Sashe 8
Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
d aga kafafunta duk yadda taso ta d aure karta yi kuka amman sai da hawaye ya zubo mata saboda tasan me zai iya faruwa ,ita kad ai tasan irin fushin da zai iya yi akan wannan matsalar . Jiki a matukar sanyaye ta shigo haraban gidansu idanuwanta akansu baba gali da aunty salma tsaye adaidai kofarsu bata dai san tsayuwar me suke ba, duk da cikin duhu ne amman ta lura idanunsu na kanta . bangaren umma ta wuce kai tsaye ,ai suna ganin shigarta da sauri suka shiga haska haraban gidan suna duba sawun takalman ta,rigerigen kwasan k asar takun suke . maryama ta iske umma a parlour daman tasan anan zata tarar daita zaman jiran shigowarta umma tace aa maryama kin dawo yanzu nake shirin kiranki ashe kina kan hanya ?ya adam din yake da fatan yana lafiya? gabanta ne ke fad u wa har lokacin tace yana lafiya ! ta fad a tana cire hijab din dake sanye ajikinta waayrta ta ajiye a hannun kujera tana kallon wata yar qaramar akwati dake gefen umma yayinda idanun umma ke kanta tana kallonta har ta samu waje ta zauna tana kiran sunan Allah !sannan tace umma wannan akwatin fa ? azu bayan fitarki subai a ta aiko miki dashi har ta dawo kenan ba gobe ko jibi ne dawowarta ba ? gashi nan dai ta dawo ikon Allah kamar jiya ne fa tayi tafiyar ? Ai kwanakin gudu suke da zarar dare yayi gari ya waye Allah dai yasa mu cika da imani ameen!maryama ta fad a tana janyo akwatin tare da budewa tana duba kayan ciki dadduma sallah ta fito dasu guda uku sai Jallabiyiyo guda biyar masu shegn kyau d aya bayan d aya ta dinga nunawa umma . gasky maryama kayan sunyi kyau subai a tayi kokarin ko da yake ai komai tayi miki bata fad i ba kin cancanta Allah dai ya barku tare ya nuna mana aurenku . maryama ta amsa da ameen acikin ranta .gabad aya sukai shiru har na tsawon minti goma kafin ahankali umma ta sake kallon maryama Maryama wai me kuke ciki ne da adam ?maryama ta dafe kanta da hannunta d aya tace wallahi umma ban San me ake ciki ba ko dai akwai matsalar da kike boye min ne dan yanzu ma gabad aya na karanci yanayinki kamar ba lafiya ba ? karki boye min maryama tabbas umma akwai matsala nayi ta kokarin na boye miki domin Ina ganin cewar matsalar zata zo karshe sai dai kwata kwata banga alamu hakan ba . matsala daga adam din ne ? umma ta tamabayeta cikin fad uwar gaba duk da bata da tabbas din daga garesa ne . a daga mahaifiyarsa ne gaskiya umma mahaifiyarsa bata kar beni a matsayin surukarta ba a ranar farko da mukaje ahaf ai nace wallahi sai da nayi wannan tunanin araina. maryama ta dubeta tana sauke numfashi. mman ita kuwa meye illarki data ki karbarki ? umma tayi tamabayr tana duban maryama ban da wata illa umma kuma bata da wata hujja da zata bayar akaina data wuce ni bazawara ce bazata yarda d anta ya auri bazawara ba ahankali maryama tayi wa umma bayanin komai d aya faru aranar da taje gidansu mr ata amamn sai ta boye mata shirin yan uwansa, umma tayi murmushi tace gaskiy bata da wata hujja ban da abunta ai addini bai hanamu auren bazawara ba amman wasu mutane har yanzu da sauran su . wallahi umma na gaji da rayuwar nan gabad aya rayuwata kullum cike take da kalubali kiyi hakuri maryama naji dadi da naji matslar da ake ciki sai mu sa rokon Allah shi aure irin haka a karshe alkhairi yake zama ,abinda nake so dake kiyi hakuri kiyi hakuri ki kara hakuri akan wanda kikeyi hakika dukkan wanda ubangiji yake so shi yake wa jarabawa Allah yayi miki jarabawa Allah ya baki ikon cinye jarabawa abinda zakiyi duk runtsi duk wahala ki taya adam yiwa mahaifiya rsa biyayya sannan ki fad a masa ya kyautata mata domin su rabu lafiya da mahaifiyarsa dan Allah madaukakin sarki yace (wakada rabbuka alla tahbudu illa iyahu abil walidaiya ihsan) iyaye guda biyu a kyautata masu ki tayasa yi mata biyayya kinji maryama ta gyda mata kai kwalla na cika idanunta. hakika maryama alamarin ki akwai tashin hankali,ina jin tausayinki fiyye da tsammaninki kice masa shima yayi hakuri yayi juriya sannan ya kyautatawa mahaifiyarsa maryama bata san lokacin data kama kuka ba tana jin kmaar ta fad awa umma sauran matsalolin da take ciki amamn kukan da take yasa ta kasa magana . Kiyi hakuri maryama komai mai wucewa ne kuma zamu fad a wa Allah shi yace idan muna da wata bukata muzo garesa zai amsa mana . umma addua nake amamn kamar ba addaur nake ba ki cigaba maryama kuma karki gaji khairan sha Allahu tashi kije kiyi sallah ki zo kici abinci kinji babu abinda zai faru sai alkhairi ta mike da kyar tana goge hawayenta ta nufi d akinta umma ta tattara kayan data fito dasu daga cikin akwati ta maidasu ciki ta zuge akwatin ta ajiye tai shiru cike da jimami halin da suka sake tsintar kansu ciki ba maryama da matsalolin ke bibita ba ita kanta ta shiga damuwa matuka. wani abun bakinciki da haushi tana gama cire kayanta sai ga sakon yan uwansa suna sake tuna mata kwanakin d aya saura aiko sai tasa wani sabon kuka tama rasa da me zataji da marin data sha koda ta ba mata jikin da danuwnasu yake ko kuma da fushin da yayi daita ? wurgi tayi da wayar ta shige bayi tana kuka ita kam gara su turu su kasheta , shirin nasu ma tana ganin kamar mr ata yasani dan maganganunsa na yau yayi Kama da yasan wani abu ko kuma yana zargin wani abu akanta ,ita dai Allah yasani bata son ta tozartane wallahi data tona asirin komai amamn kima da mutuncinta dana iyayenta yafi komai a wajenta wanka tayi ta dauro alwala ta fito bayan ta kammala da abinda zatayi wondo da riga na bacci ta saka ta hau gado ta kwanta lamo tana sake karanta sakonsu tana tunanin kiran mr ata ta bashi hakuri. Bangaren mr ata kuwa har yaje gida abinda maryama tayi masa yanata damunsa mamakinta kawai yake ta yadda har ta iya bud e baki ta kirashi da mara mutunci, ai duk son da yake mata baya jin zai d auki wannan rainin daga gareta kuma yaji dadin marin da yayi mata dan kwata kwata bai yi nadama ba kuma zai ganar daita kuskuren ta yadda bazata sake maimaita wa ba dan bai irin su ake wa rashin kunya akwana lafiya ba amman ai kaine ka jawo tai maka rashin kunya dan ba halinta bane zuciyarsa ta fad a masa haka tsaki yaja ya d auki kwalin sigari ya bud e ya zari kara d aya ya kai bakinsa ya kunna yana zuka ahankali yana cikin wannan halin sai ga kiran maryaama ya shigo wayarsa ya daga wayar ya manna a kunne yana zukar sigari batare daya duba mai kiran ba sallam muryar maryama yaji a kunnensa bai amsa ba ya katse kiran ya ajiye wayar yana sake jan tsaki . bayan second biyu wani kiran ya sake shigo ya daga a fusace me zaki ce ma mara mutunci? magiyar yayi hakuri ta dinga masa acikin wayar sake ajiye wayar yayi batare da yace mata komai ba .maryama ta kasa hakuri ta sake kiransa ai yana d aga kiran ya hau zuba masa matseefa muryarta a raunane tace haba mana ka tsaya ka saurareni muyi magana nasan ban kyauta ba amman ni ya kamata na nuna fushina fiyye da yadda kake nuna naka amman ban yi ba ko kana tunanin kai kad ai kake da zuciya a k irjinka . bayan ka wulakantani kuma nazo Ina baka hakuri banda cutar daka so kayi min Allah bai baka sa a ka mayar dani mai ido d aya ba shine kuma zaka fini fushi akan laifin da Kai ne kayi . .okay ko zaki rama marin da nayi miki ne ? saurin katse kiran tayi ta koma ta kwanta akan gado ta cigaba da kuka wayar ya bi da kallo yana mamaki shi zata kashewa waya ? ya fad a a fili yana jan tsaki maryama kukan me zaki zauna kiyi?zuciyarta ta tamabyeta casbaha ta janyo ta fara ja tana karkafa zuciyarta ya allah karka bari soyyyara bawan nan naka yayi galaba akaina kwata kwata bana son na cigaba da sonshi domin kuwa bazan iya jurar ganina cikin damuwa ta soyayya ba ,ya allah d an son nan da nake masa ma ka cire min shi gabad aya na huta ta fad a ta zubar da hawaye. bayan wani lokaci bacci ya d auketa sai dai cike da shaukinsa. shi kuwa yana nan zaune har wani kiran ya shigo wayarsa ya d aga a zuciye yana cewa maryama zaki had u a mummunar bacin raina ,me kuma zaki fad a min? yayi maganar a tunaninsa itace sai dai jin muryar amar yasa ya dafe goshinsa yana furzar da iska mai zafi daga amar yayi shiru kafin daga baya suka gaisa yace ita kuma maryamar me tayi maka haka ? kaga malam kayi abinda yasa ka kira numfashi amar ya sauke yace Ina son mu had u gobe mu tautauna akan matsalar nan data kunno kai . okay zaka iya zuwa gobe karfe tara ka sameni a Delphi muyi abinda zamuyi dan zuwa goma akwai taron da zamuyi okay sai gobe zan zo akan lokaci ,sukai sallama yana ajiye waya kiran emran na shigowa kamar bazai d aga ba dan ya gaji sai kuma ya duba yaga shi ne sai ya d aga yana cewa emran ya akayi? Wallahi lafiya daman na kira naji ya kukayi da yarinyar? da alamun abinda ka fad a gasky ne sai dai na duba gabad aya wayarta babu wata sheida data nuna haka kuma nayi mata duk dabara dan ta fad a min taki kasan yarinyar ce akwai tsoro da zurfin ciki amman zan bari ayi min binciken layinta da duk wasu call da message s din dake shiga da fita ta