Sashe 17
Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bari na kira babanka prof lawan ayi tafiyar dashi ko hakan bai yi ba ?"yayi sosai na gode Allah yasa yana k'asar dan gaskiya na kwana biyu rabona dashi ko a waya "ai kuwa yana nan dan mun had'u dashi a bikin diyar senater shehu mr ata yace "okay !"sannan sukai sallama ." Bayan sunyi sallama da baba babba mikewa tsaye yayi ya shige bedroom inshi yana mai manna wayarsa a kunnensa da wani kira ya sake shigowa daga yanda yake magana a wayar zaka fahimci yana cikin farinciki inda yake fad'a ma mb batun aurensa, mb yaji dadi sosai har yace zai zo a tsara yadda bikin zai kasance "."aa mb abar batun biki nan tukun tunda kaga sweetheart ba wai tana son auren nan bane akan bikin nan komai zai iya faruwa ni dai babban burina maryama ta shigo lafiya."hakan ma yayi amman gasky zamuyi biki daga baya "babban biki a wajena mb maryama ta shigo hannuna ,mallakarta da zanyi amatsayin matar aurena wallahi ya fiyye min duk wani biki da zaayi kasan ni ba wai Ina son hayani bane ". mb ya kwashe da wata dariya yana cewa "gsky abokina ka mugun kamuwa da son yarinyar nan "yarinya duk ta susuta maka lissafi haka Allah yasa ta canza mana kai gabad'aya mu sarara da iskancinka " yayi shiru kawai yana sauraronsa yana tunanin tare da lumshe idanunshi "?anya kuwa maryama zata iya canzasa gabad'aya?" "yauwa abokina daman Ina son na maka wata magana dan nasan kai kad'ai ne zaka fad'a aji kuma ayi aiki dashi "mb yayi maganar yana sauke naunauyen numfashi "Ina jinka!"mr ata ya fad'a ba tare daya bud'e idanunshi ba "daman akan maryam ne ."wani dogon tsaki yaja yana furzar da iska mai zafi daga cikin bakinsa "ka tsaya kaji me zance ." "ban san me yasa wani lokacin kake kasa gane bana son ko jin sunanta "amman kuma ai gashi zaka auri mai sunanta ?" "ina daf da canza mata suna bari dai ta shigo hannuna mb yayi murmushi kana ya cigaba da magana "adamcy rigimar duniya "ita sukuwa ce da zata bari ka canza mata suna bayan sunanta mai ma'ana ne ?"kai ma kasani babu macen da zan ajiye a karkashina taki bin dokata da abinda nake so ."let me go to my point ,maryam ke d'aura khaira a shafukan sada zumunta na TikTok da instagram ,a gasky abun bai min dadi ba dan saboda komai ba ,sai saboda bakin mutune ,azahirin gsky banso na fad'a maka ba duk da nasan babu abinda fad'a maka din zai yi saboda rashin damuwar da kake nunawa akan yarinyar ,amman dai at least ya kamata ka duba lamarin khaira ko a yaya aka sameta diyarka wacce bayan ranka zata gajeka kuma baka sani ba ko ita kad'ai ce diyarka a duniya ." adamcy ya ta'be bakinsa yana jin wani iri ajikinsa kafin ahankali ya bud'e tsumammun idanunshi yana kallon saitin shigowa bedroom dinsa yace "wannan ai maganarku ce zaka iya mata mgana ba sai kun sakoni ciki ba " "ai nayi mata magana taki ji ne dana ce ma zan fad'a maka babu kunya maryam tace na fad'a maka ita yanzu ta rigada ta kuna ta zama guguwa babu mai tsaidaita tayi matukar bani mamaki dan sam banyi tunanin haka daga gareta ba "dan Allah adamcy kayi hakuri kasa baki cikin al'amarin yarinyar za'a duba tayi kamara kuma abinda zai baka haushi da takaici wakar da take d'aurawa da yarinayr wai ga yar da ba'a so ta girma ,ga yar da ba'a so tai karfi,yo su barta ko dan Allah. har mb ya kai karshe maganarsa adamcy na zaune yana sauraronsa sai daya dasa aya sannan yace "okay haka ta fad'a?"ai daman ku kuke d'aure mata gindi har kuke mata kallon macen kirki amman ni tun tin tin nasan bata da mutunci amman tunda tace ita guguwa ce ni zan nuna mata ni teku ne kuma mai wanke duk wata kurar guguwar data taso dan ubanta zan nuna mata bata isa ba,yar ma idan naga dama sai na kwace gabad'aya naga ta karyar iskanci ". "no karka rabata da 'yarta ka dai yi magana nasan za'aji maganarka zaka iya kiran mahaifinta yayi mata magana ".kenan ma kana nufin a lalla'bata ?mb yayi shiru dan ya rasa me zai ce "idan dai haka ne ..."kaga bari kawai ma zan kira babanta muyi magana dashi "mb ya katse mr ata ta hanyar fad'ar haka "wannan kuma ya rage naku idan na tashi nawa kai kasan me zan iya yi."yana gama maganarsa yayi hanging call din yana shafa goshinsa karo na farko da yaji wani abu mai kama da damuwa akan khaira,lallai jini ba karya ba ahankali ya dinga juya maganar mb acikin kwakwaluwarsa ita yanzu ta rigada ta kuna ta zama guguwa babu mai tsaidaita ya jima zaune yana tunanin abunyi ba wai bazai iya taka mata burki ba ko d'aukar mataki akanta ba aa zatayi tunanin ko ya fara damuwa da khaira ne idan hakan ta faru kuwa zatayi tunanin wani abu akanshi wanda shi bazai so faruwar hakan ba ?"ai dole adamcy wata rana zaka damu da khaira dan ko yanzu kaji damuwa aranka har aka kira sallar magrib yana zaune yana tunanin khaira ,ahankali ya ajiye wayar a gefan gado ya mike ya shiga bathroom ya d'auro alwala ya fito ya sauya kaya zuwa Jallabiya fara sol ya feshe ilahirin jikinsa da turare sannan ya nufi kofar fita zuwa kasa inda ya iske mami tsaye da alamun itama shirin shiga sallah take yayi mata sallama zashi massalaci ,fuskarta babu yabo babu fallasa tace "a dawo lafiya!". yasa kai ya nufi kofar fita yana takun nan nasa mai matuqar d'aukar hankali kamar baya son taka kasa bayansa tabi da kallo gabad'aya sai taga yanayinsa ya canza daga adamcyn data sani zuwa wani dabam ,bai dawo gidan ba sai da yayi sallah isha'i lokacin daya dawo bai isketa a parlour'n ba tana d'akinta a can ya isketa yace mata ya dawo tace "sannu da dawowa" taja bakinta tayi shiru kusan minti shabiyar yana zaune ba tayi magana ba bare ma ta kalli inda yake ganin tayi masa shiru ya mike ya fito ya nufi samansa har kusan karfe goma adamcy bai ga alamun za'a kawo masa abinci ba ,dan ya tabbatar da za'a bashi ko baza'a bashi ba ya kirata tana d'aga kiran tace "uhm !"yayi shiru yana juya kalmar uhm din da tace "uhm ina jinka?"ta sake maimaitawa runtse idanunshi yayi sannan yace "sweetheart abinci ?"muryarta a dake tace "babu!"shi abincin ne babu !?ya furta ahankali sai dai direct kalmar ta shiga cikin kunneta kafin ya sake cewa wani abu ta katse kiran ,shiru yayi zaune rike da waya yana juya wayar yana mamakin canji daya kara samu daga mahaifiyar dake tsananin son shi yasan duk ya samu sauyin ne akan maryama yasan da zai ce mata ya fasa auren maryama zata ji dadi sosai har ma ta sauko daga dokin fushin data hau sai dai ina bazai iya ba dan ba abu ne mai sauki agaresa ya iya hakura daita ba yana mutuwar son maryama soyayyarta kullum sake karuwa take acikin zuciyarsa ." "wallahil azim da zai iya rabuwa da maryama da zai hanzarta barinta kodan sweetheart dinsa ta samu sukuni da natsuwa amman son maryama ajininsa yake ya zame masa jarabawa arayuwar sa, idan ma yayi ganganci barinta yasan yayi gan ganci da rayuwarsa ne ,bare a yanzu da kullum abun karuwa yake har ma ya had'e masa da tsananin sha'awarta ."waje ya samu akan dogu war kujera ya mike tare da d'aura hannunsa d'aya a saman ruwan cikinsa d'ayan hannun kuwa ya dafe goshinsa dashi ya runtse idanunshi ahankali fuskar maryama ta soma masa gezo wai gata tsaye a gabansa bai tsaya wata wata ba ya kai hannunsa ya fixgota ta fad'o jikinsa ya rungu meta tsam tsam yana sauke ajiyar zuciya duk da ba a zahiri yake jinta ajikinsa ba sai daya ji jijiyarsa ta harba da sauri, a natse yayi kasa da hannunsa ya dafe daidai inda jijiyarsa ke kwance tana wani irin harbawa da sauri sauri ji yayi wai ta sake lafewa ajikinsa ,ya sake rikota sosai yana shinshin wuyanta yana kokarin kamo bakinta da wannan imagination din bacci yayi awon gaba dashi a parlour'n." ****** Washegari tunda ya tashi yayi sallar asuba ya koma bacci bai tashi ba sai around to 12:00 Kai tsaye bayi ya fad'a ya jima yana cud'a jikinsa da sabulu sannan yayi alwala dan har an fara kiran sallar azahar ya fito d'aure da dogon farin towel a ugunsa,ruwan dake igowa ta cikin sumar kansa ya fara gogewa bayan ya gama ya shafa lotion ajikinsa ya shirya cikin wani had'a den yadi dark blue mai matukar kyau da taushi a gaban rigar an rubuta "TAT"kamar sauran manyan kayansa ." kayan ya matseefar kar'bar jikinsa ya d'aura hula a kansa hular daya saka ma ta matukar taimaka wa wajen fito da aihinin kyawunsa ya au tsadadden links ya saka a bakin hannun rigar sanyayyen turarensa red me sanyin amshi ya feshe jikinsa dashi ya sanya takalmi sannan ya kwashi wayoyinsa ya fito bai iske mami a parlour kasa ba dan haka ya nufi d'akinta inda anan ya isketa zaune akan daddumar sallah tana jan casbaha da alamun sallah ta idar ya k'arasa har inda take zaune ya durkusa a gabanta ya kamo hannunta cikin nashi ya sumbata kamar yadda ya saba sannan ya gaisheta "sweetheart kin tashi lafiya ?"ya tambayeta yana kallonta cike da tsananin kulawa." muryarta a sanyaye tace "Alhamdulillah na tashi lafiya ya kai ma ka tashi ?"ya karyar da kanshi gefe alamun lafiya sannan yayi shiru yana kallon yanayinta kwata kwata yanayinta ya nuna masa bata cikin farinciki da walwala ahankali yace "ina mai k'ara neman afuwarki sweetheart kiyi hakuri ki yafe min ki manta komai "numfashi ta sauke da kyar tace "komai ya wuce". yayi kissing din saman hannunta yana mai sake karewa yanayinta kallon sannan yace "na gode sosai sweetheart thank you for suppointing my marriage Allah ya kara miki lafiya da tsawon rai mai albarka ." "kallonsa tayi na second biyu kafin Ahankali tace "ameen "!yace zanje nayi sallah daga nan zan fita sai dai zan d'an jima kafin