Ammar coffee" tom" tafada kawai, Mamy tayi hakanne dan Zuhura ta futa tayi magana da Inna, Mamy ce takalli Inna tace " Inna Zuhura inason nayi magana dake" to Hajiya inajinki" abokin Abba ne dayazo yau yagankin ya yaba da hankalinki , to yace wa da Abba mumuki magana, muji taba kinki" Hajiya amma kinga ai inada ya'ya kuma ina zankaisu inaganin be kamata nayi aureba" kafadarta Mamy ta dafa tace " wannan duk ba hujja bane, ya'ya kuma ko mu zamu rike su" hakane Hajiya to indai kun amince nima na amince" yawwa haka yakamata kice Allah yatabbatat da alkairi" ammeen" daga haka Mamy ta tashi tafuta, bayan tahada coffee din tawuce part dinshi, tana shiga taganshi a falour a zaune, sallama tayi cikin nutsuwa, dagowa yayi ya kalleta, karasawa tayi inda yake, tsugunnwa tayi tace "ga coffee din" kallonta yayi cikin mamaki yace "nace akawomun coffee ne" Mamy ce tacemun nakwoma coffee" ok to bani" mikami tayi yakarba , mikewa tayi zata tafi yace "dawo nan" dawo wa tayi yace " me yasa dakin kawomun kike son tafiya ne, kuma inna gama waye ze futa da cup din" kayi hakuri" daga haka bata kara cewa komai ba tanemi kasan carpet tazauna " ya school din naki"? "ai se gobe zan fara zuwa" to Allah yabada sa'a "ameen" dahaka ba wanda yakara cewa komai, gabadaya tagaji bacci ma takeji ga ba damar yimai magana, tana wannan tunanin har bacci barawo yasaceta, shikuma shan coffee dinsa yake hankali kwance, seda yagama tas yajuya gareta, bacci take hankalinta kwance, tanamai kyau sosai musamman idan tana bacci, saukowa yayi daga kan kujerar da yake, yamatsa kuda ita, fuskarta yataba alamar ta tashi, ko motsi batai ba balle ma ta tashi, hancinta yakama yaja, aiko dasauri ta tashi tasa kuka, hannunsa yasa yatoshe bakinta, kokarin cire hannunsa take, amma takasa, alamar tayi shiru yamata da dan yatsansa, shiru tayi takama kanta da yanzu tagane inda take, " ke daga cewa kijira shine zakimin bacci" bansan nayiba" oya tashi ki tafi" daga haka ta tashi tafuce, tana futowa tawuce dakinsu tana tangadi, tana shiga tazube kan bed se bacci
"biki fadamun ya kukai da mahaifiyar yarinyar nan ba" kar ka damu amince" dagaske" kwari makuwa" aikam safiya nayi zan kirashi na sanar dashi dama yanata kirana" aikuwa dai kafada mai ta amince koyaushe ma za a iya daurawa" ai bazama mubari satinnan yacinye ba a daura aurenan ba" gaskiya dai haka yakamata" ga kuma hidimar bikin Ammar sati
aya ne ya rage mana" to ai ba wani abu za aiba komai akwai shi gidansa yananan a ajiye" ai wai maganar lefe " kinga ko a rana dayane zaku iya siyan jayan lefen" to shikenan Allah dai yakaimu da rai da lafiya"ameen"
Chapter 25 · 0% Book details