Sashe 67
Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina masu bibiyar books dina to ina muku albishir da sabon book dina dana fara rubutawa me suna YAN BIYU NE ina baku shawara ku bibiye book din nan dan akwai chakwakwa kiya kala kala zaku nishadantu zakuma ku wa'azantusosai kudai kawai ku bibiye kafun free page yakare ku biya kan naira 300 kacal ba tsauwalawa ina alfahari daku masoyana kune kwarin gwuiwa ta i love you so much my pans ina godiya da addu'o'in ku dayacce kuke yabon book dina duk da shine nafarko, gudiya buhu buhu nice taku har kullum Hadizatu wacce kukafi sani da (MRS K D) kucika da bibiyata nukuma zanci gaba da nishadantan daku DOMIN SHIGA GROUP DIN SOYAYYA DA IZZA KA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA https://chat.whatsapp.com/FPb99RjggTbAcCFg1aFrVx DUK ME BUKATAR SOYAYYA DA IZZA YA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA https://whatsapp.com/channel/0029VahPZYb6WaKlZQvivt0J page 56 _______________________________________________________________________ _____________________________ ________________ A daren yasamu ticket din karfe 12;30pm, se bayan yadawo yaci abinci, aikam yana gamawa yawuce bedroom dinsa, doctor Johnson yakira, ya sanar da shi zeje Nigeria gobe, amma 3 days zeyi, bayan sunyi sallama, ya kwanta, kwata kwata bacci yakasa zuwa mai, tunanin meke damun Mamynsa, dan har ga Allah hankalinsa yatashi, Bayan tayi shirin baccinta, takwanta saman bed dinta, wayarta tadauko ta danna kiran Maryam, aikam bugu biyu ta dauka, "hello Maryam" "na'am Zuhura ya gida" "lafiya lau ina umma" "umma na daki wata kilama tayi bacci" "ai umma dama dawuri take bacci" "wlh kam, Yasmeen ciki ne da ita ashe" "waya fadamaki" "waya mukai da ita, take cemun bata da lafiya" "wlh kam munkusa muyi d'a" "aikuwa da tuni kema kin samu ai kin haifa mana" "tab Allah ya sawwake" "kinjiki bakinason yaya Ahmad dinba" "eh mana inasonshi, sedai shi soyayyar dayake mun takoma kiyayya" "no Zuhura ba laifinsa bane, dukammu munsan yanasonki, kuma ban ganin soyayya sa ta bogi ce, kawai dai sharrin Nafeesa ne" "nima nasani Maryam" "to Allah dai yazabamana abunda yafi alheri" "ameen ya Allah" dahaka sukai sallama, takwanta tuni bacci ya dauketa, kafun suyi bacci, Mamy tasanar da Abba, gobe Ammar ze dawo, yayi mamaki, hakan yasa tasanar dashi komai, tafada mai ita tasa yazo, sunyi magana da Hajiya ma, tafadamai dalilin dayasa tace yazo, shima ya gamsu da maganar ta, hakan yasa yace ta jaraba tagani ko ze amince, amma shidai ba ruwansa, LONDON karfe 10:30am yana tashi yafada toilet yayi wanka tsaf, kana yashiga shiryawa, cikin kanan kaya yafuto yayi matukar kyau ba'a cewa komai, kafun ya kammala 11:00am tayi, yana futowa yatarar ana shirya breakfast, zama yayi, ba jimawa aunty A'isha tafuto ita da mijinta, gaisawa sukai, kana suka tafi dining gabadayansu har yaran, "Ammar A'isha tacemun yau zaka wuce Nigeria" mijin aunty Aisha ya tambaye shi "eh inshallah karfe 12:0pm jirgin ze tashi" "ok gara kuwa ka hanzarta naga 12 din takusa" "Daddy muma zamu rakashi airport" Alisha tafada, babbar yar aunty Aisha, "ah ah kunga itama Mommy dinku ba zuwa zatayi ba" "to Daddy se driver yadawo damu" Arif yafada, kaninta, ya'yan aunty Aisha biyu, "tom shikenan" Ammar yafada, da i ne yakmasu, suka dinga murna, "Ammar dan Allah karka jima, kada kace sekayi sati guda" "kai aunty Aisha ainima bazan zauna ba, saboda aiki" "Ammar lokaci fa ya kusa" "ok aunty Aisha bara muwuce" daga haka suka mike, har yaran, mota driver suka shiga, auntu A'isha ta daga masu hannu, bayan sunje airport din, ba jimawa aka sanar jirgi ze tashi, hakan yasa sukai sallama, yaran harda kuka wai yaya Ammar ze tafi, haka dai driver yadebesu suka juya gida, tana tashi, bayan tayi wanka tashirya cikin atamfa, doguwar riga, tana futowa kitchen tanufa, Jummai ce ke hada breakfast, gaisheta Zuhura tayi ta amsa, kana tafara tayata aikin, bayan sun kammala suka jera saman dining, Muhsin ne yafuto cikin shirinsa, dan yau zeje school, lahadi ne kawai baya zuwa, kan dining din ya zauna, dakin Hajiya Zuhura tawuce, samunta tayi zaune tana hannunta rike da Alkur'ani, sallama tayi, seda takai aya, kana ta rufe Alkur'ani ta amsa mata, bakin gado Zuhura ta zauna tana fadin "Hajiya ina kwana" "lafiya lau muntashi kalau" "lafiya lau Hajiya, an kammala breakfast" "to sannunku ganinan zan futo" "toh" tafada tamike tana fucewa, da ido Hajiya tabita kana tace "ina tausayin yarinyar nan, da karancin shekarunki an maidaki bazawara, Allah dai yasa dai yaron nan ya amince, dan banajin da in ganinki haka, uhmm nasan ma ba yadda zeba tunda ba mutunci garesa ba" kofar tabude tafuce, duk sun hallara saman dining harsu Abba, Hajiya ma zama tayi, kana Zuhura tafara serving dinsu, suka fara ci, Hajiya ce takalli Abba tace "baya yau ne daurin auren Ilham din ba" "ah ah Hajiya se gobe lahadi" "to Allah yakaimu" Muhsin ne yamike, "Abba nizan wuce nagama har nayi latti" "ok to adawo lafiya" Abba yafada "Allah yatsare kayi tuki a hankali" "tom Mamy" "itama Zuhura ai indai wannan abun beyiwuba, to zata fara zuwa school cikin week dinnan" "inshallah ma ze amince" "Allah yasa" ita dai Zuhura tanajinsu bata ce komai ba, kuma batason inda kan maganar ya dosa ba, "Amira" "na'am aunty" "cenema Halifa yaje dakin yayanku yakirashi, naga yau be futo dawuri ba, ga Daddy dinku nan harya futa office" "aunty Halifa fa yafuta keke a farfajiyar gida" "oh ni yaronnan da sassafennan, jeki ke ki kirashi maza" mikewa tayi ba'ason ranta ba, dan tun ranar daya fadamata kalmarso suke wasan buya, tana zuwa tafara knocking, amma shiru, hakan yasa ta tura kofar tashiga, hango shi tayi saman bed a kwance, ya rufe da blanket, karasawa tayi tana fadin "yaya Mahmud aunty tana kiranka" blanket din ya yaye, ya bude ido daker yana kallonta, tana gani tasan ba lafiya yake ba, idanshi yayi sha, hakan yada tamatsa inda yake tana fadin "yaya Mahmud meke damunka haka baka sa lafiya" hannunta yakama, wadanda suke zafi zau, alamr zazza i ne jikinsa, yace "Please Amira kibani amsar tambayata danayimkj dan Allah" "yaya Mahmud kamance da wannan baka da lafiya, ji jikinka zafi" "Amira kifadamun kawai idan kinasona, karkisa fargabar jin abunda zaki fada ya illata ni" hawaye ne zuka fara zubowa daga idon ta, tarike hannunsa kam tace "yaya Mahmud ai yakamata ka gane mana, da banasonka kai tsaye zan sanar dakai, amma bazan iyaba saboda ina sonka" wani da i yaji ya maimaye mai zuciya yace "thank you" "yaya Mahmud katashi muje asibiti" "no dauko wayata na fada miki number doctor seki kirashi" wayar tadauko, yafada mata, ta nemo number takira tasanar dashi yace gashinan, taimaka mai tayi yatashi, yashiga toilet dan yayi wanka, ita kuma tafuce, "Amira ina Mahmud din" "aunty bashi da lafiya ashe" "subuhanallahi muje naga jikin nasa" "aunty yashiga wanka yanzu, kuma yasa nakira mai likita yanzu" "to hakan yayi Allah ya sawwake" 2:30pm jirginsu Ammar ya sauka airport, Jawad yakira a waya, dan yazo yadaukeshi, bayan yazo, yamai sannu da zuwa, yadaukeshi suka wuce gida, Mamy tasa amai girki kala kala, ita dai Zuhura taga anata girke girke, batasan nameye ba, kuma bata tambaya ba, harsuka gama, aikam suna kammala wa tawuce dakinta, dan tayi wanka, tayi sallah, suna zaune a falour su duka, banda Muhsin dake school da Abba daya futa, suka shigo, da sallama, zama saman kujera yayi, yana fadin, "barkanku da gida" "yawwa barka da dawowa" Hajiya tafada, gaishesu yayi suka amsa suka tambayeshi yasu aunty Aisha, yace masu tana lpy lau, ina Muhsin ya tambaya Nadra tace yana school, "su Muhsin an zama manya anfara zuwa University" "ai yaya Ammar yanzu ai yazama babba" "gaskiya dai tunda shine a gidan" "my son kaje kayi wanka nasa angyara maka part dinka kaje idan kayi wanka seka zo nahadama abinci" "tom Mamy" daga haka yashige part dinsa, mamaki ne yakamashi ganin Mamy garau, kuma tacemai ba lafiya, amma ai shi hakan ma yayi masa dad'i dan bayason ganin Mamy cikin damuwa ko yaya, bayan yayi wanka, yashirya cikin farar t-shert da bakin wando, yafuto, dining yawuce, Mamy tazuba mai abinci, yanaci suna hira da Mamy dinsa, tunda tafuto wankan, bayan tayi sallar azahar, bacci yadauketa bata tashiba se 3:40pm, ita kanta tayi mamakin baccin datayi, hakan yasa tamike tayo alwala tayi sallar la'asar tadauko kaya tasa, doguwar riga pink me adon duwatsu, tamata kyau sosai, futowa tayi falour, hango shi tayi a zaune, a falour, tsakiyar su Mamy da Hajiya sunata hira, mamakj tayi dan bataji ana zancen ze dawo ba, karasawa tayi, "ina yini" tafada kanta a sunkuye, sukam su Mamy suka kuramai ido, suga aya ze amsa, "lafiya" abunda yace kawai kenan, batare dayama kalletaba, gurin tabari, dan ita dama indai yana guri bata zama, Mamy ce takalleshi tace "Ammar kuna waya da Ahmad kuwa" "Mamy tun lokacin dakikacd yasaki yarinyar can, dana kirashi be dauka ba, bankara kiransaba kuma shima be kirani ba" "to son kakirashi mana" "Mamy saboda me, shifa baya nemana" "Ammar Ahmad yashiga tarkon mace, sedai katayashi da addu'a" "Hajiya meya faru" "wannan matar daya aura ta gama dashi, dan ko gurin iyayensa ma baya zuwa tajuya mai tunanin gaba daya" "subuhannallahi Allah sarki Allah ya toni asirinta" "ameen matan yanzu ai sam basu da kirki dawuya kasamu tagari" Hajiya tafada "ni shiyasa ma auren yafuta a raina" "ah ah inason kayi aure kuma ka auri yar mutunci wacce muka sonta muka san halinta" shidai bekara magana ba dan harya gaji da magana be cikason yawon surutu ba, mikewa yayi yacemusu zeje ya huta, suka ce mai to, bayan yatafi Hajiya takalli Mamy tace "Khadija banajin yaronnan ze amince" "ah ah Hajiya karki yanke hukunci, sonake idan ya huta se muyi magana dashi" "to Allah yabada sa'a" tana barin gurin kitchen tanufa gurin Jummai, tasameta tana wanke wanke, kujera taja ta zauna, Jummai ce ta kalleta tace "kin tashi ashe" "natashi" "ai dazu Nadra taje ta tashe ki zata fada maki yaya Ammar yadawo, ta tarar kina bacci" "kuma banji shigowar taba, dama yau ze dawo ne" "to waya sani nidai banji ana zancen dawowar sa ba" "to ai shikenan" Ahmad yashigo, bayan yadawo daga masallaci yayi sallar magaruba, tarar da Nafeesa tana ta kai kawo a falour ga wayarta a hannunta alamar wani take kira takasa samunsa, karasowa yayi inda take yace "Honey lafiya kuwa" "wayar Mommy naketa kira tun jiya nakasa samun ta" "toh lafiya