← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 97

Sashe 76

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

SOYAYYA DA IZZA
Story and writing by Hadizatu
Mrs (KD)

Ina masu bibiyar books dina
to ina muku albishir da sabon book dina
dana fara rubutawa
me suna YAN BIYU NE ina baku shawara ku bibiye book din nan
dan akwai chakwakwa kiya kala kala zaku nishadantu
zakuma ku wa'azantusosai kudai kawai ku bibiye kafun free page yakare ku biya kan naira
300 kacal ba tsauwalawa
ina alfahari daku
masoyana
kune kwarin gwuiwa ta
i love you so much
my pans
ina godiya da addu'o'in ku
dayacce kuke yabon book dina
duk da shine nafarko, gudiya buhu buhu
nice taku har kullum Hadizatu wacce kukafi sani da (MRS K D) kucika da bibiyata nukuma zanci gaba da nishadantan daku
DOMIN SHIGA GROUP DIN SOYAYYA DA IZZA KA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA
https://chat.whatsapp.com/FPb99RjggTbAcCFg1aFrVx
DUK ME BUKATAR SOYAYYA DA IZZA YA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA
https://whatsapp.com/channel/0029VahPZYb6WaKlZQvivt0J
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_

alaminmu
ancinmu
page 62
_______________________________________________________________________
_____________________________
________________ Asuba nayi yafarka, yana janyeta daga jikinsa dan gabadaya manne jikinsa, janyeta yayi yadda bazata tashi ba, kana ya mike ya wuce toilet, alwala yayi kana yazo ya gabatar da sallar asuba, kana yayi azkar dinsa yayi addu'oinsa, juyawa yayi yana kallonta, yadda take baccinta hankali kwance, mikewa yayi yakoma kan kujera ya kwanta, ya rufe idanunsa, yana tunanin sauya zamansu da Zuhura, dan gaskiya baze jure ba, da wannan tunanin wani sabon bacci ya kwashe shi,
itakam bata farka ba se karfe 8:00pm tana tashi tashige toilet tayi wanka, kana tazo tadau kaya doguwar riga mara nauyi tasa, kana ta tufke gashinta tadau hula tasa, ta fuce, tana futa ta tarar da aunty Aisha a kitchen tana hada abincin karya wa, shiga kitchen din tayi, tana gaida aunty Aisha, ta amsa cikin fara'a kana tace "jiya inata jiranki naji shiru" "aunty jiya banji dadi bane shiyasa" "ayyah sannu kuma nace da Ammar yaje ya dubaki kuma be dawo ba" "eh yamun allura ne" "kice dai shiya kula dake" murmushi kawai Zuhura tayi kana tafara taya aunty Aisha aiki, nan suka gama kammala komai, me aiki ta shirya yara, suka wuce school, "Zuhura maza kije ki tashi Ammar dan naga kamar ma yayi latti" "to aunty" "kuma karkije ki tsaya mai aka wai kina tashinsa, kiyi salonki har ya tashi kinjiko" kai kawai ta kada mata cikin jin kunya, daga haka aunty Aisha tawuce, itama Zuhura ta wuce, tana shiga ta taddashi yanata baccinsa, tsayawa tayi tana tunanin yazata tasheshi ma, ,Zuhura kicirr tsoronshi ki tadashi kamar yadda aunty Aisha tafada maki' zuciyarta tafada mata, tsugunnawa tayi gabansa, tana kallon kyakkyawar fuskarsa, dake kewaye da saje baki wuluk, hannu tasa tana shafa sajensa, tana kallon shi, tabbas yaya Ammar kyakkyawan gaske ne tafada cikin zuciyarta, jin kamar ana shafa fuskarsa, yasa yabude idanunsa, yana saukesu akanta, ganin tsoro ne yakamata, amma ta dake tace "katashi zaka makara" daga haka tamike, wayarsa yaduba yaga 9:44pm dasauri yamike, kallonshi tayi tace, "kafun kafuto bara na hadama breakfast" "ok kikawon nan" daga haka yashige toilet, fucewa tayi, hadamai tafarayi kana tashiga kitchen ta hadamai coffee, tadawo tawuce bedroom din, yana tsaye gaban mirror yana shiryawa, yanasa balle bottle din rigarsa, seda yazo nacan wuya yadinga kiciniyar ballewa, amma saboda sauri sam ya gagara, tire din dake hannunta ta ajiye tana nufarsa, tsaywa tayi gabansa, tana dage, tafara balle mai bottle din, kallonta kawai yake yanajin kamar ya rungume ta a jikinsa, dahaka takarasa sakamai, bayan tagama tace "ga breakfast dincan" "inaga abarshi kawai nayi latti sosai" "no gaskiya sekasha ko coffee ne" tafada tana nufar inda ta ajiye tire din tadauko cup din coffee, ta nufeshi, shikam kallonta kawai yake, mikamai tayi, ya karba yana kaiwa bakinsa, kurba biyu yayi yafara kokarin ajiye cup din gaban mirror, saurin rike hannunsa tayi, tana fadin "Please ka kara karka futa cikinka ba komai" kallonta kawai yake, harta dau cup din tana kaimai bakinsa, idonsa na kanta, hanninta ya rike ya kai cup din bakinsa, idansa nakanta hakama itama kallonsa take, seda yasha rabi kana ya sakar mata, yana daukan wayarsa tare da key din mota, yace "nawuce" bejira amsar taba yafuce, itakuma tashiga gyaran dakin tanajin wani farin ciki aranta yadda taga Ammar yasake da ita,
bayan Ahmad yagama breakfast, yacewa dasu daddy shifa kaduna ze wuce, sun tambaye shi me zeyi a kaduna, yace zeje yabawa su Abba dasu Mamy da Hajiya dama mahaifiyar Zuhura hakuri, hakan dasukaji yace yasa sukace seya dawo, shi dama oredy yayi booking flight, hakan yasa yana gamawa yanufi airport, nan da nan jirginsa yatashi, se Kaduna, yana zuwa gidan Mamy yawuce, suna zaune a falour suna hira lokacin karfe 1:30pm yana shiga da sallama duka suka zubomai ido, karasawa yayi ya zauna kasan carpet yana gaidasu, da mamaki suka amsa, "Mamy nasan kunyi mamakin ganina" "kamar kuwa kasani munyi" Hajiya tafada "Hajiya Mamy dan Allah kuyi hakuri kan abunda yafaru" "haba Ahmad ai munsan ba yin kanka bane aikin asiri ne" Mamy tafada cike da tausayinsa "bakomai ai yawuce sedai kuma ka nemi yafiyar ita Zuhura" "hakanne yasa nazo dan nasamu number ta nakirata na nemi yafiyarta" "toka kira wayar Ammar mana ya hadaku" dan sosa keya yayi kana yace "nakikirashi be dauka bane" "tohh kuma kaga number Zuhura bata shiga muma wayar Ammar muke waya da ita" "am Mamy ina su muhsin da Nadra ne" "ai suna school" "ok Jawad fa najima ban ganshiba" "ohh Jawad kasan yanzu aiki shiyasa" "gaskiya kam aikam zanje har gida mugaisa dashi" "daka kyau ta kuwa" "tashi kaje ka watsa ruwa sekazo kaci abinci ko" mikewa yayi yashige, "wlh Hajiya ina tausayin yaron nan" Mamy tafada "Allah ya kadarta haka seta faru to mu mance da komai" "gaskiya kam mu godewa Allah ma da asirin ya bar jikinsa" "to Allah ka kara tsaremana du" "ammeen"
Nafeesa na kwance a gadon hotel din data kama, taji ana knocking, hakan yasa tamike tanufi kofar tana budewa, ma'aikacin hotel dinne, "lafiya" Nafeesa tafada tana kallonsa, "dama madam kudin dakinki ya kare fa naga kamar kin mance shine aka ce nazo natina maki" "ohhh Allah na yi hakuri dan Allah bara na hada kayana" takarashe mganar tana komawa ciki, zama tayi ta rafka uban tagumi, saboda gabadaya yanzu kudinta ya kare a biyan kudin daki, ba yadda ta iya haka tashiga hada kayanta, hoton Mommy dinta tagani cikin tv dana Alhaji madu, wato dadiron Mommy dinta, ana labarai akai, tsayawa tayi tana gani, wani irin kuka ta fashe dashi, tana fadin "wayyo nashiga uku Mommy yazanyi wane tsanenene wannan ya salwantarmin da mahaifiya" wayarta tashiga nema, tuni tadauka ta danna kiran DPO yana dagawa tace "meke faruwa ne kaga labari kuwa" tafada cikin kuka, daga cikin wayar yace "nagani wani yasiyar da wasu part ajikin mahaifiyarki" "to amma meka tsaya kanayi" "so ai hukumar yan sanda ta kamashi yana hannunmu" "ok kajirani zanzo office din yanzu wlh hazan yarda ba" daga haka takashe wayar tana figar akwatinta,
bayan Ahmad yayi wankasa fees yazo yaci abinci, kana yacewa dasu Mamy zeje gidan mahaifiyar Zuhura yabata hakuri, hakan yasa sukace se ya dawo, daga haka yafuce, yana futa ya hau mota yanufi gidan Inna, bayan ya isa me gadi yabude mai gate yashiga da motarsa, bayan yafuto yanufi cikin gidan, yana shiga falourn da sallama, Mahmud ne da Amira zaune sunata shan hirar soyayya, Mahmud na ganinsa yamike yana nufarsa, hannu ymimai suka gaisa, dayake sun san juna, itama Amira gaidashi tayi ya amsa cikin fara'a, "yaushe kashigo garin ne yaya Ahmad" Mahmud yafada yana kallon Ahmad, "yau nashigo" "ok Amira kiyiwa aunty magana" tashi Amira tayi tawuce, ba jimawa ta dawo ita da Inna, zama Inna tayi saman kujera, shikuma Ahmad ya sauko kasa, yana gaidata, amsawa tayi fuska a sake, kana yashiga bata hakuri kan abunda yafaru shida Zuhura "bakomai Ahmad kaddararku ce a haka kuma ba laifinka bane" "nagode" "bakomai ai" "nace kozan samu nimber Zuhura dan inason nabata hakuri na nemi yafiyarta" "yaya Ahmad ai number ta bata shiga" Amira tafada, "gaskiya dai bata shiga" ji yayi ransa ba dadi, hakan yasa yace "ok shikenan bara na wuce" daga haka yamike yana masu sallama, Mahmud ne yatashi dan ya rakashi, haka sukai sallama da Inna, bayan Mahmud ya rakashi ya nemi yabashi number Yasmeen, be tambayeshi me zeyi da ita ba kawai yadauka yabashi, sukai sallama, cikin gaggawa ya shiga kiran Yasmeen seda yakira har sau uku se ana hudun ta dauka tana fadin "hello waye" "sorry Yasmeen na takura maki ko" "ah ah bangane me magana ba" "yaya Ahmad din Zuhura ne" "ohh yaya Ahmad ina yini" "lafiya lau Yasmeen, dama number Zuhura nakeson kibani nakira tsohon layinta baya shiga" "gaskiya bani da sabon sim dinta" "to yanzu yazanyi kenan agurin wa zan samu" "ina ganin asamu gurin Maryam" "ok a ina take Maryam din" "a can unguwar su Zuhura take, amma zan baka number ta kakira ta" "yawwa Yasmeen nagode" "amma yaya Ahmad me zakayi mata matar aure cefa yanzu" "stop Yasmeen zuciyata tana zafi idan kina fada" "to Allah ya huci zuciyarka" "ok shikenan magode kituramun yanzu" daga haka yakashe wayar,
bayan Nafeesa ta isa Police station, ta tarar da Alhaji madu cikin sale, ji tayi kamar ta kasheshi saboda bakincikin daya sata ya kashe mata mahaifiya, "karki damu nafeesa anjima kotu zamu wuce dashi" "amma dai ya cuceni ya rabani da mahaifiya ta" "to wai ita mahaifiyar taki meya hadata dashi da har mata wannan aika aikn" "kaga DPO karka dameni da tambaya" "tobara kiji ya cire part biyar jikin mamanki ya siyar a kasar waje, kinga kuwa ai dole muyi kwakkwaran bincike" "kai Allah ya tsinema wlh kasani cikin bakin ciki da takaici" dan matsawa kusa da ita DPO din yayi kana yace "kozamu shiga office dina ne kidan bani abunda ze kramun kwarin gwuiwar bincike" harara ta daka mai kana tace "nika barni da abunda ya dame ni bazan bayarba" kallonta yayi kana yace "kanki kika yiwa ai" yana kaiwa nan yafuce, jitai gaba daya duniyar tadena mata dad'i komai yamata zafi bata dakowa yanzu se ita kadai, zama tayi ta dafe kanta tana tunanin ina ta nufa daga nan,
LONDON
bayan sun kammala aikinsu tas, misalin karfe 5:00pm ta wuce dakinta da tayi wanka, tanyin wanka tashirya cikin riga da wando, rigar har gwuiwarta, gaban rigar duka bottles ne masu kyalli, ba karamin kyau tayi ba, ta tufke gashinta da riboom kalan kayan, kana tadau dan kwalin kayan ta daura, ta feshe jikinta da turare, kana tafuce, samun aunty Aisha tayi a zaune tan chat da mijinta, zama tayi kusa da ita tana fadin "aunty Aisha sannu d chat" "ke Zuhura ina chat da habibi nane" "gaskiya kam aunty Aisha ki kula dashi" "wow wannan irin kyau haka ai sekisa dana ya zauce" "kai aunty Aisha yaya Ammar din" "da anyi magana sekice yaya Ammar din" "ai aunty Aisha yafara saukowa jiya ma gado daya muka kwana" "what dama ba gado daya kuke kwana ba" tsuru tsuru da ido Zuhura tayi tana kallon aunty Aisha, "ke meyasa kike haka kamar ba mace ba, kikasa sawa namiji mutu akanki musamman ma keda yakesonki" "nifa aunty Aisha kunya nakeji" dungureta aunty Aisha tayi tana fa
in "matsa ca kibani guri mara wayyo ta inda Yasmeen ta fiki kenan" ita dai Zuhura lakwas tayi tanjin aunty Aisha, haka aunty Aisha ta dinga mata fada, tana koya mata dabaru, na janyo hankalin miji, a haka har 6:00pm tayi, suna zune suakaji shigowar Ammar, sannu da zuwa Zuhura tamai ya amsa, kana yace ma da aunty Aisha yadawo, daga haka yashige, kallon Zuhura aunty Aisha tayi kana tace "jira kike nace kibishi" kallonta Zuhura tayi "senace kibishi wai" hanya Zuhura takama tawuce, aunty Aisha ce takirata hakan yasa tadawo, bottle din rigar aunty Aisha tahau balle mata, ganin haka yasa Zuhura zaro ido tana kallonta, "kinbi kin wani rufe jiki ruf taya zeki ja hakalinsa" ganin aunty Aisha ta balle mata bottle har uku, har ana iya gano dukiyar fulaninta, tace "aunty Aisha a haka zanshiga" "eh kuma kada kisake ki gyara" itadai Zuhura ba'ason ranta ba tawuce, tana shiga taganshi yana rage kayan jikinsa, kallonta yayi kana ya kauda kai, daga haka ya shige toilet, yana wanka yana tunanin ta yadda yaga tayi shigar tayi matukar kyau, daga haka dai yafuto, gaban mirror ya tsaya yana shafa lotion, itakam kallonsa kawai take tanajin sonshi yana kokarin cusawa zuciyarta, wayarsa ce tadau ringing datake kusa da ita, "mikomun wayata" mikewa tayi tadau ka tanufeshi, seda takusa mikmai kiran ya katse, karba yayi yana ajiyewa gaban mirror, kana yajuya yana kallonta, idanunsa ne ya sauka kan kirjinta da suka dan futo ta rigar, ji yayi yakasa janye idansa, ganin inda yake kallo yasa Zuhura tafar fadin "am...na....bara..naje" tafada tana kokarin juyawa, besan sanda ya fuzgota ba, yana kallon fuskarta, wanda itama shi ta tsurawa ido, hannu yasa yafara balle mata bottles din, ya rufe mata rigar, kana ya kalleta yace "bakisan waye mijinki ba ko, to bana iya sarrafa kaina idan naure, kuma zamisha wuya ne, idan kuma zaki jure to" wata irin kunyace ta kamata, batasan sanda ta kifa kanta cikin kirjinsa ba tana rufe fuskarta, shidai ji yayi yayi mutuwar tsaye, yaji inama su dawwama a haka, ganin yaki motsi itakuma kunyarma hada ido take dashi, hakan yasa nima MRS KD ta tarkata komatsaina nafuce tabarmusu dakina dan naga abun nasu batamun lokaci zeyi
Chapter 76 · 0% Book details