Sashe 92
Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
min duk abinda nayita maka nayi saboda sonka da kishin ka ne" nasani nadia nima ki yafe min ai kai mutumin kirki ne, matsalarka wannan maryama din kuma tunda an rabu shikenan kowa ya zauna lafiya "yayi murmushi yana sak had'eta da jikinsa ."a ransa kuwa yace idan kinsan wata baki san wata ba ko waye ya aurar min mata wallahi sai ya dawo min daita tunda addini ya bada zabi idan an nemi miji an rasa duk ranar daya dawo za'a bawa matar zabi ." ***** Maryama tana kwance akan gadon hospital kawai sai ganin maryam tayi ta shigo sanye cikin doguwar riga baka wacce aka yiwa stone work da pink stone a gaban rigar da hannun rigar tayi rolling kanta da mayafin abayar tayi kyau sosai ga wani kamshi da tunda ta shigo d'akin ya sauya yayinda khaira ke rungume a kafad'anta sosai tayi mamaki ganinta adaidai lokacin ."wani tsoro da matsanancin firgici maryam taga ya bayyana a kan fuskar maryama yayinda zuciyarta ta shiga bugawa da karfi numfashinta ya soma barazanar d'aukewa cikin sanyin jiki ta yunkura ta zauna tana cigaba da kallonta still fuskarta d'auke da mamakin ganinta ."ta kara taku biyu ta tsaya nesa kad'ai da inda take tana shafa bayan khaira sannan ta motsa bakinta ahankali "maryama sannu ya jikin ?"wani sanyayyen ajiyar zuciya maryama ta sauke a fili sannan tace "Alhamdu lillah da sauki tana k'ara mamaki acikin zuciyarta. "D'akin ya d'auki shiru tamkar babu wasu halitta aciki kowanesu da abinda zuciyarsa take kissa masa bayan kamar minti goma maryam tace "kiyi hakuri da duk abinda ya faru duk da nasan akwai matukar wahala ki iya hakura amman dai kiyi hakuri komai ya wuce na ari bakin gabad'aya 'yan uwana " maryama tace "babu komai dan ni a wajena komai ya wuce ."maryam ta had'iye wani tuttukin bakinciki da zazzafan kishin maryama dake makale cikin ranta ta cigaba da kallonta da kananun idanunta "ance kin rasa cikinki ko ?"maryama tai shiru tana kallonta tana tunanin abinda zata fad'a mata wanda ya jawo suka sak d'aukar wasu minti goma sannan ta bud'e baki zatai magana sai ga likitoci sun shigo su uku suna cewa "good afternoon mrs adam ?!maryam ta d'an matsa kad'an domin basu dama suyi aikinsu dan taga suna kallon maryama wacce ta amsa da "afternoon! excuse us suka fad'a tare da duban inda maryam take tsaye." fita tayi daga d'akin ta tsaya a bakin kofar d'akin tana zance zuci .""we have checked all your scan and checkups is all fine I hope your husband can be here in few minutes ?"ahankali ta gyd'a masu kai alamun "eh!"suka dubata sannan suka fita maryam ta sake shigowa d'akin "ki zauna mana !maryama ta nuna mata kujerar dake ajiye wanda an ajiyesa ne saboda mai kula da mara lafiya " ta girgiza mata kai alamun bata bukata sai dai tayi shiru tana kallonta tana tunani acikin ranta bata ga abinda ta fita wanda yasa yaya adam yake mutuwar sonta ,har ma ya iya rufe idanunshi ya kai yan'uwansa ga hukuma ba.wallahi ita dai a ganinta bata ga shararren kyawau da take dashi ba gashi ita din bakowa ba ,sannna ba diyar kowa ba ,wannan son da yake nuna mata itace tafi cancanta ya nuna wa ba ita ba amman tasan ita kam har abada sai dai ta hangesa daga nesa shiyasa ma tayi tunanin gara ta zubar da maka manta ta rungumi maryama din koda bata so ko hakan zai sa ya tausaya mata ."anya maryam kina ganin wannan mufutace agareki sai kinbi matarsa kafin ki samu shiga a wajensa ?"kyak kwar zuciyarta ta jefeta da wannan tambayar "hakika wannan ba mafuta bace ki tsaya a ra'ayinki dana yan'uwanki kawai gur'batacciyar zuciyarta ta fad'a mata haka ." Maryam bata Jima da dawowa d'akin ba sai ga adamcy ya shigo turus yayi alokcin da kwayar idanunshi ya sauka akanta cikin tsananin tashin hankali yace "what are you doing here ?jiya ma naga sunanki cikin list din wad'an da suka zo me kika zo yi ?menene had'in ki da matata ?ya jera mata wad'an nan tambayoyin ajere ita kuwa tunda ta ganshi ta birkice tasan ta shiga uku a hannunsa "tamabayarki nake "what are you doing here!"tayi shiru tana kallonsa jikinta na rawa wata razananniyar tsawa ya buga mata yana sake tambayarta bakinta na rawa tace "na kawo khaira ne bata jin dadi shine nace na shigo na.." "enough!"ya katseta ta hanyar fad'ar haka nan take ta ji wani irin mummunar fad'uwar gaba ta dirar mata "ki tsaya iya limit dinki bana son shishigi kuma bana son ganinki a kusa da matata domin idan wani abu ya samu matata bazan d'aga miki kafa ba dan banga dalilin da zai sa ki fara bibiyar matata ba tunda ke kanki kinsan cewa muguwa ce kuma macuciya ce"yana gama fad'ar haka yace "leave !"ya nuna mata kofa da yatsan hannunsa yana huci ." Mmn Sudais MAR'ADAMS PAGE 31 "wani murmushi maryam ta sake saki tare da share hawayenta ta d'ago ahankali ta kalli mami dake goge nata hawayen"Ina son d'anki mami ina matukar son shi Ina ma zai soni kamar yadda nake son shi da yaji dadi arayuwarsa domin kuwa zan sadaukar masa da rayuwarta ta hanayr masa biyayya tamkar baiwa sai dai ya nuna ya fi karfi na?"tayi maganar a kasan ranta idanunta na sak cika da kwalla"na rokeki maryam karki sake shi ga harkar adamcy da wacan yarinyar ko babu komai adamcy makiyinki ne kinga matarsa ma makiyiyarki ce"ita dai ce makiyiyata mami sabda mutun d'aya muke hari daita amman shi fa mami"?tai mata tambayr tana kallonta idanunta cike da kwalla "yaya ba makiyi bane a wajena bayan danganta akwai khaira a tsakaninmu duk abinda na aikata nayi saboda shi ne"karki sak bana so dan yanzu baki ji yadda naji araina ba cike da sanyin murya tace "to mami kiyi hakuri in sha allahu bazan sak ba ".tana gama fad'ar haka ta yunkura ta mike ahankali ta d'auki wayarta ta bar d'akin inda mami tabi bayanta da kallo cike da tausayawa"Allah mai yadda yaso sai ya jarabe ka da son abu ya kuma hanaka shi,Allah ka kawo wa maryam mafuta ka bata ikon cinye jarabawa. "bedroom 'dinsu ta shiga tana zubar da hwaye ta haura gado ta tura wayarta a karkashin pillow ta kwanta kusa da khaira ta kamo yatsun hannunta tana kallo tana k'ok'arin danne damuwarta sai dai hawayen dake cikin kwarnin idanunta yaki tsayawa dan haka ta bar gogewa ta bar shi yana tsiyaya akan pillow ."ahankali taji wayarta tana ringin da kamar bazata d'aga ba saboda halin da take ciki sai kuma ta tura hannunta ta lalu'bo wayar tana dubawa sunan aunty shahida ta gani numfashi ta sauke tana goge hawayenta sannan ta mike zaune ta d'aga kiran cikin raunanniyar murya tace "hello aunty Ina yini ?"hello maryam lfy ya kike?"lafiya lau !ta fad'a tana kallon saman d'akin "mami tace ta sak baki damar komawa gidan adamcy amman kin yanke hukuncin bazaki koma ba salim zaki auren?tace "eh aunty !." Aunty shahida ta numafasa kana tace "maryam garaje ba naki bane ki tsaya kiga yadda a sannu zamu tarwatsa rayuwar yarinyar nan , da duk wani munafukin dake zugata"gidan adamcy dake yafi da cewa ba da wann an yar matsiyatan ba . maryam tayi shiru tana sauraronta batare da tace komai ba har ta dasa aya sannan tace "Aunty kuyi hakuri nasan kunyi iyakar kokarinku akaina kuma na gode maku sosai Allah ya bar zumunci amman Ina ganin ya dace zuwa yanzu kowa ya hakura ,ba kuma dan na daina sonshi ba wannan abu ne da bazan ta'ba dainawa ba har karshen numfashina da son shi zan mutu "shikenan zaki je gidan wani da son wani ?"ya zanyi aunty yaya adam yaki ni to the extended ya nuna wa duniya baya sona ba kuma zai soni ba kinga ko darajan khaira bana ci agurinsa kunga kona koma gidansa wahala kawai zan cigaba da sha zan auri salim kawai aunty. Allah yasa hakan shi yafi zama alkhairi arayuwata "ke dai karki yi gaugawa da saurin yanke hukunci tukun nan ki bamu lokaci dan wannan yarinyar sai ta bar gidansa dama aurensa gabad'aya.tana gama fad'ar haka ta katse kiran maryam tayi shiru rike da waya tana juya maganar aunty shahida ." Bayan adamcy ya gama bawa maryama magani ya tashi zai bar d'akin "tai saurin riko hannunsa cikin nata tana murzawa tana kallon cikin kwayar idanunshi da nata idanun dake bukatar a tausaya masu dan tayi missing din jikinsa da komai nashi "menene kuma ya tambayeta yana tsareta da tsumammun idanunshi yana karantar yanayinta dan kallo d'aya zaka mata ka fahimci tana cikin tsananin bukatarsa.ahankali ta sunkuyar da kanta kasa tana motsa bakinta ahankali "zumana na kasa gane kanka ." me yasa kake son rayuwar aurenka ya fita raina? ya kamata ka hakura ka manta komai mu cigaba da zamanmu kamar yadda muka faro ."zare hannunsa yayi cikin nata yace"baki san halina bane that's why maryama". "nasani mana!.ta fad'a batare da ta d'ago ta kallesa ba sannan ta sauko daga kan gadon ta tsaya abayansa jikinta yana gugan nashi "kana da kirki sosai amman baka da saurin yafiya amman kasani banyi laifin komai ba ".alright tunda baki yi laifi ba ki cigaba da tsayawa akan haka "tunda ka aureni na ta'ba maka abinda ya 'bata maka rai ne ?"no amman kin bari gangancinki yasa cikina ya zube" ya fad'a tare da juyowa ahankali ya zuba mata idanunshi "kin d'auka aure suna ne kawai ?ko kin d'auka aure sex ne kawai ?wai a gidan nan ake takaki ake wulakantaki har wacan yarinyar tasa hannunta ajikinki tana k'okarin miki illa amman kika min shiru saboda ko kasheki suka yi baki da asara ." Ta sauke numfashi da ajiyar zuciya atare tana d'ago kanta ta zuba masa shayayyun idanunta "Haka fa aka dinga shirya makirci akan kiyi auren wucin gadi dani ,wannan tsoron naki yasa kika amince kuma kika kasa fad'a min har sai da asiri ya tono ,ki sani acikin horon da zan miki ban miki komai ba domin sex ma da kika ga Ina yi dake all the time sa kaina nayi yanzu kuwa no sex no romance no fellings kinga I only love you understand "ya