Sashe 7
Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
to ki bani kanki a yanzu na sanki ya mace shikenan zan samu natsuwar cewar ba aurena zakiyi da wata manufa ba "gabanta ya fad'i hantar cikinta ya kad'a nan take taji jiri na dibarta ,da kyar ta samu taja baya ta mike tsaye tana tangadi da baya manufar hakan da tayi shine ta samu ta gudu ."ta dan kalli fuskarsa taga babu wani annuri akanta nan kuma dukkanin alamu sun nuna da gaske yake zai iya aikata abinda ya fad'a,take taji hankalinta ya sake tashi matuka yayinda gumi ya shiga tsatsafo mata ganin har ya cire rigar shan iskar dake sanye ajikinsa ya wurga a saman kujera shine abinda ya sake tsoratata ta juya a guje tana ihu azo aceceta ." hankalinta bai sake tashi ba sai data karasa bakin kofa ta ta'ba tajita a kulle gam tayi tayi kofar ta bud'e taki bud'e wa tana cikin wannan halin na tashin hankali taji ya karaso gareta yana kokarin ta'bata tai saurin gocewa ta koma jikin window parlour'n amman babu motsin mutane sai data zagaye parlour'n tass yana biye daita amman bata samu hanyar fita ba "ki tsaya mana ki daina 'bata min loakci idan nayi bashi zai sa na fasa aurenki ba zan aureki ,kanta kawai take girgiza masa tana taresa da hannunta dan maganar ma taki fitowa daga bakinta hankalinta gabad'aya ya gama tashi kallo d'aya zaka mata ka fahimci bata cikin haiyacinta sauran kad'an ta bashi dariya dan bakaramin rikicewa tayi ba ,da gudu tabi wata doguwar hanya da tai tunanin zata fitar daita zuwa kofar waje." bashi da tabbacin kofar a rufe take aiko taga ya biyota a guje wata irin fixge yayi mata ya had'ata da bango ,shi yayi daidai da fasa ihu da tayi wanda bai razana shi ba sai ita kanta datayi kayanta ta razana shi kuwa tsumammun idanunshi har sun canza kala ya matseta da bango yana sauke numfashi yana kokarin had'e bakinsu adaidai lokacin tasa iykar karfinta ta turesa sai dai ko gezo bai yi ba ji tayi ma kamar dutse ta ta'ba ,tana jinsa ya sake matseta ajikinsa "kayi ..kayi hakuri dan giraman Allah karka sadu dani babu aure ,wallahi gara ka bari idan ka aureni kayi duk abinda kake so kayi dani "okay yanzu acikin sharadin farko kin zabi d'aya kenan ?"tai saurin gyad'a masa kai tana haki ." Ya Kai hannunsa yana shafa fuskarta yana kallon face dinta data fara 'batawa da ruwan hawaye "sauran sharadi d'aya ai daman biyu nace zaki zaba." Shiru tayi tana son tuno d'ayan "kar dai har kin manta ?"tai saurin gyad'a masa kai dariya ta bashi amman ya fiske "na baki minti shabiyar ki tuna "inna lillahi "ta shiga furtawa tana maimaitawa yayinda shi kuma ya cigaba da shafa fuskarta can tace "na tuna !"okay ina jinki zan aurena ba da wata manufa fa "are you sure? "tai saurin gyad'a masa kai "kin ta'ba mafarkin mun kasance tare acikin gida d'aya kuma a waje d'aya muna rayuwa kamar haka kafin zuwan wannan lokacin "?kanta ta girgiza masa da sauri "karki min karya mana ."yayi mgnr muryarsa a kasalance yana zagaye pnky lip's dinta da d'an yatsansa "nasan kina mafarkin haka dan a yadda nake kallon wad'an nan shayayyun idanun naki sun dade cikin nitson son adam ".ta sake girgiza masa kai alamun "a'a!numfashi ya fixgo da karfi ya fitar ,kallon fuskarta yake cike da tsananin tausayawa tana da matukar rauni kuma daman yasan sai raunin ta ya jawo anyi mata illa kuma shine dalilin da yasa ya kasa gabatar daita ga yan'uwansa dan a yadda idanunsu ya rufe akan son wacan yarinyar sai sun nuna mata wariya abinda ya guda dai sai da ya faru shi ." Shida zuciyarsa ke cike da tsananin muradin kasancewa daita shine za'a kafa mata sharad'i akansa ,zai ga uban da ya isa ,zai ga ta yadda wannan sharadin zai yi aiki aiko mami ce tace kar ya kusance wallahi sai dai tayi hakuri bare wasu can "maryama na sha mafarkin mun kasance tare acikin gida d'aya kuma a waje d'aya muna rayuwa kamar haka kafin zuwan wannan lokacin" yayi maganar yana sak had'e ta da faffadan k'irjinsa tare da sauke mata numfashinsa a wuyanta,jikinta ya sake d'aukar rawa sosai duk maganar da yake mata bata fahimta komai amman ta'ba mata jiki da yake ji take kamar tasa ihu ko ta bashi wani lafiyayyen mari saboda bakinciki,shi kuwa gabad'aya jinta a jikinsa ya sake rikita masa lissafi da kyar ta aro jarumta ta sanyawa jikinta sannan ta soma magana cikin bacin rai "idan ka gama wulakantani ka sakar min jiki ka maidani gida dare nayi !"tayi maganr hawaye na zubo mata." shiru yayi yana shafa lip's dinta yana tunanin wani wulakanci yayi mata? jikinta kawai ya ta'ba kuma daman ya saba ta'bawa kuma bazai daina ta'bawa ba har zuwa sanda zata dawo karkashinsa yanzu ma so yake ya d'an tsotsa bakinta dan yasan zai yi dadin sha ,dan haka ya sake matso da fuskarsa zai kamo lip's dinta "ban san baka da mutunci ba sai yau ... " "cak ya tsaya ya kasa aiwatar da abinda yayi niyya yana mata wani irin kallo ,ji yayi ma kamar maganar ba daga bakinta ta fito ba amman yasan ita tayi maganar yace "ke ki kalleni da kyau waye bashi da mutunci ?"yayi maganar yana janye jikinsa daga nata dan yaji zafin kalmar ". "waye da wuce Kai wallahi baka da mutunci "ta samu karfin halin fad'a masa haka ne ganin sun samu tazara a tsakaninsu "yanzu ni zaki fad'a wa wannan kalmar ?" ba dole na fad'a maka ba tunda ka nuna min baka da mutu..."ai wani lafiyayyen mari ne ya ratsa mata kwakwalu warta abinda bata saba ji ba arayuwarta jinshi yau kuwa sai ya zame mata wani bakon alamari sai ya zamo duk ta rude ta rasa Ina ma zata saka kumatunta taji sanyi ai ko ta zame kasa ta durkushe , ta dinga shafa kumatunta kamar mai sabon ciwon hakori sai data d'auki minti biyar tana jinyar kumatunta na dama tare da idonta da d'an yatsantsa ya d'an shafa ,ahankali ta iya d'aga kanta sai dai ta hangosa zaune yana fuskantarta sanye da Kaya ajikinsa sa'banin d'azu ,ta girgiza kanta tana son tabbatar wa kanta da gaske abinda ya faru daita kenan ?" ,kumatunta ta cigaba da shafawa dan har yanzu dai tana Jin zafin radadin zafin marin data sha ."to a yaushe ne har yaje ya canza Kaya bata sani ba ?"ina zaki sani kina cikin gigita ."zuciyarta ta bata amsa da haka . mikewa yayi ya nufi kofar fita jiki a sanyaye ta mike ta isa gaban mirrow dake parlour'n ta duba fuskarta a madubi ta ganta kalau babu abinda ya sameta sai dai gefen idanunta yayi ja sai lokacin taga d'an digon hawaye sun cika mata ido suna kokarin fito wa daga kwayar idanunta ahankali ta maida idanunta ta lumshe domin su karasa gangarowa taji sanyi aranta wata uwar ashar ta zuba masa wanda wallahi ta tafi karfin shekara goma batayi ashar ba dan ba dabiar ba ce sai bayan da tayi ta dawo tana nadama duk da ba agabansa tayi ba hawaye ta cigaba da zubarwa sannnan ta tabi yo bayansa tana gunji kuka tare da nadama me yasa zatai masa rashin kunya ?tamabayr da tayiwa kanta kenan ,sai ma tazo tana ganin laifinta da rashin kyautawarta ,a haraban gidan ta iske shi tsaye ya bud'e mata gaban mota yana jiranta kanta a sunkuye ta shiga ta zauna ya maida kofar ya rufe mata ya zagaya ya shiga mazaunin direba ya zauna ya fizge motar da gudu uka suka bar gidan ." Mmn sudais MAR'ADAMS BOOK 4 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 3 Zuciyarsa na matukar zafi yake murza stearing batare daya kalli inda take zaune ba, ahankali ta d an waigo inda yake zaune ta kallesa a tsanake fuskar nan tashi a had e tamkar zaki kwata kwata babu alamun annuri akanta numfashi ta janyo ta sauke da kyar zuciyarta cike da matsanancin tashin hankali,tana son ta bashi hakuri amman tana jin matukar tsoron abinda zai biyo baya dan fushinsa ba kyau shiyasa bata son wannan fushin nashi dan zuciyarta bazata iya d aukar fushinsa ba, kwananki baya da yayi fushi daita ta azbatu matuka. basu zame koina ba sai akan titin unguwarsu yayi parking batare daya kashe motar ba alamun jira yake ta sauka ya k ara gaba. shiru tayi taki sauka tana kallonsa kamar zatayi kuka har acikin zuciyarta bata ji dadin rashin kunyar da tayi masa ba ,a kalla sun d auki kusan minti shabiyar suna zaune shiru acikin mota sanyi ac motar na ratsa masu sansar jikinsu yayinda kamshin turarensa wanda ya gauraye da sanyi dake ratsa cikin motar suka dinga bugar mata da zuciya . zaune kawai take acikin motar tana ko kuwa da numfashinta da zuciyarta tana tunanin hanyar mafi sauki da zata bi wajen bashi hakuri kafin su rabu amman ta rasa, shi kuwa agogon motar ya duba a karo na kusan biyar tare da jan dogon tsaki bai san zaman me take masa acikin motar ba ,jarumtar ta aro ta sanyawa jikinta tare da kwantar da muryarta cike da girmamawa tace yalla ai tun kafin ta kai k arshe taji sautin muryarsa cikin tsananin fushi . Get down ! ya fad a atakaice zuciyarta cike da rud ani da tashin hankali ta kai hannunta ta bud e murfin motar ta fito tana kallonsa shi kuwa ko kallonta bai yi ba gabansa yake kallo yana jiran ta k arasa sauka yaja motar, tana maida murfin motar ta rufe ya soma kokarin yin revise tare da jan motar wani suuuuu taji motar ta d auki hanayr fita titi . Ahankali ta tabi bayan motar da kallo har sai data daina ganinta, two second ta d auka tsaye tana kallon hanyar da ya bi da tsantsar tashin hankali akan fuskarta,sannan ta soma