← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 97

Sashe 75

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

SOYAYYA DA IZZA
Story and writing by Hadizatu
Mrs (KD)

Ina masu bibiyar books dina
to ina muku albishir da sabon book dina
dana fara rubutawa
me suna YAN BIYU NE ina baku shawara ku bibiye book din nan
dan akwai chakwakwa kiya kala kala zaku nishadantu
zakuma ku wa'azantusosai kudai kawai ku bibiye kafun free page yakare ku biya kan naira
300 kacal ba tsauwalawa
ina alfahari daku
masoyana
kune kwarin gwuiwa ta
i love you so much
my pans
ina godiya da addu'o'in ku
dayacce kuke yabon book dina
duk da shine nafarko, gudiya buhu buhu
nice taku har kullum Hadizatu wacce kukafi sani da (MRS K D) kucika da bibiyata nukuma zanci gaba da nishadantan daku
DOMIN SHIGA GROUP DIN SOYAYYA DA IZZA KA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA
https://chat.whatsapp.com/FPb99RjggTbAcCFg1aFrVx
DUK ME BUKATAR SOYAYYA DA IZZA YA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA
https://whatsapp.com/channel/0029VahPZYb6WaKlZQvivt0J
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_

alaminmu
ancinmu
page 61
_______________________________________________________________________
_____________________________
________________ futowa tayi shabe shabe da hawaye, aunty Aisha na ganinta ta mike ta nufeta tana tambayarta "Zuhura meye yafaru me Ammar din yamiki" cikin shashshenar kuka tace "aunty Aisha dagaske yaya Ammar yanadona naji yafada da bakinsa" "dama aina fada maki yana sonki" "amma aunty Aisha baya nunamun ko kadan" "ai kece bakiso ya nunamiki ba Zuhura" "aunty Aisha yaya Ahmad yadawo cikin hayyacinsa Allah inason yaya Ahmad" "subuhannallahi aikam karki bari Ammar yaji" "wlh aunty Aisha dagaske inason yaya Ahmad" saurin rufe mata baki aunty Aisha tayi tana fadin "haba Zuhura da aurenki, kike cewa kinason wani, bakya tunanin ya Ammar zeji idan yaji abunda kike fadi, karna sake ji, ki mance da wani Ahmad kiyi kokari ki janyo mijinki ajiki ki nunamai so da kulawa tunda shima yana sonki kuma kinji da kunnenki" "to" tafada kawai dan batasan me zatace ba, "ki kula kisa ido akan mijinki ki janyo hankalinsa zuwa gareki kusa damar nunawa juna soyayya" "tayaya" "ta hanayar kissar mu mana ta mata zaki janyo hankalinsa, karki damu zankoyar dake dabarun kama miji ba boka ba malam" kai kawai Zuhura ta kada mata, alamar to, "ki goge fuskarki ki koma gurin mijinki ki sanar dashi yazo yaci abinci" to tafada tana share hawayenta, kana tawuce, yana zaune dafe dakai yaji tabudo kofa, be dago ba, zama tayi daga gefe, kana tace "sannu da zuwa" dagowa yayi yana kallonta batare daya amsa mata ba, tsoro taji ganin yadda yake kallonta dan tasan ko kallo bata ishe shi ba, "Ahmad yadawo hayyacinsa" yafada yana kallonta dan yanason yaga mood din dazata shiga, itakam batare da nuna damuwar taba tace "masha Allah, Allah yakara tsareshi" tafada a halin ko in kula, tayi ne saboda karta nuna farin ciki ta yaji haushi, shiyasa tabarshi cikin zuciyar ta, wani dad'i yaji ganin ta nuna bata damu ba, 'hakan na nufin kenan batason Ahmad' yafada cikin zuciyarsa, "akawo ma abinci ko kuma zaka futo kaci" "no kawomun kawai" mikewa tayi tafuce, shikuma yabita da kallo, kamar yace mata kayan datasa yayi mata kyau, amma yafi karfin ya yabeta, yanaji da izzar sa, tana futa tashiga kitchen tahada mai abincin kana tadawo tawuce, bayan tashiga ta ajiye mai abincin kan centre table, kana takoma saman kujera ta zauna, "ga abincin" mikewa yayi yanufi kujera yana janyo centre table din gabansa, yafara ci, kallonsa take tanason tamai maganar wayarta, dan tanason takira yan uwanta, "yaya Ammar dan Allah kabani wayata" seda yadan jima kana yace "kimance da wayar nan" "yaya Ammar dan Allah inason nakira su Mamy ne dasu anty mu gaisa" "zoki karbi wayata ki kirasu" aikam jin haka tamike da sauri tana nufarsa, ta zauna kusa dashi har jikinsa na gugan na juna, hannu yasa cikin aljihu ya dauko wayar yamika mata, karba tayi da sauri, ganin da password akai yasa tace "password din" "345678" yafada, sawa tayi wayar ta bude, number Mamy tafara nema, aikam tana gani ta danna dialing number, bugu biyu Mamy tadauka, tana fadin "hello my son" "Mamy nice" "Zuhura lafiya dai ko" "kai Mamy lafiya lau nake kuna lafiya" "lafiya lau Zuhura kin tabbata dai babu wata matsala ko dan nasan halin Ammar" "Mamy yaya Ammar bashida matsala muna zaune lafiya" saurin kallonta yayi itakam ta dauke kai, "to Masha Allah haka nakeson ji" "Mammy ina Hajiya" "Hajiya tana nan lafiya" "Mammy kice ina gaidata da Abba ma harda Nadra da Muhsin" "to shikenan duk zasuji ki gaida Ammar din" daga haka sukai sallama, kallonta yayi yace "wato ke kin gaisa da ita niko ohoo ko" marairaice fuska tayi tace "ohhh namanta dakai yi hakuri" "dama nican ai ba tunawa kikeyi dani ba" bata kulashi ba taci gaba da saka number Inna, kiranta tashiga yi, aikam ba jimawa ta dauka "aunty ina yini Zuhura ce" "Zuhura ya gida ya kike kina lafiya dai ko" "aunty ina nan lafiya inasu Amira da Halifa" "duk sunanan lafiya sunata kewarki" "wlh nima aunty ina kewarku sosai, ina Yasmeen me ciki" tafada tana dariya "Yasmeen tana nan jiyama tazo" "aunty kisa Amira ta turo mun number ta ta wannan number" "ok to zan fada mata" daga haka sukai sallama "zaki bani wayata ko akwai sauran wadanda zaki kira" mikewa tayi dan shima a tsaye yake, harya kammala cin abincin yayi abunda zeyi, wayar tamika mai tana fadin "mutane ma dayawa, dan dai bani da number su akai nane shi yasa" karbar wayarsa yayi, "lah na manta inason nakira yaya Ahmad" hade rai yayi yace "bada wayata ba" "saboda me ai abokinka ne" tana sane tafadi hakan dan taga ya zeyi "eh tun kafun a haifeki muke tare ai" wata dariya taji tazo mata amma ta kimtse tace "to shiyasa nace kabani ai nakirashi kokuma nakira aunty Ilham" matsawa kusa da ita yayi sosai yana kallonta yace "meke damunki kinsan banason surutu ko" jitai gabadaya yamata kwarjini hakan yasa tace "sorry na dena" dariya tabashi yayi dan murmusa kadan kana yabude kofa yafuce, tsayawa tayi tana kallonsa, a zuciyarta tana jinjina hali irin na Ammar yanasonta amma izzarsa tahanashi ya nuna mata
yana futa salla yayi, itakuma jitai jikinta ba dadi hakan yasa tasauya kayanta zuwa na bacci, dama tana perieod ba salla take ba, tana gama shiryawa, tahau saman bed din ta kwanta taja blanket, tasan ba anan take kwana ba, amma ta kwanta dan tasan ba lallai yashigo yanzu, aunty Aisha na falour tana jiranta tafuto suyi hira, tajita shiru hakan yasa tace ma da Ammar yaje yaduba ta, batayi dinner ba, mikewa Ammar yayi yanufi hanyar bedroom dinsu, yana shiga ya ganta kwance saman bed din, karasawa yayi, ya yaye blanket din, jin sanyin datakeji yakaru yasa tabude idon ta daduka kankance sukayi ja, tana kallonsa, a rikice yakai hannu goshinta yana fadin "meke damunki haka, jikinki akwai zazzabi bara naduba ki" bata iya cewa komai ba, yanufi drower yadauko first aid box, yadawo inda take, yabude akwatin yana dauko allura, zaro ido tayi tana kallonsa, ganin yana hada ta, yasa tayi saurin kama hannunsa tana fadin "Please yaya Ammar karkayimun allura banaso" tafada hawaye na bin kuncinta, ganin ta tsorata yasa yace "ba zafi ki rufe idanunki bazakiji zafi ba" "kawai kabani magani Allah zansha" "ah ah gara allura kawai nafada maki bazakiji zafi ba oya taso" yafada yana dagota, hawaye take tana girgiza masa kai, bata tsammata ba taji ya rungumeta a kirjinsa, hakan yasa tayi shiru ta lafe a kirjinsa tana shakar kamshinsa, hakan yasa yasamu damar yimata allurar, ji yayi yakasa janyeta daga kirjinsa, a haka harsukai minti 30, seda yaji wayarsa na kara, kana ya dagota, yaga ita bacci ma takeyi, hakan yasa ya kwantar da ita a hankali, ya jamata blanket ya rufe ta, kana yamike, wayarsa yaduba, yaga Jawad ya kirashi, be bi kiranba, yawuce toilet yayo wanka, kana yafuto yasa kayan bacci, kan bed din ya zauna, yana kallon fuskarta, yanajin shauki na fizgarsa, system dinsa ya janyo danya gudanar da wani aiki,
a falour kuwa aunty Aisha data gaji da jira, ta wuce dakinta, dan mijinta yadawo, yaran ma tace suje su kwanta
bangaren Ahmad kuwa duk ya daga hankalinsa, jin Ammar yace baze saki Zuhura ba, kuma wai yanasonta, hakan yasa yadinga neman su Muhsin su Jawad dasu bashi number Zuhura dan yasan Ammar sauya mata layi yayi, sukam sukace basu dahi, hakan yasa yayi tunanin yaje gurin Yasmeen dan yasan itace kawai zata samu number Zuhura,
Daddy ne ya kalli Ahmad yace "Ahmad ka hakura da Zuhura haka Allah ya kaddara maka" "Daddy bazan iya ba inasonta wlh ba wacce zata iya mayemun gurbin ta" "aikam yazama dole ka hakura da ita tunda yanzu matar wani ce" Mommy tafada "Daddy ka taimaka kayiwa Ammar magana nasan kai zeji maganarka ka rokeshi ya saki Zuhura tadawo gareni" "bazan tabayin haka ba, kuma koda Ammar ya amince ze saki Zuhura ni bazan bada goyon bayan hakan ba, baze yiwu ku mayar da yar mutane kamar wata akuya waccan yasaka wanccan ya aura" "nafada mai ai taya za ai yace wai Ammar yasaki Zuhura hauka ma kenan, kawai kaje ka nemi wata ka aura shine kawai" "Mom bazan taba samun kamar Zuhura ba Zuhura ta dabance" "to ai seka bada himma" daga haka Mom tamike tana shigewa, shima Daddy mikewa yayi yanufi part dinsa, dafe kai Ahmad yayi yana fadin "dole ne kidawo gareni Zuhura kodan na nunamaki soyayyar da ban nunamaki a bayaba" shi kadai yadinga surutai, nikaina MRS KD canai bara nagudu kada yafara kai duka
seda yagama aikinsa tsaf, kana yakwanta a gefenta, shima yaja blanket din ya rufa, hannunsa yakai gishinta, yaji zazza
in ya sauka, harta fara gumi, hakan yasa ya yaye mata blanket data rufa, idonsa ne yayi tozali da rigar bacci ta data yaye takoma cikinta, ga rigar ta amshi fatar ta, kallonta kawai yake yana dan cije libs dinsa, yana tunanin dashi kadai yasan na maye, ganin harkalarsa nasan mikewa yasa yayi saurin saita kansa, dan idan feeling dinsa yatashi bame dakatar dashi, kwanciya yayi yasa kansa sama, yana kallon ceiling, yana tunanin kyawun sura irin na Zuhura, dan gaskiya idan yana ganinta haka, to watarana baze iya sarrafa kansa ba, ze aiwatar ne kawai kowa ya huta, da wannan tunanin bacci ya kwasheshi
cikin dare yaji muryarta tana fadin "yaya Ammar zansha ruwa" nikam nace lallai Zuhura kin rika wato Ammar ne ze tashi ya baki ruwan
, cikin bacci yaji maganarta hakan yasa bude idanunsa
ya saukesu akanta yana fadin, "menene zazza
in ne yadawo" "ah ah ruwa nakeson sha" mikewa yayi ya sauka daga kan bed din yaje fridge yadauko mata kana yadawo, nidai ina kokonto anya Ammar ne kuwa
to muje dai zuwa
, ya bude mata, yana mikamata, maimakon ta karba seyaga ta matso da bakinta saitin gorar, tsayawa yayi yana kallonta, kamar wanda be gane me take nufi ba, kallonshi tayi tace "kishirya nakeji fa" se lokacin yadawo hayyacinsa, ya dora mata gorar kan bakinta tafara sha, seda ya isheta kana ta ture jarkar, takoma takwanta, shikam kallonta kawai yake dan gaba daya ta sauya mai kamar ba ita ba, Ammar kenan darasin aunty Aisha tafara dauka
mikewa yayi yaje ya ajiye gorar cikin fridge yadawo shima ya kwanta, matsawa tayi kusa dashi tana shigewa jikinsa, wani irin shock yaji ajikinsa, itakam bama tasan yanayi ba, kawai son jikinta ne ya kaita, fuskarta ya leka yaga bacci take, a zuciyarsa yace 'yarinyar nan batason waye ni ba, so take ta tdokanoni nakasa control din kaina' cikin zuciyarsa yake wannan zancen, idanunsa ya rufe, yana shakar kamshin jikinta, itakuma se kara shigewa take jikinsa kamar wata mage, blanket din yaja ya rufe su sosai,
PARIS
Ilham nagani zaune a wani hadaden falour, ta dora kafa daya kan daya, tasha kayan bacci, wani mutum ne ya futo wanda shine mijinta, karasawa yayi kusa da ita, ya zauna kana yace, "sweet bazaki kwanta dawuri ba" "kana bukata nane" murmushi yayi yace "aini kullum cikin bukatar ki nake, hannunsa yakai saman cikin ta yana shafawa yace "ya lafiyar baby dinmu yanadai kalau ko" hannunta tadora saman nashi tace "yana lafiya" "Sweet tashi muwuce bedroom" mikewa tayi ba musu suka shige, nikuma suka barni a tsaye, ina binsu da kallo, nace lallai su Ilham an kwantar da hankali, anmanta da Ammar, rayuwarta take cikin farin ciki, ta mance da komai ta gyara rayuwarta, kuma ta kudiri niyyar zatayi zaman aure, harta samu aljanar ta a karkashin kafar mijinta,
Chapter 75 · 0% Book details