Sashe 4
Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
din motar zugewa akai Ahmad ne manne da wata yarinya yana kissing dinta ya kwantar da kujerar da take kai, ganin haka yasa Ammar juyawa yabar gurin motarsa yanufa yayimata key yabar makarantar gida yanufa yanazuwa yashiga wanka sedaya gama shiryawa tsaf, yunwa yakeji dan haka yashiga kitchen ya hada copee yazauna afalon yana kallo wayarshi ya dauka yayi dialing number mamynshi Zaune take afalo ta mike kafarta anamata tausa wayarta taji tayi kara dauka tayi tana fadin my son ykk lpy lau mamy gobefa nake Shirin dawowa Nigeria to gobe kuma bazaka kara hutawaba ah ah mamy nagaji da kasarnan to shikenan Allah yadawo dakai lpy ammeen yace mamy abba yadawone daga dubai din, be dawoba tukun ok to zankirashi yanzu bayan sungama wayarne ya kira abba, abba ina yini lpy lau Ammar ya karatu kun kammala ko yaushe zaka koma gida eh dama abba sonake gobema nakoma to gobe kuma eh abba to shikenan nasadai akarasa aikin hospital din naka me bi ko sun gama amma zantambayi mamynka to abba ngd Allah yakara arziki ameen ya amsa sukai sallama Ahmad ne yashigo yana fadin abokina ashe kadawo ko kallonshi Ammar beyiba yadai ko patreshia tazone yafada yana dariya au namanta ban gayamakaba tace ta gaji da wulakacinka ta hakura, yafimata sauki to dawasa nake sonake dama kayi magana kasan dai bazata taba rabuwa dakai ba sedai id an Nigeria kakoma to ai gobema zankoma ni, gobe kuma haba kabari se jibi mana, naga da kaine kake tacewa ka matsu ka koma Nigeria yanzu kuma kace se jibi abokina bazaka gane bane akwai yarinyar da mukai ciniki da ita ne kuma gobe 10 na dare zamu hadu wannan kuma kaita shafa nidai gobe zanbi jirgi natafi kai kazauna se jibin taya zanai nazauna ace kuma ina ina kaji dashi yamike yabar falon Babane yashigo yana sallama amsawa sukai su duka karasowa yayi yayinda zuhura ta daukomai tabarma zama yayi yana fadin samun ruwan wanka bazaka fara cin abincinba faradai samun ruwan saboda na gaji sosai yau ogonmu yasamu aiki da yawa mikewa tayi tahadamai ruwan wankar yayi, seda yagama shiryawa sannan ya futo zama yayi ya jawo kwanan abincin ci yafara y,i zuhura ce ta mike tashiga daki tafuta da kayan da sir mansir yabata, baba kaga anbani kyauta a makaranta to kyauta kuma me kikayi baba tambaya yayi shine nabashi amsa shikenan se ya dau wannan kayan yabaki harda kudi wlh baba babu wani abu daga wannan to yayi kudin tabashi tace gashi baba kayi amfani dashi to ngd to jeki kwanta daki tanufa dan tayi bacci bata jima da kwanciyaba tayi bacci baba ne ya kalli inna yace yarinyarnan tanada kokari naga alama kyanta makaranatar masu hali tab lallai malam dawani kudin yace Allah ze kawo to Allah yakawomana ammen yace yana tashi hannu ya wanke yanufu daki inna ma kayan ta ta tattara takai dakin girki Soyayya da izza Story and Writing by hadeexatu (Mrs KD) yar amanar jajirtattu Page 4 Mamy ce sukete shirye shiryen dawowar su Ammar saboda yakirata yace mata karfe 2:00pm na rana zasu sauka dan haka tun karfe 11 suka fara aikace aikace, girki sukai kalala Zuhura ce tafuto daga daki zama tayi kusa da inna yajikin naki dasauki inna ai kan yadena ciwo, tunsafe take fama da ciwon kai hakanne yasa bataje makarantaba, ina baba? yafuta gun aiki tun dazu inna barana watsa ruwa amira daukomun bokiti a bandaki to tace tamike wai ina halifa yana kofar gida yaronnan yakoyi yawo wlh tafada yayinda amira takawo mata bokitin tana fadin yaya zuhura gashi yawwa yar kanwata tashi tayi tanufi bandaki dan tayi wanka amira zoki karbomun mai shogon isah to ta amsa tana futa Babane kwance zazabi yarufeshi yanata nishi ko tashi baya iya yi ogansune ya nufo wurin yana fadin haba malam haruna yazakazo ka kwanta bayan kasan aikinka dakyar yake magana yace wlh jikina ne ba dadi to waye yakejin dadi yanzu inbazaka iyaba sena nemo wani mikewa yayi dakyar yazauna ah ah barana tashi da dai yafi yafada yana yin gaba 2:30pm su Ammar suka iso gida inda dama ankai bala driver yadaukosu, bayan ya saukesune suka shiga falon, da gudu nadra tazo ta rungume Ammar tana fadin oyoyo yaya Ammar jin an anbaci Ammar yasa mamy futowa daga kitchen tana fadin well come my son Ahmad sannunku da dawowa yawwa mamy yagida lpy mamy nayi kewarku sosai nima haka nadra ce tace ya Ahmad oyoyo aini fushi nake dake ni bikimin oyoyoba kika tafi gurin yaya Ammar ko to munbata rungumeshi tayi tanafadin kayi hakuri yaya Ahmad kaifa abokinane kamanta dariya yayi yana daukanta yace to na hakura kiss ta mannamai a kumatu tanafadin yawwa yaya Ahmad, ina muhsin da jawad mamy ce tace muhsin yafuta jawad kuma yana school ok Ahmad ku shiga ku watsa ruwa seku futo nahada muku abinci to suka fada nadra yasauke suna nufar part din Ammar, nadra ce tabisu abaya ke dawo mana karki bisu mamy gurin yaya Ahmad zanifa ai yanzu ze dawo zoki jirashi anan Bayan sunshigane mamy tashiga hadamusu abinci wanka sukai suka futo dining suka nufa dan suci abinci mamy tayimusu abinci kala kala da juice kala kala saving dinsu tayi suka faraci mamy ce tace Ahmad munyi waya da momynka tana abuja eh mamy nasani amma seka huta kaje ko eh se gobe bazaka bari next week ba mamy gobendai ai zandawo to ai shikenan, tunda sukafara maganarsu be samusu bakiba abincinshi kawai yakeci Ammar sekuje tare da Ahmad abuja inba hakaba baze dawoba mamy sena dan huta yabari se jibi mana to Ahmad kaji kabari se jibin ko tom shikenan nadra ce tace yaya ahmad nima zanbika tom shikenan zan tafi dake dagaske gyada mata kai yayi. Seda suka gama cin abincin Ahmad yacewa da Ammar yazo yarakashi gurin wani friend dinsa ba inda zani, ba inda zaka? eh ok tom yanafadin haka yafuce motarshi yadauka ya futa. Ammar kwanciya yayi kanshi na kallon siling da haka har bacci me dadi ya daukeshi Baradai natashi na shirya islamiyya karna makara au makarantar zakije eh inna ai naji sauki to Allah ya kiyaye daki tanufa tashirya tsaf tafito inna nagama to sekin dawo bara najira maryam tazo zamatayi, yaya zuhura ki tsayamu mutafi tare toki sauri ki shirya mutafi yaya zuhura nima zanje wlh bazani dakaiba bazama kakeba sedai ka hanani karatu dan haka ba inda zakaje kazauna a gida. autah na tawonan kaji idan yaya maryam tazo zaka bita, itama taki zuwa amira futo mutafi na biyamata gidansu tom muje inna sukaiwa sallama suka nufi kofa. halifa muje namaka wanka unguwa zamuje inna ba unguwar dazamu je shikenan se za a unguwa ake wanka muje ni suka wuce bandaki Gidan su maryam tanufa sallama tayi aka amsa mata shiga tayi dakin su. umma inayini lpy lau zuhura ya ummanki tana gida umma ina maryam bangantaba maryam sun tafi unguwa bata fada mikiba amma shine bata fadamunba ai dayake batasan harda itaba mikewa tayi tana fadin to umma semun dawo to Allah yabada sa a ammeen ta amsa hanun amira takama suka wuce makarantar Se kusan karfe 5 yatashi yayi wanka yayi sallar la'asar seda yagama shiryawa sannan yafuta falour mamy ce kadai a falourn. mamy ina yini anyini lpy ina Ahmad din yafuta, tundazu ai, ok muhsin ne yashigo sanye da headphone akunnenshi ganin Ammar zaune yasashi saurin cire headphone din karasowa yayi yanafadin yaya Ammar yaushe kadawo, yau sannu da zuwa yawwa ina yaya Ahmad yaje unguwa daga ina kake dama yasan dole se yayimai wannan tambayar yaya dama ball naje to yayi dayawan ai gara aje ball din bara naje nayi wanka azuciyarshi kuma yace to yanzu mun banu tsauri yadawo, wucewa yayi, Ammar ne yakalli mamy yace mamy ya maganar hospital dinane eh munyi magana da abbanku harma angama, kai kawai yake jira yawwa dan wlh nafusan nafara aiki dawuri da canaiwa da abbanku yabudema Ahmad ma tunda kaga komai tare kukeyi to mamy ai zamu iya yi da wananan duka ko da dai shima yabudemai daya fi. to kaga ka girma yanzu ka gama karatu gashi har zaka fara aiki yakamata ka nemo mata kayi aure mamy bayanzuba se dan nan gaba inane gaban bakai yanzuba se gaba kazama tsoho kaki auruwa dan ba budurwar dazata auri tsoho tafada tana dariya kai mamy tsoho kuma habadai kasan me nida zakajema gurin ilham ka daidaita danaji dadi ilham kuma mamy to meyeda ilham din kyakyawa da itah mamy bance tanada aibuba kawaidai ni bayanzu zanyiba, kai tokodai sena kaika amma rukiyane dariya yayi yana mikewa mamy barana dauko wayata nakira Ahmad yayi hakan ne kawai danya kauda zancen.part dinshi yanufa wayarsa yadauka gaban mirror yakira Ahmad waikai yaushe zaka dawone yanzu zan tawo kaffa ka shirgani asibiti zamuje ok ganinan katse wayar yayi yakoma yazauna tunanin maganar mamy yake wai ilham wata yarinya da ita kozanyi auren ma se in auri yarinya Antashi daga islamiyya hanun amira tarike suka nufi hanyar gida tafe suke sunata hira amira nabawa zuhura labarin yan ajinsu tanata dariya . tafiya yake yana gudu dan yasan halin Ammar baya jira hangota yayi tanata dariya, dariya take sosai, wow yafada yana kallonta, saitinsu yayi parking tare da zuge glass yana fadin sannufa bata bashi amsaba, amira ya kalla yace kanwata yayarki bata magana ne? tanayi tafada tana kallon zuhura dake tafiya shikuma yana binsu kadan kadan amota to ai ni takimun magana yan mata ki dan kalleni mana in fada miki wani abu gaskiya kinada kyau saurin kallonshi tayi wow Masha Allah beautiful girl kinga bara na nafito hannun amira taja tafara sauri kokarin futowa yake wayarsa tayi ringing dauka yayi, kaifa nake jira ok ganinan Ammar kabatamun shirina amma duk yacce zanyi sena nemoki akwai kaya bana wasaba ga kyau gaskiya yarinyarnan tayimun kala tace, daga haka yaja motar yatafi