Sashe 51
Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
zaki iya maimaita abunda kika fadamun yanzu" "eh zan iya" Nafeesa tafada, "to munajinki" "Ahmad saurayi nane, kuma muna son junanmu, har ta kai yamun alkawarin ze aurene, yanemi na dinga biyamai bukatarsa, nikuma na amince jin yace ze aureni, muka dinga sharholiyar mu, har ta kai yamun ciki, dana sanar dashi, se yace, sai dai a zubar, haka na yarda muka zubar, akalla dai yasani na zubar da cikinsa har sau uku, dana tunamai maganar aurenmu sai yace baze aureniba, na dinga rokonsa, yace shi baze auri yar iska ba, kuma bayan shine yamai da ni yar iskar" takarashe maganar tana kukan makirci, shikam Ahmad baki yasaki yana mamakin karayar da Nafeesa ta shimfida, "kabani mamaki Ahmad" Mom tafada tana kallonsa, "Daddy wlh ba gaskiya bane duk abunda tafada" "yimun shiru kana nufin kenan karyane bakayi lalata da ita ba, bayan naga hotunan ku" bashi da bakin magana hakan yasa yayi shiru, Daddy ne ya kalli Mommy din Nafeesa yace "yanzy me kukeso ayi" "ni dai kawai yacikawa yarinyata alkawarin daya mata naze aure ta, a daura musu aure" "Daddy nifa sam bazan aure ta ba" "yimun shiru bayan ka lalata masu yarinya" "nifa sam ban lalata musu yarinya ba, yarinyar nan dama a lalace take" "ka rufemun baki, inason sanar dakai yanzu zamu daura muku aure a masallacin cikin gida katafi da ita, tunda kai ka jawa kanka, na dauka dakazo kacemun kanason yarinyar nan Zuhura, nan take na amince, dan na yarda dakai, ashe sam ba haka bane, yanzu ya kake tunani idan yarinyar nan taji abunda ka aikata, yarinya me hankali, da nutsuwa, tabbas mutucinka ze zube a idanunta, bama ita kadai ba harmu, yanzu mutuncinka yazube, a idanunmu, yardar danai maka ta tashi" "ni wlh ban tabajin ina rausayin yarinyar nan daya aura ba se yau, tabbas yarinya ce me hankali" Mommy tafada cike da danasanin tsanar Zuhura da tayi, "yanzu zan fita Masallacin gida, zan bada sadaki a daura musu aure" daga haka Daddy yamike yafuce, shikam Ahmad zuciyarsa kamar tafashe, ga haushin Nafeesa daya cika mai zuciya "kai amma nayi mamakin lamarin nan, yanzu kenan ita Ilham din tana ina" Abba yafada yana kallonsu, "yaya tanacan gidan amma bansani ba ko yanzu ta tafi" Mamy ce takama hannun Ammar tana fadin "kayi hakuri my son duk laifinmu ne damuka matsa ma kayi aure batare damun duba tarbiyar wacce zak aura ba, duk bamuyi tunanin haka daga Ilham ba, tunda yar uwar kace, daga yanzu bazamu kara matsa ma kayi aure ba, ka zabi wacce kake so, bazami kara zaba ma mata ba, kayi hakuri" "ah ah Mamy ba laifinku bane, bakusan hakan zata faru ba" "yanzu dai nizan kiran mahaifinta na sanar dashi komai" "Ammar kabiyoni kawai mu koma London, sekai aikinka acan kaji" "ah ah Aisha kibarmun shi anan" "Mamy kiyi hakuri zan tafi kawai, bansan na zauna anan hankali na baze kwanta ba, inaga zanyi transfer din aikina nakoma can london din" "to meyasa zakai haka" "kinga Khadija kibarshi acan ze fu samun nutsuwa" shima bawai yanason zuwan bane, kawai dai ze tafi ne kodan Zuhura tafuta a zuciyarsa, dan ya tabbata indai yanan kuma ze daga ido yaganta a matsayin matar Ahmad to zuciyarsa zata iya bugawa Zuhura na falour a zaune, tana tunanin har yanzu yaya Ahmad dinta be dawo ba ko kalau, zuciyar tace tace 'to ki kirashi a waya mana' hakan yasa tamike danta dauko wayar tata, taji knocking, hakan yasa tanufi kofar danta bude, Ahmad da Nafeesa tagani, kallonshi tayi, taga kanshi a kasa, hakan yasa tace "yaya Ahmad sannu da zuwa" "yawwa" yafada yana shigewa, Nafeesa takalla tace "sannu" yatsina fuska tayi ta dage bakin glass din dake idonta tace "yawwa sannunki kema" kana tashige ciki tazauna kusa da Ahmad , ita dai Zuhura kallonsu kawai take su duka, seda ta rufe kofar kana itama ta dawo ta zauna, dagowa Ahmad yayi ya kalli Zuhura yace "ina me baki hakuri queen nayi miki laifi ki yafemun" "yaya Ahmad ai baka laifi agurina" kallonta Nafeesa tayi ta tabe baki "wannan sunanta Nafeesa kuma ayanzu matata ce abokiyar zamanki" mamaki ne yacikata, amma sam taki nunamai hakan, sema tace "toh" kallon Nafeesa yayi yace "wannan itace Zuhura matar dana aura kuma nakeso" tsaki taja tace "ni na dauka zanga wata hamshakiyar budurwa wacce ta amsa sunanta mace, se naga wannan figigiyar yarinyar" "ya isheki, koma dai menene tafiye mun ke" "aikin banza kafun dai tasanka nina fara saninka" "dakata dalla" yafada yana daga mata hannu, ita dai Zuhura tayi shiru tana kallonsu, zuciyar ta kamar ta fado kasa, bakin ciki yacika zuciyar ta, se taji tama tsani yaya Ahmad din shi kansa, "bara nadauko wayata acikin daki" tafada tana mikewa, dakallo yabita tabbas yasan zataji haushinsa, tana zuwa dakinta tarufe tafada saman gado tana kuka me tsuma zuciya, kuka take sosai har yakai takasa dakatar dakanta, tabbas tanason yaya Ahmad shiyasa kishinsa yacika mata zuciya