← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 97

Sashe 24

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

SOYAYYA DA IZZA
Story and writing by Hadizatu
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan
asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau
page 24
________________ Abba ne yashigo , ganinsu yayi sun taru a falour, "ah duk kun shirya kenan" wlh mungama dama kai muke jira se Ammar, sannu da zuwa sukai mai su duka, itama Zuhura sannu da zuwa tayimai, amsawa yayi yanacewa, " ya makarantar taki kunje yaudin ne" eh munje gobema zan fara zuwa" to Allah ya taimaka Allah yabada sa'a" ammeen" daga haka ya shige part dinsa , Mamy ce tamike tabishi, Ahmad yamatsa kusa da Zuhura ya rada mata yace, "kinyi kyau sosai my queen" murmushi kawai tayi, Ammar ne yashigo ganinsu yayi duk a falour, Ahmad yakalla dake kusada Zuhura, Ilham ce tace " sannu da zuwa" tafada tana wani juya ido, ko kallonta beyiba , yace ke kawomun coffee, ta san da ita yake , tamike tanufi kitchen, seda tagama tahadamai coffe din ta wuce part dinsa danta kaimai, shikam yana shiga yafada toilet dan ya watsa ruwa, tura kofar tayi tashiga bakowa a falour , bedroom din tawuce nanma bata ga kowaba, coffe din taje gaban mirror ta ajiye, harta juya zata tafi tajuyo muryarsa yana cewa" nabaki umarnin tafiya ne" ah ah naga baka futo bane" to dauko mun coffee din ki kawomun " tom" ta amsa, coffee din tadauka takaimai, karba yayi yana fadin "ke kika zabo kayannan" ah ah" to waya zabo miki" wacce kace takaini" ok yafada yana kara kai coffe din bakinsa a karo na biyu, " karki kara sasu daga yau" kallonshi tayi tace "saboda me" saboda sunmiki kyau dayawa karki kara sasu" tom kawai tace" zan iya tafiya" no sena gama" mikomun lotion dincan" gaban mirror din tanufa ta daukomai, ta mikamai, "zauna kan kujera" ba musu tazauna, amma gaba daya ita ba a nitse take ba, gashi daga shi se tawul a kugunsa, mutsu-mutsu take yi alamar zaman ya isheta, yana kallonta yanuna bemasan tanayi ba, Ilham ce a falour gaba daya hankalinta yaki kwanciya ganin Zuhura tayi part din Ammar, tashi tayi tanufi part din, shan coffee din yake yana kallonta jefi-jefi , kamar ba wanda ake jiraba, itakam tagaji da zama sotake yace mata ta tafi, shi kuma yaki fada, shi kansa besan meyasa bayasan ta tafiba, haka kawai yake jinshi cikin nishadi, Ilham ce tashigo dakin , kallon Zuhura tayi tace "ke meya zaunar dake anan" kame-kame tafara alamar tatsorata, kallonta Ammar yayi , yayi murmushi kana yace, "ni nace ta zauna" ok to tashi kifuta"tom tafada tana mikewa zata tafi" Zuhura yafada , akaron farko daya fadi sunanta , juyowa tayi tace "na'am" karbi wannan cup din kitafi dashi" karba tayi tai maza ta futa, kallon Ammar Ilhmam tayi tana cewa" wai kai meye hadinka da wannan yarinyar" be bata amsaba yaci gaba da shafa lotion din a jikinshi, "kasandai koya naganka da wata mace dole zanji ba dadi amatsayina na matarka" dagowa yayi yana kallonta yace" ke kidena proud da cewar zaki zama matata" ko yanzu zan iya cewa nafasa " dama nasani baka sona ai dauramaka ni akai" kamar kuwa ki sani" Nagode yaya Ammar" ok futar mun daki" baseka koreniba zanfuta" daga haka tafuce shikam ko a jikinshi yaci gaba da shiryawa, bayan yagama shiryawa yafuto ba karamin kyau yayi ba, suma su abba da Mamy duk sun futo, dan haka tafiya sukai, bayan sun isa airport dinne basu fi minti 5 ba jirginsu hajiya ya sauka, farace tas idan kaganta kai kace ba jikokinta bane, Abba ne yatafi gurinta rungumeshi tayi , tana dariya, karasowa sukai, Mamy ma rungumeta tayi tana mata sannu da zuwa, suma sannu da zuwa sukai mata gaba dayansu,zuhura ma kallonta tayi tace"sannu da zuwa" yawwa sannu yarinya" ya hanya" lafiya lau usman ina kuka samu wannan kyakyawar yarinyar" Hajiya muje dai gida, daga haka suka nufi mota " ah ah nifa bazan hau motar dan iyayinnan ba kar inje ya cillar dani a hanya" dariya sukai har shi Ammar din yace" aikam dai kika hau cillar dake zanyi" dariya suka kumayi , kana suka shige mota, bayan sun isa gida Mamy tasa Zuhura takaima Hajiya akawatinta dakinta da aka gyaramata, wanka tayi tafuto , dining suka nufa su duka, saving dinsu Zuhura tayi, Hajiya ganin dambu yasata washe baki tana fadin "kai amma dai Allah yamuku albarka abunda nake sha'awar ci" ai Hajiya nasan kinasan dambu shi yasa nasa amiki" aikam kin kyauta" to sukuma su dan iyayi kuma me zasu ci" ganasunan zata zubanusu" oh wai bazasu ci abincin gargajiya ba waisu turawa" wlh kuwa hajiya " daga haka takammala zubawa kowa, ta wuce zata tafi taji muryar Hajiya nafadin " ke yar nan kizo muci abincin mana" ah ah zanci acan" ah ah zonan tawo kusada ni kizauna kici kema kinji" bayadda ta iya hakan yasa tace to, zama tayi abincin tazuba , kawai dai ci take dan ba a sake takeba, seda suka gama tas, tana gani sun fara tashi itama ta tashi tawuce ciki, Hajiya ce tace , " wai usman ina kuka samo yarinyane gatanan kyakyawa" labarin abunda yafaru yabata tun daga farko har karshe, ta tausaya musu sosai, dahaka tashige dakinta danta huta, Zuhura kam nashiga tafara cewa Inna zata ci abinci, nunamata kular Inna tayi tace taje ta diba, diba tayi takoma gefe tana ci, amira ce takalleta tace" aunty Zuhura kinga jirgi" eh nagani kato makuwa" ba irin nawasan Nadra bane" eh yafi nata girma sosai" haka sukai ta hira harta gama cin abincin tawanke bannunta, dukansu kowa yabar falourn duk sun shige ciki, Abba da Mamy ne kawai a zaune, Abba ne yake waya yana fadin" wato Alhaji Aminu sabida kaji Hajiyar ka ta dawo ka kirani ko"? yi hakuri abokina kasanfa dole nazo naga Hajiya" gaskiya kam to seyaushe zakazo"? yau dinan ma zan zo da daddare" ok to seka zo" daga haka yakashe wayar" wai kaida wa kaketa wayane"? wlh Alhaji Aminu ne yaji Hajiya tadawo yace zezo da daddar
e" to Allah yakawoshi" ameen" futa Ahmad yayi, gurin Nafisa yanufa dan ta dameshi da kira, yana zuwa yayi knocking , budewa tayi, shiga yayi, wasu mata yagani su biyu , ba marabarsu da tsirara kallo su yayi a wulakance sukan suna ganinsa suka fara kissa da kisisina , sedai sun makara dan Ahmad yanzu ya rage maitar mata, yana shiga tabishi, "haba me yasa zakamun haka tun yaushe kace zakazo" nagayamiki ina wani uzuri ne shiyasa ban zoba" ok yanzu kana cikin shiri ko" no baby banjin dadi yanzu" anya ba watace takwace mun kaiba da kaida kafun na nema kanema kusan sau uku" kafadamun kodai yanzu bakajin dadi nane" no baby bahaka bane yanzu banajin dadi ki bari se next time" amma banji dadiba" ok nizan wuce" kai tun yanzu" eh inada abunda zanyi" daga haka yanike , futa yayi , bayan ta rakashi ta dawo, " kai anya ba watace takwace mun shiba" daya daga cikin yan matance tace" kema tun yaushe ake miki kizo murakaki gurin wani boka wlh daba wannan maganar ake ba aida tuni ma kunyi aure" aini sadeey tsoron irin wadannan nakeyi" to shikenan seki tazama kina zaune ganinsama seya gagareki" shikenan zanyi tunani
Chapter 24 · 0% Book details