← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 97

Sashe 72

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

yace ina Zuhura to bayasan a rainashi ace yadamu da yarinyar, abincin yafara ci, sukuma su Mamy da Hajiya da Muhsin, suna kallon wani series, wayarta Mamy ta duba taga 7:30pm tayi, hakan yasa tace "Muhsin tashi kaje kadauko su Zuhura dare nayi" "Mamy wlh motata tana gurin masu gyara, dan yau se abikinane yakawoni gida" "wato ka lalata motar ko" Ammar yafada, batare daya kalli Muhsin ba "yaya wlh ba abunda namata, kawai jinai tana daukan zafi" "to kiyiwa Bala driver mana magana" Hajiya tafada, "na aikeshi gidan Hajiya Turai" "Ammar arama Muhsin motarka yadaukosu" "Mamy nifa motata bana bawa kowa, ballantana nabawa Muhsin shida ko kwarewa baiyiba" "bara nakirata kawai nace sufuta titi su samu dan sahu su hau" kamar bazeyi magana ba can kuma yace "no Mamy kinsan dare yayi zanje na daukosu kawai" "ok to kaje kadukosu" seda yagama cin abincin, yadan zauna kamarma yamanta, kana yamike yafuce, suna zaune falour, "Zuhura dare fa nayi bazaki kira driver yazo yadukeku ba" "kai aunty zezo fa" me gadin su ne yashigo da sallama, "shigo mana malam Musa" Inna tafada shigowa yayi ya tsungunna yana fadin "Hajiya kinyi bako a waje" "bako kuma" "eh" "ok ta cenamasa ya shigo" daga haka yamike yafuce, "to aunty wanne bako kuma kikayi" "toni taya za"ayi nasani" suna tsaka da maganar sukaji sallamar Ammar, a razane Zuhura tajuya tana kallonsa, cikin falourn ya shiga ya zaune saman carpet kana yagaida Inna, ta amsa tana fadin "haba Ammar kidanku ne fa seka nemi izinin shigowa" saman kujerar yakoma ya zauna, kana yayi murnushi, first time kenan da Zuhura taga murmushinsa, gaida shi Yasmeen da Amira sukai, da Halifa ma, ya amsa yanama Halifa alamar yazo, hakan yasa Halifa yaje gurinsa, "abokin ya kake yakuma school" "lafiya kau kullum ina zuwa ai" "Masha Allah haka akeso ai" "Mamy tacemun gobe zaku wuce ko" "eh gobe inshallah zamu wuce saboda aiki na shiyasa zan koma dawuri" "to masha Allah Allah dai yabaku zaman lafiya ya hada kanku" cikin zuciyarsa yace 'ameen' kana yamike yace "bara muwuce" "tom Allah yatsare" daga haka yafuce, "Zuhura tashi ki kimtsa yana jiranku" "tom aunty" "kin wani zauna kamar wani dutse daga kinga yaya Ammar" Yasmeen tafada tana dariya, mikewa Zuhura tayi cike da mamakin taya akai Ammar yazo daukansu, haka dai ta shirya, takama hannun Nadra, leda Inna tamikamata, tace "kidinga sha bashi da wani daci da zuma akai hadin" "tom" tafada hawaye suka ciko idanunta "meye hakan to" "aunty yanzu shikenan bazan dinga ganinku ba" "kai Zuhura ga waya zamu dingayin waya ai" rungume Inna tayi tana kuka "kinga kiyi hakuri, kiyi shiru ai zamu dingayin waya" Yasmeen ta rungume tace "Yasmeen se Allah ya sake hadamu" "kai Zuhura sekace wacce zaki mutu" Amira ce tanufeta ta rungumeta tace "yaya Zuhura ina maki fatan alheri" "nagode kanwata" ganin haka yasa Halifa yace "yaya Zuhura wai ina zakije" "zatayi tafiya ne zataje London amma bazata jimaba" kada kai kawai yayi alamar ya gamsu, "Zuhura kutafi yana jiranku" hannun Nadra takama suka fuce, yana mota a zaune yana danne dannensa a wayarsa, gidan gaba suka fude suka shiga, su duka, kamar besan sun shigo ba yaci gaba da danna wayarsa, ita dai Zuhura tamaida kanta gefe tana kallon taga, dakanshi dayagama danne dannensa yayiwa motar key, tunda suka fara tafiya ba wanda yace kala se Nadra datake ta game a wayar Zuhura, dan haka karar sound game din kawai kakeji, "wa kika tambaya dazaki futa" taji maganar tasa sama taka, kallonshi tayi taga driving dinsa ma yake, hakan yasa tace "Mamy" tafada a takaice kamar bazece komai ba, se daga baya yace "Mamy ce mijinki kenan" kadamai kai tayi alamar ah ah, "kinsan haka amma kika futa batare da izinina ba" ita mamaki ma yabata, tome yake nufi, kishi yake kome, daga haka ba wanda yakara cewa komai, wayar Zuhura ce tadau ara, hakan yasa takarba daga hannun Nadra, ganin Maryam ce yasa tadauka tana fadin "hello Maryam ya kikaje gida" "lafiya lau umma tanata godiya data ganni da kaya niki niki" "oh Allah sarki umma" "yanzu goben zaku tafi" "eh gobe zamu tafi, zanyi kewarku sosai" "nima wlh zanyi kewarki kawata, dannasan kafun kizo inaga sekin kai nan da shekara 2" Ammar najinsu saboda wayar nada speaker sosai hakan yasa yanajin maganar Maryam din "haba dai ko shekara daya bazanyi ba ma" "kinjiki shi dawo dake zeyi lallaima" "uhmmm kinga nifa bazan iya zama har 2 years ba ga ba wanda nasani" dariya Maryam tayi kana tace "kiyi kokari kisamu ciki ki haifa mana baby kinga semuzo London suna" Maryam takarashe tana dariya, kallon Ammar Zuhura tayi dan tasan yaji me Maryam tace, gani tayi hankalinsa nakan driving dinsa kamar ma beji me tace ba, nan kuwa yanajin su, har seda yayi murmushi cikin zuciyarsa, "ke Maryam se anjima" daga haka takatse wayar, "waya baki wannan wayar" yafada yana shigar da motarsa cikin gida, "yaya Ahmad ne yasiya mun lokacin dazamuyi aure" wani malulun ba in ciki ne ya tokare mai a makoshinsa, hakan yasa yace "ok muga wayar" bata kawo komai ba tamikamai, karba yayi yabude wani guri a gaban motarsa yasa wayar, kallonshi tayi ya kauda kai, parking yayi , ta bude kofar Nadra tafara futa, kallonshi tayi tace "wayar tawa" "kin rabu da ita ai" "saboda me" "saboda haka nayi niyya" takaici ne yacikata tafuce afusace, shima yafuce yabi bayanta, tana shiga bakowa a falourn se Muhsin hakan yasa tace "Muhsin nadawo" "sannu ku da zuwa" daga haka tashige, Nadra ma wucewa tayi, Ammar ne yashigo shima, "yaya Ammar sannu da zuwa" "yawwa" daga haka yashige part dinsa, dakin Mamy ta nufa, ta sanar da ita ta dawo kana tawuce dakinta
Chapter 72 · 0% Book details