← Book details Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 97

Sashe 69

Soyayya Da Izza Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

SOYAYYA DA IZZA
Story and writing by Hadizatu
Mrs (KD)

Ina masu bibiyar books dina
to ina muku albishir da sabon book dina
dana fara rubutawa
me suna YAN BIYU NE ina baku shawara ku bibiye book din nan
dan akwai chakwakwa kiya kala kala zaku nishadantu
zakuma ku wa'azantusosai kudai kawai ku bibiye kafun free page yakare ku biya kan naira
300 kacal ba tsauwalawa
ina alfahari daku
masoyana
kune kwarin gwuiwa ta
i love you so much
my pans
ina godiya da addu'o'in ku
dayacce kuke yabon book dina
duk da shine nafarko, gudiya buhu buhu
nice taku har kullum Hadizatu wacce kukafi sani da (MRS K D) kucika da bibiyata nukuma zanci gaba da nishadantan daku
DOMIN SHIGA GROUP DIN SOYAYYA DA IZZA KA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA
https://chat.whatsapp.com/FPb99RjggTbAcCFg1aFrVx
DUK ME BUKATAR SOYAYYA DA IZZA YA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA
https://whatsapp.com/channel/0029VahPZYb6WaKlZQvivt0J
page 57
_______________________________________________________________________
_____________________________
________________ Bayan Abba yadawo Mamy tasanar dashi Ammar ya amince da auren Zuhura, mamaki ne yacikashi, dan be taba tunanin ze amince ba, hakama Hajiya tayi mamaki dataji ya yarda, dan duk sun dauka baze amince ba,
karfe 10:00am su Abba sun gama shirin tafiya Abuja daurin auren Ilham, har Jawad shima yazo, Abba ne yace ma da Ammar shima ya shirya su tafi, se yace shidai bazejeba, Abba yayi yayi sutafi, yace bayajin zeje, shikuma Abba da biyu yace Ammar din suje, saboda sun yanke shawarar da an daura na Ilham, shima Ammar din a daura nashi, ganin dai bayason zuwa dagasken yasa Abba yakeleshi, yace ai ba dole seyana gurin zasu daura mai aure ba, haka dai su Abba sukai tafiyarsu, shikam part dinsa ma yawuce, ya zauna, yafara kiran Ahmad a waya, yaga ko ze dauka, amma se yaji Nafeesa ta daga wayar, jin muryar mace ma be tsaya tantance wacece ba yakashe wayar
Zuhura yau tana daki tunda tayi breakfast tashige bata futoba, se Nadra cema tace mata su Muhsin sun wuce Abuja, itama Nadra tazauna nan dakin Zuhura, tana game a wayarta, seda 11:30am tayi kana ta tashi tafuto, kitchen tashiga, ta tarar da Jummai na hada kayan dazata dora girkin rana, sannu da aiki tamata, ta amsa, kana ta nemi guri ta zauna,
12:00pm daidai aka daura auren Ilham, ana gamawa Daddy yabada sadaki amarsayinsa na waliyin Ammar ya nemi auren Zuhura gurin Abba, atake a gurin aka daura auren Zuhura da Ammar, Ilham tayi mamaki da aka zo ana fadin an daura auren Ammar kuma wai Zuhura ya aura, da farko taso tasawa kanta damuwa, ganin kuma ba abunda damuwa zata tsinanamata yasa ta manta, tafara shirinta, dan dawuri zasu wuce ita da mijin, Abba ne ya kira Mamy yafada mata andaura auren, tasamu Zuhura tafada mata, saboda kar a shiga hakkin yarinyar, aikam tace to, suna gama waya, takira Inna take fada mata, aikam Inna tayi murna, kuma tayiwa Mamy godiya dan ta tabbatar Mamy nason Zuhura tunda harta iya hadata da danta wanda tafuso, haka ta dinga yimata godiya tare da yimusu addu'ar Allah yabasu zaman lafiya har karshen rayuwar su, su kasance tare, bayan sun gama waya, Mamy tasa akira mata Zuhura, Nadra ce taje ta kirata, aikam ba jimawa tazo, kusa da ita Mamy ta nuna mata tazauna, hakan yasa taje ta zauna, kallon ta Mamy tayi tace "Zuhura kindauke ni matsayin mahaifiyarki" saurin kallon ta Zuhura tayi tace "tabbas Mamy ina kallonki matsayin mahaifiyata ne" "to nagode, na yenke wani hukunci akanki ne, wanda nasan bazaki bujeremunba, saboda keme hankali ce da sanin yakamata kuma kin dauke ni matsayin uwa" kai kawai Zuhuda ta girgiza mata "Zuhura andaura maki aure yau" azabure ta kalli Mamy, tana zaro ido, hanunta Mamy takama tace "wlh Zuhura banajin da
in ganinki a matsayin bazawara, kuma da karancin shekarunki, Zuhura ina kallonki ne matsayin y'ata, kuma ina kaunarki, hakan ne yasa na sa d'ana ya aureki, danshine gatan dazanmiki" "Amma Mamy bekamata ki hada aurena da yaya Jawad ba kodan Yasmeen, hakan ze iya lalata zumuncin dake tsakanin mu" murmushi Mamy tayi, ganin Zuhura bama ta kawo Ammar aka auramata arantaba, "Zuhura nima nasan ai meye daidai bazan taba bawa Jawad aurenki ba, saboda hakan ze iya lalata zumuncin dake tsakaninmu gaba daya" ita dai Zuhura shiru tayi tana tunanin to idan ba yaya Jawad ba wa Mamy ta aura mata, sam bata kawo Ammar arantaba, danko tunaninta ma bezo ba, Mamy ce takatse mata tunanin da cewa "Zuhura yanzu Ammar zaki kalla matsayin mijinki dan dashi aka daura maki aure" gabanta ne yafadi taji tamkar zuciyarta zata fado kasa, tace "ma Mamy yaya Ammar fa" "kwarai kuwa Zuhura Ammar ne mijinki yanzu" "nashiga uku" abunda tafada kenan "Zuhura ki kwantar da hankalinki, nayi magana da Ammar kuma ya amince da auren, Please dan Allah karki sawa kanki damuwa, dan har munyi magana da mahaifiyarki, itama ta bada goyon baya kuma tamaki fatan alheri" ita dai Zuhura yawun bakinta ne ya kafe takasa cewa komai "watakila Ammar ne zabin Allah damuke ta rokamaki kada kice zaki jajaya bakisan me Allah yaboye nan gaba ba, kowa ya yarda da auren to dan Allah Zuhura karki watsamana kasa a ido" girgiza kai Zuhura tayi alamar toh "ok bara naje dan Allah karki sawa kanki damuwa" daga haka tafuce, hannu Zuhura tadora aka tana fadin "nashiga uku na yanzu yazanyi rayuwa da yaya Ammar amatsayin miji, mutumin da ko kallo ban isheshi ba, ta zamanmu zeyiwu a haka, wayyo Allah na yazanyi, gashi bazance masu banasoba, tunda harshi ya amince nikuma sai nace masu banaso idan nayi haka banmusu hallaci ba"
karfe 3:00pm ango yazo yadauki Ilham suka wuce airport, daganan se Paris, tayi kuka sosai, takira wayar Ahmad dan ta rokeshi ko ze zo suyi sallama, amma Nafeesa tadauka, ta ki tabashi, haka dai suka wuce, Mom ma tayi kuka sosai, su Abba ma daganan sukai masu sallama, dan su koma kaduna, Daddy yayi yayi su bari se gobe sukace, saboda aiki, kuma Muhsin na zuwa school ga Jawad tana aiki, haka dai suka wuce, har airport Daddy ya rakasu, bayan yadawo, ya tsaya masallaci gurin malam Liman, yabashi kudi na saukar da akeyiwa Ahmad, dama yakan bashi, sannan idan anyi saukar se ayi sadaka,
tunda sukai magana da Mamy, bata futo ba, sallar magaruba ma acikin dakinta tayi, koda Nadra tazo tana fada mata su Abba sundawo, batace mata komai ba, har ta fuce,
Abba ne yakalli Ammar yace "ango yaushe zaka koma ne" "ango kuma Abba" "ke baki fadamai ba ne" Abba yafada yana kallon Mamy "oh namanta ne banfada mai ba" "Abba wai me" "andaura ma aure yau, tunda dai ka amince to me za'a jira" Hajiya tafada "amma meyasa ba'a tambaye ni ba" "kaga Ammar tunda dai ka amince to me kuma zamu jira" "yaya Ammar kenan yaushe zaka koma ko anan zakuci amarcin" Jawad yafada da sigar tsokana, wata harara balla mai hakan yasa yadena dariyar dayakeyi, "Abba nifa jibi nakeso nakoma, gashi kunzo dauramun aure" dariya Mamy tayi kana tace "kai kazata bar mana ita zakayi anan kai katafi, ai tare zaku tafi" har cikin ransa yaji da
in hakan amma yaki nunawa saboda kar su gane dama yanasonta, hakan tasa yace "no Mamy nifa ba inda zani da ita" "au to maye marabarta da bazawarar indai anan zaka barta" Hajiya tafada tana kallonsa "kaga Ammar bazeyiwu kabarmana matarka anan ba dole katafi da ita" Abba yafada da fada "dole makuwa" "to Abba shikenan se dasafe" daga haka yawuce part dinsa, da kallo kawai suka bishi, se yayi kala da kamar ba'ason ransa ba,
yana shiga dakinsa yazauna saman kujera, yana fadin "alhamdulillah Allah nagode maka, da kabani Zuhura cikin sauki, addu'ar danayi bata fadi kasa banza ba, Allah Nagode ma" gaba daya farin ciki ya cikashi, jiyake kamar yayi ta ihun dadi' haka yakwana cikin farinciki,
dasafe tana tashi tafuto ta nufi kitchen, ta tarar da Jummai tana hada breakfast, gaisheta tayi ta amsa, kallonta Jummai tayi tace "Zuhura kamar baki da lafiya" "kawai dai jikina nakeji ba da
i" "ayyah Allah ya sawwake" ameen tace tanemi kujera ta zauna, Mamy ce tashigo da sallama, amsa mata sukayi su duka, kana suka gaisheta, Abba tafara hadama breakfast dinsa kan tire, "Zuhura" Mamy takira sunanta "na'am Mamy" "yakamata yau kije gurin mamanki, kiyi mata sallama, dannaji yana cewa gobe zaku wuce, saboda aikinsa" "tom Mamy" abunda ta iya fada kenan "anjima sekije ki wuni ki dawo, kifara shirye-shiryen tafiya" bata iya magana ba, har Mamy tagama zata fuce tace "kitashi ki hadama mijinki breakfast kafun yanema" daga haka ta fice, Jummai ce takalli Zuhura tace "Zuhura wai Ammar kika aura" batason lokacin da hawaye suka zubo idonta ba tace "aunty Jummai wlh banson yazanyi ba, kowa tasan halin yaya Ammar mutum ne da bayason mutane, bayason hayaniya, yafuson yayi rayuwa shi kadai, bayason magana, taya za'ayi na zauna dashi dan Allah" takarashe maganar hawaye nakara gangarowa a idanta, "kinga Zuhura karkisa wadannan aranki, kisa aranki zaman aure zakiyi, kuma aljanna kike nema, kisank idan kikayi niyya zaki iya sawya mijinki dakanki" "nifa duk ba wannan ba bazan iya jure zama dashi ba" "kidena fadin haka, kada Mamy taji, zataji ba dad'i, saboda Mamy tanasonki, shiyasa tahadaki da d'anta, kawai kedai kici gaba da addu'a" "inshallah aunty Jummai" "yawwa ko kefa kitashi ki hadamai breakfast kikaimai" mikewa tayi jiki a sanyaye tashiga hadamai, bayan tagama, tafuce tanufi part dinsa, ta jima a bakin kofar fargaba ya hanata shiga, tunda take zuwa part dinsa bata ta
a jin bugun zuciya ba irin na yau, daker ta daure ta tura kofar tashiga, bakowa cikin falourn, hakan yasa ta sunkuya ta ajiye saman centre tables takama hanya zat fuce, futowarsa ce ta dakatar da ita, dantasan tunda yaganta, to seta tsaya tayi serving dinsa, daure yake da tawul a kugunsa, alamar daga wanka yafuto, kunnensa kare da waya, da alama me muhimmancin ce, "ok doctor Johnson ka sanar dasu gobe zan dawo" daga haka yakashe wayar, da turanci yake maganar, fridge yanufa yabude, yadauko ruwa, kana yadawo yazauna kan kujera, ka'idarsa ce kafun yayi breakfast seya fara shan ruwa, sunce yana kara lafiya, su doctors, karasawa tayi inda yake ta tsungunna tace "ina kwana" da hannu yamata alamar ya amsa, saboda ruwan dayake sha, serving dinsa tayi kana ta ajiye mai, batare daya kalleta ba, yadauka yafara ci, sunkuyar dakanta tayi tana wasa da yan yatsunta, kallonta yake ta gefen ido, wanda ko kallonsa kakeyi bazaka taba sanin kallonta yake ba, kadan yaci kan yadau coffee yafara sha, "kinyi breakfast din ne" "ah ah" "ok dauka kici" "ah ah nakoshi" "kince baki breakfast ba kuma nace kici kince kin koshi" "eh banajin yunwa ne" "bansan jayayya ki dauka kifaraci yanzu" "azumi nake" tafada da sauri, dan ita kanta batason lokacin data saki karyar ba, seda yadan jima kana ya mike, yana fadin "kin taba ganin mata tayi azumi mijinta be sani ba" kallonshi tayi tana mamakin shine yayi maganar, "saboda haka kafun nagama shiryawa nafuto kicinye shi yanzu" be jira me zatace ba yashige, yana murmushi, kallon abincin tayi kana tace "nashiga uku haka ze dingamun dure idan ma muntafi can" abinci ta dauka tafara ci, ya jima be fito ba, gashi itakuma tana tsoron karta tafi yazo ya mata fada, kanshin turarensa ne ya doki hancinta, haka yasa ta dago tana kallonsa, sanye yake da shadda milk colour yayi bala'in kyau, izzarsa ta bayyana karara, kafeshi tayi da ido, hakan ne yasa yace "cinye ni zakiyi ne da kike ta kallo na" yafada yana gyara agogon hannunsa, dasauri ta dauke kanta, daga garesa tace "wlh naci ya isheni" tafada a marairai ce, "ok tashi kije" da sauri tamike ta ta hada kayan zata fuce yace "tsaya" tsyawa tayi tare da juyowa tana kallonshi "daga yau idan zakiyi azumi kifara tambayata kafun ki dauka" girgiza mai kai kawai tayi alamar toh, kana tafuce da sauri "kina burgeni Zuhura komai naki a nitse ina sonki" yakarashe maganar yana murmushin shauki,
Chapter 69 · 0% Book details