← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 97

Sashe 26

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

SOYAYYA DA IZZA
Story and writing by Hadizatu
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan
asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau
page 27
_________________ Dasafe tana tashi bayan tagama komai, itama taje ta tashirya tafuto cikin uniform, ash da fari, skirt be iya gwuiwa ash colour, se farar riga me dogon hannu ,se hijabi fari, safarta tasa fara tarufe mata har kwairinta, jakarta tagoya, uniform din sun mata kyau sosai, Bala driver ne ya shigo yace musu insun kammala yana jiranasu, sun gama komai dan haka kawai suka fuce, har cikin makaranta hakaisu, class Nadra da Muhsin suka wuce, ita kuma office din principal tawuce, bayan taje ne, principal din ta hadata da wani malami daya kaita ajinsu ya gabatar da ita, hakan akai aji yakaita, ya gabatar da ita, gurin zama yanunamata, mutum biyune mata itace ta uku, bayan malamin yafuta ne, daya dag cikinsu takalleta tace, "nice to meet you my name is islam" thank you" dayarce tace "nikuma my bame is walida" ok nice to meet you all" danaka suka saba har suka fara fira kamar su san juna, malami ne yashigo hakan yasa duk sukai shiru, gaishe shi sukai, kana yabasu izinin zama, koyar dasu yashi yi, kuma ba laifi kuma suna ganewa, bayan yafuta ne, Walida takalli Zuhura tace"amma dai kingane ko" murnushi tayi tace "eh nagane" indai akwai Abinda yashuge miki duhu ki tambaye mu inshaallah" murmurshu takarayi tace "karku damu indai naga abinda bajganeba zan tambaya, Nagode da kulawa" bakomai ai yanzu munzama daya" Zuhura taji dadin yanda suke nunamata kulawa,
Abba ne yakira alhaji Aminu yasanar dashi sungama magana koyau yakawo kudi, yayi murna sosai har yace yau zezo, bayan sun kammala magana yakashe wayar,
Ammar yana part dinsa be ma futoba har anyi azahar ko break fast be fito yayi ba, dan yau ma kwata-kwata bayasan fita hispital, yana zaune a falour yana aiki a laptop dinshi, wayarsa yadauka yakira Mamy "hello Mamy insan coffee" au bazaka futoba yau kenan"? Mamy ina aiki ne shiyasa" ok to bara akawoma" daga haka takashe wayar, ajiye wayar yayi , se lokacin yatuna batanan taje school, seyajima baya sha'war coffee din, Mamy ce tafuto tasamu Ilham a falour ita kadai tana danna waya, "am Ilham kikaiwa Ammar coffee " tom Mamy" daga haka tawuce kitchen din, hadamai tashigayi, kwata-kwata bata iya hadawa ba , a haka dai cakuba tagama ta tsiyaye a cup tawuce part dinsa, tana shiga ta tadda shi a falour, karasawa tayi tana wani karya jiki, ko kallonta beyiba ballantana yanuna tashigo, "yaya Ammar ga coffee dinka" ok ajiyeshi anan" abunda yafada kawai kenan batare daya dago ya kalletaba, ajiyewa tayi tasamu guri tazauna, kallonta yayi yace"lafiya kuwa"lafiya mana" to tashi kije" wai ya Ammar korata kake" kinga bansan hayaniya dan Allah tashi kiwuce" shikenan naji" daga haka tafuce, falour tafuto rai a bace, Hajiya ce takalle ta tace "ke kumafa kike bata rai ko dai keda dan iyayinki ne"? Allah Hajiya nagaji da abunda yaya Ammar yakemun" haka zaki hakuri mu daura muku aure kuta fi can yadena" daga haka Hajiya tamika tana fadin "bara naje kitchen dincan naga me ake dafawa" daga haka tawuce tabar Ilham a zaune, Ahmad ne yafuto daga dakinshi da alama futa zeyi, Ilham ce takalleshi tace "ah yaya Ahmad ina zaka"? "zanje dauko su Zuhura daga school naga time yayi" yaya Ahmad dakaine kake daukosu"ti daga yanzu nafara"nifa yaya Ahmad bangane maka ba da yarinyar nan"sonta nake kuma zamuyi aure" da wannan yarinyar haba yaya Ahmad" wayar sace tai ringing , yasa ya futa yana daukan wayar, "hello Nafisa ina hanya ne zankirki" daga haka be jira me zatace ba yakashe wayar, bin wayar tayi da kallo tana fadin "kungafa yakashemun waya" kadan ma kika gani indai maza ne" kai gaskiya Ahmad yasauya sosai, dafa arana se yakirani Kusan sau biyar, zuwa kuwa dama tare muke kwana ko nace yatafi se yaki" kinga kawai tashi zaki kitsaya ki auresa kiwuce gurin" Allah kawata"wlh haka zakiyi kawai" daga haka suka tafa, sauri yake tayi ya karasa karsu gaji da jiranshi, bayan yakarasa makarantar, samun su yayi a zaune suna ta hira suna dariya, parking yayi kana yafuto daga motar, Muhsin ne ya hangoshi, seda yakarso, har inda take zaune yace, gimbiya barka da hutawa, kallon su Walida tayi tace, "zamu tafi gida se gobe"ok to Allah yakaimu"Nadra muje" hannun Nadra takama su nufi gurin mota, kafun takai har yayi sauri ya isa yabude mata gidan gaba, batai musu ba tashige, Muhsin kuma yashiga baya shi da Nadra, kallonta yayi tace, gimbiyata ya school din"?"Alhamdulillah" abunda tafada kenan, "yaya Ahmad wai ina zaka kabiyo kadauke mu" kamar ya se zani wani gu zanzo in daukeku" to naga baka taba zuwa ka daukemuba" to yau gashi nazo" daga haka ba wanda yasake magana, harsukazo gida, bayan yayi parking su Muhsin suka futo shida Nadra, itama kofar tabude danta fita taji yariko hannunta, juyowa tayi takalleshi, shima kallonta yayi yace, "my queen kamar kina fushi dani ko"? "ah ah banajin haushinka to damme yasa ma zanji haushinka, kawai nagaji ne" kin tabbata"eh" kumatunta yashafa kana yabude mata murfin motar, futa tayi, shima futowa yayi shima, tana shiga falour bakowa hakan yasa tashige dakinsu, nan ma bata ga kowaba, jakarta ta ajiye tafuta, kitchen tashiga, tana shiga taga Mamy da Hajiya ne kawai a kitchen din, sallama tayi , dukansu suka juyo suka kalleta "Mamy mundawo" to sannunku da dawowa" Hajiya mundawo" sannunku ya gajiya" Hajiya aikam da gajiya" kije ki watsa ruwa kizo kici abinci" Hajiya me kike dafa mana" dan wake nake jefamana ai kinaci ko" aikam inaci sosai" yawwa to jeki kiyi wanka kizo nazuba miki kici" Mamy ina Inna"? tayi bako ne yanzu zata dawo" tom bara naje nayi wanka" daga haka tafuce, wanka tayi tashirya kana tafuto, bayan tafuto ne ta tadda Hajiya kan dining, itama zama tayi tana fadin"Hajiya harkin gama" nagama Zuhura bara nazubamiki" plate tadauka tazuba mata tasa mata komai nahadin har kwai, bayan tazubamata ne tamukamata, karba tayi tafaraci tana fadin"kai Hajiya ta kinfi kowa iya dan wake" dariya tayi tace"karfa kifadi garin santi" Allah hajiya ba santi bane" haka suka cigaba daci suna hirarsu, Ammar ne yafuto daga part dinsa, dan yanzu yafarajin yunwa, dan coffee din da Ilham takawomai yakasa sha ba da
i ga daci, ganinsu yayi zaune kan dining sunacin abinci sunta hira suna dariya, karasowa yayi inda suke yana fadin, "Hajiya me kuke ci haka" abincin mu mana" abincinku kuma" eh mana tunda ku bakwa ciba" ah nikam banaci" to ai shikenan" ke jeki hadamun coffee nasha" yafada yana zama, mikewa tayi danta taje ta hadamai, Hajiya ce takalleta tace "zauna ki karasa ci seki hadamai" kallonshi tayi, "Hajiya banfa karya ba" to kuma se akace ka tasheta tana cin abincinta" to Hajiya in ta dawo baseta karasaba" to kai ina matar taka kaje kace mana tahadama wato ita tanacan yar hutu bat iya komai ba" Hajiya nidai kibari kawai dan Allah taje ta hadamun ta dawo" aikuwa seta gama ci zauna ki karasa" zama tayi tacigaba da cin abincinta, seda tagama tas kana ta tashi tanufi kitchen tahadamai, takawo mai, karba yayi yafara sha , Hajiya bara naje nagyara miki dakinki kafun time din islamiyya yayi" bazaki hutaba kindawo kin gaji" ah ah ai nariga na huta" daga haka tashige, tayi hakan ne sabida batasan zama a gurin,
Chapter 26 · 0% Book details