← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 97

Sashe 10

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Soyayya da izza
Story and Writing by hadeexatu
(Mrs KD)

yar amanar jajirtattu
Page 9
6:30am iya lami ta tasheta saboda su nadra na zuwa school sesuyi abunda zasu su gama kuma takara nunnamata wasu abu buwan, ba laifi duk abunda takoyamata tana ganewa, breakfast suka shiga hadawa chips and eggs sukai sannan suka hada kunun gyada seda suka gama tass suka zubawa nadra a lunch box shidama muhsin bayazuwa da abinci, sannan suka koma daki wanka zuhura tayi tasa wasu riga da wando rigar har gwiwa seta daure gashinta da ribom tasa hijabinta hargasa, tafuta falo dama iya lami tace mata nadra tana zuwa makaranta kullum se anje anshiryata dan haka ta nufi dakin nadra budewa tayi ganunta tayi ta dukun kune jikinta blanket din yakoma gefe , wai itah kadai take kwana adakinnan koni ai bazan iya kwana ni kadaiba gaba daya se tausayin yarinyar yakamata , blanket din taja ta lulubeta ta shiga toilet tahada ruwan wanka ta dawo ta tasheta bandakin takaita tamata wanka ta dawo ta shafa mata mai tasa mata uniform ta shiryata tsaf suka futo , nadra muhsinfa ai auty zuhura kullum se anje antasheshi baya tashi dakansa eh mana dakin muhsin suka nufa nocking tayi seda tayi har sau uku sannan yafuto yabude ganin nadra da uniform yace kai harkin shirya kaje kai ma kayi wanka kashirya muna dining munajiranka ok yafada yakoma ciki dawowa sukai kan dining tazaunar da ita tahadamata tea da ta zubada chips da egg din muhsin ne yashigo zama yayi shima tahadamai kamar yadda tahadawa nadra ga kunun gyada azuba muku eh sukace zubamusu tayi a cup kowa ta mikamai, kaidama baka zuwa da abinci ko tun wanne zamanin nadena zuwa da abinci school haka kawai friends dina sudinga mun dariya , zuhurace tayi dariya tace a harkar ci ai ba dariya hakin cikinkanefa kabasa abinci inya bukata nabashi biscuits da lemo tab yaya muhsin daurewafa kawai kakeyi amma nsan kanajun yunwar nadra tafada kedai kikeji angayamiki ni ban da kudi kece yarinya me zuwa school da lunch box , nidai ba yariya bace nagirma ko aunty zuhura kwarai kuwa kingirma sosai makuwa tafada tana dariya, mamy ce tafuto danta hadawa abba breakfast ganinsu tayi sunata fira sunata dariya karasowa tayi zuhura ce ta durgusa har gasa tace mamy ina kwana lpy kalau zuhura sannu da kokari murmushi tayi tamike kunanan kunata surutu ko suma gaisheta sukai ta amsa musu am zuhura insungama kikaisu gun driver yakaisu tom mamy abincin tahada takoma dakin , gunga kuyi sauri time yana tafiya , bayan sungamane ta rakasu hargurin driver sannan ta dawo gyara kan dining din tayi takwashe flate din da suka ci abincin takai kitchen ta wanke takoma daki bacci tadanyi inda suma su inna suketa bacci se 10:00 suka tashi, futowa tayi falo mamy tagani afalo ita kadai yawwa zuhura kintashi eh mamy duk sun gajiyar dake yarannanko murmushi tayi , mamy bara na share falon bazaki bari iya lami tafutoba ah ah bara na share ok to baranaje nadan kwanta tom gyaran tafarayi , jawad ne yafuto cikin shirinshi na kananun kaya kan dining yanufa yazauna kallonta yayi yace zoki zubamun tom tace tanufi inda yake zubamai tayi ta ajiyemai a gabansa waike biki iya gaisuwaba ne ina kwana seda na roka shiru tamai zauna yace mata bata zaunaba kallonshi takeyi shima kallonta yake kizauna nace ah ah ina aiki ne ok tom zaki rakani unguwa zaro ido tayi ina wani gurine to ai ni aiki nake kibarwa iya lami tayi ah ah nidai nizanyi to shikenan jeki cigaba da aikinki tafiya tayi barin gurin tayi takoma daki, kai yarinyarnan na lura akwai duhun kai atare da ita , seda yagama sannan yafuce
Se karfe 11:30 yatashi wanka yashiga seda yayi wanka sannan yashirya cikin kananun kaya ya taje sumarsa yashafa mai se sheki takeyi yayi kyau sosai izzarshi tafuto fuskarshi ba yabo ba fallasa yafuto falo direct dakin mamy yanufa yasameta azaune gaisawa sukai tace kayi breakfast ah ah yanzu dai zanyi ok bara nasa akawoma ok futowa kitchen tanufa samunsu tayi aciki sunata aiki banda zuhura dake zaune kan chair gaisheta sukai su duka ta amsa zuhura zoki zubawa amar breakfast tom tafada tashi tayi tafuta, tarar dashi tayi azaune alamar ita yake jira, karasawa tayi , ina kwana tafada gudun karyace shima bata gaishe shiba be kalletaba be kuma amsaba azuciyarta tace wannan yafiye gadara da girmankai ga izza, zubamai tayi ta ajiyemai agabanshi ci yafara yace ke bazan iya ci ba yayi sanyi kimin wani yanzu ki hado da copie kikawomun part dina tom tace shikuma ya wuce part dinshi sauran kayan kan dining din tadebe tanufi kitchen tanashiga taga iya lami na wanke wanke, iya sannu da aiki yawwa zuhura sannu sun kammala ne eh amma yallabai yace sedai amai sabo wanan yayi sanyi kash mantawa nayi bayacin abinci me sanyi yafusan ana gamawa a kaimai yanzu jeku dauko dankali tom store tashiga tadebo tazo taferaye ta soya sannan tahadamai copie din tadaura kayan akan try tanufi part dinshi kofar falon ta tura yana kwance kan doguwar kujera yana danna wayarsa , da sallama tashiga be kalletaba amma ya amsa sallamar shima iya shi kawai yaji dan ita bata jiba ,karasawa gurinshi tayi try din ta ajiye kan center table tamatsomai da table din gabansa yallabai gashi an kammala mikewa zaune yayi yabude try din yafaraci, itakuma takama hanyar futa kamar daga sama taji muryarsa yanacewa inna gama waye ze futar da kayan dasauri tace nice yayi kyau amma kuma zaki tafi kayi hakura tafada tana dawowa , bawanici dayawaba yamafi shan copie din dan yasha rabin cup, bani ruwa a fridge tom tafada tana nufar inda fridge din yake budewa tayi tadauko ruwan jarka tadawo tamikamai ,cup fa nizan dauko ah ah tagyadamai kai kan fridge din takoma tadauko glass cup tadawo tazubamai ruwan tamikamai karba yayi yasha yamikamata cup din lallai wannan mutumin cup dinma baze ajiyeba sena karba na ajiyemai azuciyarta take maganar daidai lokacin datazo ajiye cup din yafadi kasa ya tarwatse rufe baki tayi tana ja da baya dafe goshinsa yayi saboda karar fashewar glass din, kayi hakuri yallabai wlh bansaniba , ya isheni samo abu ki sharemun tom taje tadauko tsintsiya jikinta na rawa tazo tafara sharewa wata katuwar kwalba ta taka inda kwalbar tashigemata kafarta nandanan jini yafara ambaliya wata wawiyar kara tasaki wanda tasa yaji kansa ya sara kallanta yayi tana zaune rike da kafar tana kuka oh my God wannan foolish girl dinnan seta doramun ciwon kai, tashi yayi yanufi gurinta tanata rusa kuka kaikace guntule kafar akai , matsawa yayi daf da ita habarta yatallabo ya dago kanta yatsansa yadora a lebenshi alamar tayi shiru ganin bawasa a idonshi yasata yin shiru oya tashi ki hau kujera namiki treatment murya da alamar kuka tace baxan iyaba ganin zata batamai lokaci ya yadauketa cak kamar yar tsana yadora kan kujera bedroom dinshi yashiga tadauko first aid box yafara treatment dinta kokarin zaremata kwalbar yake amma yanatabawa seta rike hannunshi tana kuka seda yadakamata tsawa sannan tacikamai hannu yazare kwalbar yafara wanke gurin nanfa tafara ihu tana kiran inna dasu mamy da nadra be kulataba yacigaba da wankemata seda yagama yasa plaster sannan yashare gurin to tashi kitafi tom tafada ashagwabe kokarin tashi take amma sanjikinta ya hanata tana taka kafar setaji zafi takoma tazauna dahaka har yaje yamaida akwatin bedroom yadawo yasameta yadai kitashi kitafi , nidai bazan iyaba kafata zafi takemun tayi maganar a shagwabe ok karasawa yayi yariko hannunta to tashi itama rikeshi tayi gam, ilhamce taturo kofar turus tayi abakin kofa tana kallonsu wanda su bama sugantaba , wash zafi sorry karasa can gurin ,gabadaya ilham kanta ta kulle takasa gane meke farywa
Soyayya da izza
Story and writing by hadeexatu
Chapter 10 · 0% Book details