← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 97

Sashe 41

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

SOYAYYA DA IZZA Story and writing by Hadizatu Mrs (KD) Yar amanar jajirtattu https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau Ina masu bibiyar books dina to ina muku albishir da sabon book dina dana fara rubutawa me suna YAN BIYU NE ina baku shawara ku bibiye book din nan dan akwai chakwakwa kiya kala kala zaku nishadantu zakuma ku wa'azantusosai kudai kawai ku bibiye kafun free page yakare ku biya kan naira 300 kacal ba tsauwalawa ina alfahari daku masoyana kune kwarin gwuiwa ta i love you so much my pans ina godiya da addu'o'in ku dayacce kuke yabon book dina duk da shine nafarko, gudiya buhu buhu nice taku har kullum Hadizatu wacce kukafi sani da (MRS K D) kucika da bibiyata nukuma zanci gaba da nishadantan daku page 41 ___________________Harta gama samai besani ba , ya lula cikin kallon ta yana tunanin da shi kadai yasani, matsawa tayi, kana takalle shi, shima ita yake kallo, Mamy ce tafado dakin tana fadin, "son kamaji wai ba se an tafi dashi ba, tunda dawo dashi za ai nan din" se lokacin ya dawo hayyacinsa, yayi saurin kallon Mamy yana fadin "hakan ma yayi" "Zuhura kije kiga Jummai takarasa shirya Nadra" amsawa tayi da to tana fucewa, binta da kallo yayi, harta fuce "son su Abba fa sun futo suna falour" "ok ai nima nagama" "to kasa babbar rigar mana" "ah ah Mamy bayanzuba" "tom shikenan muje" tafada tana daukan jakarta, futowa falour sukai, duk sun hadu tafiya kawai ake jira, harda amarya Ilham tana zaune taci shadda golden yellow dinkin yasha duwatsu tun daga sama har kasa, se kyalli take tana walwali, futowa Zuhura tayi ita da Nadra se Jummai da take binsu abaya, itama tayi kwalliyarta dan Mamy tayi mata dinki har kala biyu, mikewa sukai dukansu suka fuce zuwa farfajiyar gidan, Bala driver ne yakwashi su Nadra da Muhsin da Zuhura yatafi kaisu airport, shikuma Jawad yadau Ammar da Ilham da Mamy da Abba, Abba ne agaba, sukuma suna baya, "jummai idan bala driver yadawo zaku tawo" "tom Hajiya" daga haka suka wuce, Abba ne ya kalli Jawad dake waya yace "Jawad kashe wayar nan kasan dai dokan tuki ko" tom yafada yana fadin "Yasmeen ina driving idan na sauka zan kiraki" kana yakashe wayar, shikam Ammar yajuyar da kansa yana kallon gefe fuskar nan a tamke kamar an aiko mai da sakon mutuwa, Mamy na lura dashi, harsuka isa airport be kalli Ilham ba, bayan sun isa suka isa jirgin suka shiga, ita dai Zuhura gabanta nata faduwa dan bata taba hawa jirgiba, wani iri takeji wai yau itace zata shiga jirgi, a daddare take hawa matartakalar jirgin, bayan sun shiga, taga kowa yana duba number kujerar, can baya Ilham da Mamy sukai, sukuma su Jawad suna tare da Abba, Muhsin kuma da Nadra na can gefe, shikam gogan tuni ya zauna, itama dubawa tashiga yi, setaga kusa da Ammar take, hakan yasa tazauna kusa dashi, ita dai har yanzu zuciyar ta bugawa take, har ta zauna, announcement aka fara kowa yasa belt jirgi ze tashi, sawa suka fara itama sawar tayi, bugun zuciyar ta na karuwa, lokacin da jirgin yafara tafiya kamar ta nutse saboda tsoro, jirgi yana tashi, tasaki wata razananniyar ajiyar zuciya, tana kamo damtsen hannunsa ta kamkame, tare da rumtse ido, kama hannunta yayi data zagayo dashi ta damtsensa, yana shafa hannunta a hankali dama yana taso ya taba fulawar tata, itakam bama tasan meke faruwa ba, cikin ta ya kada ya duri ruwa, kara tura kanta tayi jikinsa tana kanainaye shi sosai, seda sukai 30mint a haka, daga baya tafara bude idonta, se lokacin ta tuna wa ta rike, da sauri taci ka shi, shima hade fuska yayi yana kawar da kai gefe, tuni ta nutsu ta dawo hankalinta, "yaya Yasmeen kifuto inji Daddy ke ake jira" "ok muje au tsaya na dau bag dita" daga haka tadauka suka futa, duk sun hallara a falourn , Inna boil les me adon orange yayi bala'in yimata kyau, shikuma yasa shadda ligh blue, Yasmeen kuma tasa atamfa, iri daya sukai da Amira dinkin riga da skirt, shikam Halifa kanan kaya yasa yasha takalmi, kamar wani saurayi se iyayi yake, "to mu tafi dan inaso nasamu daurin auren nan" daga haka suka rankaya suka tafi, driver ne yakaisu airport, suma jirgi suka bi, ita dai Inna se Alhaji Aminu ne yarige ta dan dagyar ta iya hawa jirgin, shikam Halifa a rawar kanshi yashige, Amira kam basarwa tayi tana iyayi tashige, daga haka dai har jirginsu ya tashi bayan sun sauka driver yazo yatafi dasu, gida kam harya cika, A'isha ma kanwar Abba ta iso ita da mijinta, falour suka zauna anata gaisawa, shikam Ammar bayan yagama gaisawa ya wuce bedroom din Ahmad, dan baya san jama'a dayawa, samun Ahmad din yayi yagama shiryawa cikin shadda ashhh colour yanasa hula, beji sallamar sa ba , saboda can cikin makoshinsa yayi, sedai kawai yaganshi zaune saman kujera ta mirror, juyowa yayi yana fadin "haba ango ai seka tsora tani" be kulashi ba, yakara cewa "kace dai kun iso" "eh" abunda yafada kenan, shima bekara magana ba, raba ido kawai Zuhura take ko zata ga Ahmad, dan a zahiri tayi kewar sa sosai, ganin bashi ba alamar sa yasa taci gaba da zaman, su Jawad kuwa dasu Muhsin tuni sun bar falourn sun wuce gurin sauran cousin dinsu, ya'yan yayyen Abba da kannensa, dan family din sunada yawa ba laifi, susu 11 ne agidansu, dan haka kowanne su nada iyali , Hajiya ce da Hajiya Zainab kadai suka rage a matan Alhaji, hira suke tayi na yaushe gamo, itakam Zuhura tayi tsamo tsamo a cikin su, aunty Aisha ce takalle ta tace "aunty Khadija ya'r taki bata magana ne" murmushi Mamy tayi tace "tanayi mana bukuji damuka shigo ta gaggaisheku ba" "naji tayi shiru ne" "ina su zakiyya suzo su tafi da ita ko tafi sakewa a cikinsu" "oh su zakiyya sunacan compound din gida suda su Aliya naga ma su Jawad da muhsin agurin" "Nadra tashi ku rakata keda Afnan" amaswa Nadra tayi tana mikewa, tashi Zuhura tayi tabi Nadra suka fuce, "aunty Aisha ce takalli Mamy tace "aunty Khadija da ina da namiji ai da nayimai mata, gatanan tabar kallah kyakkyawa" "gaskiya dai" mom din Ilham ce tafuto tana fadin "wai haryanzu yarannan basu futoba gashinan 11 saura" "ai kema dai kya fada" ku kyalesu mana angwaye ne fa kukasan mesuke tattaunawa" dariya sukai kawai mom Ilham tasamu guri tazauna, Ilham anyi dai dai kan bed ga kawayenta zagaye da ita, sunata hira suna shewa, sai kace ba amarya ba, "yaudai Ilham zaki zama matar yaya Ammar dinan kowa ya huta" "ai jina nake kamar in zuba ruwa akasa nasha saboda dad'i" "gaskiya dai zakiji " daga haka suka cigaba da shewar su, "Ammar queen tazo ko"? wani kallo ya wurga mai kana yamaida kansa kan wayarsa, "nidai zanje naganta kai ka zauna anan" wani irin kishi ne yataso mai wanda besan yanada shi ba se yanzu haka ya danne bece komai ba, turare Ahmad yadauka yana fesawa, wayar Ammar tayi kara, dagawa yayi yanafadin "hello abba" "yawwa Ammar ku tawo zamu wuce gurin daurin auren, kowa ya ya hallara" da to kawai ya amsa yakashe wayar, Ahmad ne yakalle shi yace "lokaci yayi ko" kadamai kai kawai yayi, lamar eh, daga haka suka mike suka fuce , yana futowa suka fara mai guda matan dake falourn, shikam ya tamke fuska kamar me, harya fuce suna mai guda, bayan sun futa, suka tarar da sauaran abokansu kokuma ma nace cousin dinsu duk sun hallara, karasowa suka fara yi suna gaggaisawa suna musabaha, masu tsokanarsa nayi, ba abokinsa ko daya, saboda be gayyaci abokansa ko daya ba, su Alhaji aminu ne suka karaso, bayan sun futo daga cikin motar, suka fara gaggaisawa, sukuma su Inna dasu Yasmeen suka shiga ciki, Zuhura na ganinsu ta tawo da gudu ta rumgume Yasmeen, se lokacin Ahmad yaganta, jiyayi kanar ya tafi inda take, sedai kuma ai maman ta tana gurin, hakan yasa kawai yacigaba da amsa gaishe gaishen mutane, bayan sun isa, Mamy ta taso tana tararsu, gurin zama tanuna mata tazauana, kana suka fara gausawa, gabatar da ita Mamy tayi amatsayin matar Alhaji Aminu, kowa kam ya yaba da kyan ta, kuma sun sakar mata fuska, Yasmeen kam janye Zuhura tayi suka koma gurinsu Aliya, mom Ilham ce tashiga tace Ilham taje tayi wanka tasake kaya, "mom dazamu tawo fa nayi" "bansan dogon zance kije kiyi wanka kisake kaya kafun yan daurin auren su dawo" ba a san ranta ba ta tashi tayi wankan tashirya, su Jummai suma kafun adawo daga dauro auren suka iso dan haka aka karasa girkin biki dasu, suna dawowa gida ya kaure da guda, ana angwaye sun dawo, shikam Ammar zuciyarsa kamar tafashe, haka Ilham tafuto aka dinga hotuna , duk hoton da akeyi fuskarsa a tamke, sukam Abba part din Daddy din Ahmad suka wuce gabadayansu, Yasmeen hira suke tayi, wayar ta tayi kara, Jawad ne ke kiranta, hakan yasa tamike tabar gurin saboda hayaniyar dasuke, "hello yaya Jawad" "Yasmeen dama kunzo baki neme niba" "bamu dade da zuwa ba kuka tafi daurin aure" "ok to yanzu kifuto inasan ganinki" daga haka ya kashe wayar, komawa dakin tayi tadau mayafinta, tace musu zataje ta dawo, sekin dawo kawai suka cemata, tana futowa compound din gidan ta hangoshi hakan yasa tanufe shi, harta karaso yana murmushi, seda takaraso, ya kalleta yace "wow kinyi kyau sosai fa" "na gode" hirarsu suka cigaba dayi suna dariya, zamewa yayi daga gurin hoton dan ya gaji dama kawai dai yanayi ba a san ransaba, bedroom din Ahmad yakoma yacire babbar rigar ya hau kan bed ya kwanta, abinci aka fara rabawa dama sundauko masu saving, dan haka suka shiga aikinsu, sunata raba abinci, mom ce tace ma da Ilham takaiwa mijinta abinci, abincin tahada mata, takarba tawuce bedroom din yaya Ahmad, tana zuwa ta tura kofar, yana kwance idonsa arufe kamar me bacci amma ba bacci yake ba, abincin ta ajiye tanufesa, hannu takai ta taba shi, bude ido yayi, yana kallonta, dasauri yamike yana hade rai, "yaya
Chapter 41 · 0% Book details