← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 97

Sashe 30

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

SOYAYYA DA IZZA
Story and writing by Hadizatu
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan
asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau
page 30
________________Bayan yafuto theater, yadawo office dinsa yazauna lokacin har 5:15pm tayi, court dinsa yadauka yasa yadau key din motar sa da wayarsa, yafuce, reception yaje yace ma da norse din yariga yafuta, ko waye yazo kar a nemeshi, amsama tayi cikin girmamawa, daga haka yafuce , yamotarsa yayi wa key ya nufi gida,
bayan ya isa gida yatarar falour ba kowa hakan yasa yawuce part dinsa dan yayi wanka, yana shiga yafada toilet, ruwa yasakarwa kanshi, seda yayi wanka yafuto, kananun kaya yadauka , farar riga da trequater yasa, bayan yagama shiryawa yafada saman bed yakwanta, gaba daya yagaji , jiyay cikinsa na kugi alamar yunwa, wayarsa yadauka yadanna kiran mom dinsa, bayan tadaga yace mata "Mamy nadawo kuma inajin yunwa" "ayyah kaga kuma nafuta bana gayama yau zamuje hado lefe ba" "lefe kuma Mamy lefen wa"? "bansaniba ai auren baya gabanka shiyasa" se lokacin yatuna yace "ok natuna Mamy yanzu dai inajin yunwa" "ok kaje dakin Hajiya Zuhura nacan kasa ta hadama" "wlh Mamy bansan ma futa" "to seka zauna da yunwarka" daga haka takashe wayarta , idonsa ya lumshe, in ya tuna da aurennan komai jagulemai yake, dawannan tunanin yamike yafuta, dakin Hajiya yanufa, Hajiya nata bawa Zuhura labarin yan matakansu dasukayi a da, shigowa yayi bakinshi dauke da sallama, amsawa sukai, bata dago ba takalleshiba , zama yayi kan kujera yana fadin "Hajiya good evening" kallonshi Hajiya tayi ta tabe baki tace "to turawa dan iyayi kadawo" jin ance dan iyayi yasa Zuhura kwashewa da dariyar da batasan sanda tazo mataba, kallonta yayi cikin mamaki, itakam kunshe dariyarta take taki kallonshi, "ke hadamun abinci kikawo mun part dina" daga haka be jira mezata ce ba yafuce, itama tashi tayi tana fadin "Hajiya bara naje nadawo " "to sekin dawo" daga haka tafuce, kitchen tanufa tahadamai abincin kan tire, tawuce part dinsa, tura kofar tayi tashiga ciki, zaune tasameshi kan kujera, karasawa tayi inda yake, ajiyemai tayi kan table din gabansa, be ko kalle taba yaci gaba da canja channel, "ga abincin" be kalle taba ballantana tasa ran ze mata magana, ganin haka yasata juyawa zata fuce, kafun takai kofa yayi maza yasawa kofar key, kallonshi tayi ido cikin ido, alamar tambaya, shima ita yake kallo, komawa yayi ya zauna inda yake, abinci yazuba yafara ci, sakeke tayi tana kallonshi, shikam cin abincin sa yake kamar ba kowa kusa dashi, ganin tsaiwar bazata kai mata ba yasa tamatsa kusa dashi tace "ina son nafuta" ko kallonta beyi ba ballantana ya bata amsa, ganin haka tasake cewa "kabudemun nafuta" be kalle taba yace "wa kike ma dariya dazu"? shiru tayi batare da tace komai ba, abinshi yagama ci kana yadau phone dinsa yana dannawa , ganin tsaiwar bazata kai mata ba yasa tace "dan Allah kayi hakuri wlh bansan sanda dariyar ta kufce mun ba" "uhmmm kinga dariya taja miki kita zama anan se sanda nagaji nabude miki" "dan Allah kayi hakuri wlh akwai abunda zanyi" "bake kin raina mutane ba ko"? yafada yana kwanciya saman kujera, matsawa tayi kusa dashi ta tsugunna tana fadin "dan Allah yaya Ammar kayi hakuri wlh bazan karaba" lumshe idonsa yayi yana jinta amma yamata banza kamar yafara bacci, ganin baze hakura ba yasa ta kifa kanta kan gwuiwar ta tana shashekar kuka, jiyayi kukan nata nataba zuciyarsa, haka kawai yaji zuciyarsa kamar tafashe saboda kukan datakeyi, still idonshi arufe yace "ke kukanki yadameni kuma inasan nayi bacci" hadiye kukanta tayi batare data dago kanta ba, tana haka bacci yakwasheta tuni tafara bacci har tana gyara kwanciya kan carpet, shima baccin yake,
Hajiya nata jiran Zuhura ta dawo, shiru har bacci yadauketa, 6:30 su Mamy suka dawo lokacin Alhaji Aminu na kokarin futa da motarsa, futowa yayi suka gaisa, har Mamy tana tsokanarsa wai ango, daga haka dai yawuce sukuma suka shigo ciki, Ahmad nayin parking , suka futo suka wuce ciki, me gadi da Bala driver sukasa su shigo musu da kayan dasuka siyo, shikuma Ahmad ganin ana kiran sallah yasa yawuce masallaci, Inna ce tashiga neman Zuhura bata gantaba, daki tawuce tanufi toilet tayi alwala, "watakila ma tana dakin Hajiya" Inna tafada tana zura hijab, ta tayar da sallah, bayan sun iso falour , Mamy bedroom tawuce dantai sallah, ita kuma ilham tawuce part din Ammar tana iyayi, knocking tayi, shiru ba'a budeba, bugu takarayi da karfi, a firgice yamike yana salati, tashi yayi yanufi kofar danya bude, yana budewa yaga Ilham tsaye, hade rai yayi yace "ya akai" "bakomai kawai dai dama cazan maka mundawo" "to na ganku" yafada yana shigewa yafada toilet dan yayi alwala ,binshi ciki tayi tana murmushi, turus tayi ta tsaya ganin Zuhura kwance kan carpet tana bacci, "kai yaya Ammar me nake gani haka" tafada lokacin dayake futowa, be kalle taba yafuce dan ya wuce masallaci, wata uwar tsawa Ilham ta daka tana kai ma Zuhura duka, afirgice tamike tana sosa gurin "ke uban me kikeyi a dakin nan iye"? hawaye Zuhura tafara, "ba tambayarki nake ba me kuka yi" "bakomai " "muna fuka kawai zoki futa" dagudu Zuhura tafuce, mamaki ne yacika Ilham tafara tambayar kanta me Zuhura keyi dakin Ammar, ganin bata da amsa yasa tafuce, dakinsu tawuce , tana shiga taga Inna zaune kan sallaya tana lazumi, toilet tawuce, kallonta Inna kawai tayi, seda tafuto Inna takaleta tace "Zuhura ina kika je ne "? "ina dakin Hajiya" tafada tana tada sallah, kallonta Inna kawai tayi ta cigaba da lazimi, bayan sundawo masallaci suka zauna a falour gaba dayansu, Ahmad kam hankalinsa baya gurin, soyake kawai yaga ta inda Zuhura zata
ullo, so yake yaganta, zancen bikin Ammar suka shigayi, Ahmad ne yace "ai Mamy ana gama nashi nima zanyi" "ah dagaske gara ai kuyi, amma ina kasamo yrinyar"? "Mamy ai yar kice" "ya'ta kuma"? "eh Mamy" "wacce yar'tawa kenan"? "Mamy ai zamuyi magana" "ah tom seka zo" Ammar ne kadai yagane wadda yake nufi, tashi Mamy tayi danta hada lunch, kitchen tashiga Inna ta tarar da har ta kusa gamawa , tayata tayi suka karasa suka zuba cin fulas , Zuhura ce tashigo tana fadin "sannunku da aiki" "yawwa Zuhura zoki dauka mukai dining" "tom " tafada tana dauka tafuce, itama Mamy sauran tadauka tafuce, ita kuma Inna tashiga gyara kitchen din, bayan sun ajiye a dining, Mamy tamusu magana suzo suyi lunch, tasowa sukai gaba dayansu, Ahmad ne yakalli Zuhura dake tsaye yamata murmushi, itama murmushin tasakar mai, Ammar na lura dasu, haka kawai yaji zuciyarsa ba da
i, saving dinsu tayi, seda tagama, Mamy takalleta tace "to zauna kici mana kema" "ah ah Mamy bara nasanarwa Hajiya angama abinci" to shikenan" daga haka tawuce, Ahmad ne yace "oh namanta nabar wayata a daki zanje na dauko" busuce komai ba yatashi yawuce , jitai an riko hannunta, tayi saurin juyawa, ganinshi tayi yana sakar mata murmushi, yace "my queen nayi kewarki fa yaudinnan" nima haka" tafada tana sunkuyar da kanta kasa "dagaske my queen" daga mai kai tayi alamar eh "yanzu kenan kema kina sona" murmushi tayi kanta akasa tace "eh" hamdala yafara zubowa yana daga hannunsa sama yana godewa Allah, itakam tuni tadiba da gudu tayi dakin Hajiya, komawa yayi danya cigaba dacin abincinsa, yau jiyake kamar anmai kyautar aljanna, tana shiga dakin Hajiya taganta zaune "Hajiya an kammala abincin dare fa" "oh bansaniba ai, dazu biki dawo ba"? "eh naje nayi wani aikine a dakinmu" "tom shikenan muje" daga haka suka wuce, seda suka kusa zuwa gurin dining din Zuhura tace "am Hajiya bara naje kitchen nadawo" "tom shikenan" daga haka tawuce ita kuma Hajiya tawuce dining, zuba mata abinci Mamy tayi, tazauna tafara ci, Ammar ne yamike yana fadin "se dasafenku" "toh tun yanzu " eh nagaji ne" to Allah yatashemu lafiya" Inna tafada tana kai cokalin abinci bakinta, dakinshi yawuce yana shiga ya wuce bedroom dinsa, saman bed yafada yakwanta, yana tunanin ta, kwana biyun nan besan meke damunshi ba, dahaka bacci yadaukeshi, seda suka gama gaba daya, kowa yatashi yawuce dakinshi, zama Ahmad yayi yana jiran ko ze ganta tafuto, shiru bata futoba, har ya gaji yatashi yashige dakinsa, itakam Zuhura tana gama cin abinci tayi sallar isha takwanta,
Chapter 30 · 0% Book details