← Book details Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 94

Sashe 81

Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

rike shi ta kowani bangare tace "to umma naji kuma in sha allahu zanyi aiki da maganarki na gode sosai Allah ya kara girma tai mata sallama " saboda an tabo Miki abinda baki so shine duk kika wani rikice ya miko mata hannu nsa babu mutsu ta taso tasanya nata cikin nashi "ki kwantar da hankalinki ko baki nemi ba ni bazan iya wannan hakurin dake ba zan kawo kaina dan kina da baiwa da niimar da zai sa dole a bukaceki "kuma asan nima kina jin dadina ko?hannunta d'aya tasa ta rufe fuskarta "maryama are you okay with me ?"ta gyad'a masa Kai "Ina son komai naki hatta kunyar nan Ina so tace "na gode ." ****** tunda maryam ta dawo gidan ta kuma d'aura kwayar idanunta akan adamcy komai nata ya canza tsohon ciwonta ya motsa most especially yadda taga adamcy yake kulawa da maryama yake bata lokacinsa kuma baya shayi ko shakkan nuna mata tsananin son da yake mata nan fa mami ta rasa gane kan diyarta suna zaune a dinne gabad'ayansu suna breakfast maryam ta fito tana yatsuna fuska sakamakon ganin maryama kusa da adamcy zaune yana karyawa mami tace lafiya "?ta karaso da kyar ta zauna kusa daita tace "gani nan dai zazzabi nake Ji cikin tsananin damuwa mami tace "Ina ke miki ciwo ?da kyar ta bude baki ta so ma mgn 'cikin in Ina wl..h.Wlh mami babu ma inda bai min ciwo tai maganar tana kallon adamcy maryama ta dan d'ago ahankali ta saci kallon Inda take zaune taga mijinta take kallo ta dawo da kallonta ga adamcy taga shi kwata kwata ma hankalisa bai kanta ya manne kunnensa da ipod yayinda idanushi ke kallon abincin gabansa hakan ya tabbatar mata da baya ma sauraron abinda take cewa dan hk ta cigaba da kallonta tana shafa saman kafarsa da tafin kafarta a natse ya d'ago ya zuba mata ido yana sakar mata murmushi ya dibi irish ya kai bakinta ,ta d'an saci kallon inda mami take zaune taga hankalinta yana kansu kamar ta girgiza masa kai sai dai taji bazata iya kunyata mijinta ba dan haka a natse ta bud'e baki ya saka mata ." Aikuwa ran mami idan yayi dubu ya gama'baci wani mugun kallo ta dinga jifansu dashi inda shi adamcy ko ajikinsa maryama ce kawai a gabansa idanun mami dake tsaye akansu yasa ta sha jinin jikinta ta masa alamar mami na kallonsu kafad'a nsa ya d'an d'aga yana sakar mata murmushi wanda bai ta'ba yin irinsa ba itama murmushi ta sakar masa tana jin yadda ya tsarke kafafuwanta da nashi byn ya gama ci abincin ya mike itama maryama ta mike cike da kulawa take biyesa dashi suna shiga parlour'n su ya rungumota "zaka makara fa "ko kin mata ni ne mai kamfanin "oh na tuna Kai ne mr ata mai firgita ma'aikata murmushi yayi yana jan kumatunta sannan sukai sallama tare suka dawo har kasa sai data ga fitarsa sannan ta juya ta nufi sama inda maryam tabi bayanta da kallo idanunta cike da kwalla "wasu mata kaga kamar su suke zabawa ma kansu rayuwa mai dadi ."ta k'arasa maganr hawayen dake boye a idanunta suka zubo ." mami ta kamo hannu maryam ta mikar daita suka nufi dakinta ta kwantar daita tana mai kwantar mata da hankali akan abinda ta hango atare daita tace "kowa da irin jarabawar da Allah yake masa ke kuma jarabawarki ta adamcy ce kuma da ina da yadda zanyi adamcy ya soki fiyye da komai maryam da tuni an wuce gurin fatana kada ki sa damuwa a ranki da har zai gane har yanzu kina son shi ,mu godewa Allah da yanzu zuciyarsa ta fara sanyi akan khaira ni adduarta Allah yasa iya rabon zama ne kawai a tsakaninsu da yarinyar nan dan kwata kwata bana son adamcy ya haihu daita domin rashin haihuwar su shi zai sa hankalinsa gabad'aya ya dawo ga Kha ran nan dai mami tayi ta mata nasiha ." ***** Kullum maryama zuba idanu take taga ta inda period dinta zai zo sai dai shiru yau kam tun barin adamcy gida take jin tashin zuciya da zazzabi can kuma sai amai tayi amai har ta galabaita sakamakon bata ci wani abinci kirki ba wanda haka yasa ta dinga jin juya da kyar ta wanke fuskarta ta dafe bango ta fito ta kwanta a katifa tana nishi sama sama bata jima da kwanciya ba wani aman ya taso mata ta tashi da sauri ta shiga bayi wannan karo fa babu abinda ya fito sai uwar kakari ,bayan ta gama kakarin babu abinda ya fito ta yunkura da kyar tana gyara wuyan rigarta ta fito har karfe uku tana kwance tana fama ahankali ta kai hannunta ta dafe goshinta tana jin wayarta tana ringing Amman bata da kuzarin da zata d'auka dan haka tana kallo wayar tayita ringing ta gama sai wajen shida na yamma ta dan ji dama dama har ma ta sauka tai masa girki tana kitchen ya kirata ta daga tana d'agawa yace "a ina kika ajiye waya inata kiranki "kukan shagwaba ta sakar masa tana cewa bani da lfy ne "what ?"ya fad'a cikin tsananin tashin hankali yana tashi daga zaunen da yake a Office dinsa "okay ganin nan ya fad'a yana katse kiran." Karfe takwas ya shigo gidan ya iske mami zaune tare da maryam sama sama ya gaisheta sannan ya nufi samansa biyu biyu ya dinga taka step inda gabad'aya suka bishi da kallo .a kwance ya tarar da maryama lullu'be cikin bargo ya tsaya shiru yana kallonta kafin ahankali ya soma taku zuwa inda take kwance ta tashi zaune tana wasa da yatsun hannunta yayinda muryarta a sanyaye tace "Sannu da dawo wa ,sannu princesse ya jikin ? "da sauki ahankali ta yunkura zata mike tsaye yace "Ina kuma zaki?ta koma ta zauna tana sauke numfashi zanje na kawo maka abinci !" "haba wani abinci zauna ana ta lafiya wake ta wani abinci baki San sai da lafiya zaayi komai ba ta sunkuyar da kanta kasa tana tsuke k'aramin bakinta "ba sai naje na d'auko abincin nacin da kaina ba ya zauna yana fuskantarta tare da kamo yatsun hannunta "yanzu dai lissafo min abubuwan dake damunki tai shiru kamar bazatai magana ba har sai data ji ya matse yatsun hannu nta cikin nashi sannan ta motsa bakinta."Ina jin zuciyata na yawon tashi yace "uhm sannan kuma jikina babu karfi dan yau amai na wuni ina yi ta k'arasa maganr tana d'an karyar da kanta alamun maganar tana mata wahala amman haka ta d'aure ta cigaba da magana"kaina ma na min ciwo sosai" duk da kinki yarda dani amman wad'an nan abubuwan da kika lissafa alamomi ne na masu ciki "kai dai komai ciki! eh mana ciki mana gareki tun yaushe nake fad'a miki amman kin ki yarda ko yanzu kin daina son baby's ne wai ?"ta d'an yi murmushi tace "Ina so!"ta k'arasa maganar tana rufe fuskarta da tafin hannunta cikin tsananin jin kunya ya mike gabad'aya rike da hannunta ya dawo kan kujerar da take zaune yana kallonta bari dai yau na kira likta ta tabbatar mana." Wayarsa ya lalubo ya soma neman likitar data dubata kwanaki "ni da ka bar kiran likitan nan abinda zanji sauki "bai kulata ba kira d'aya ta d'aga sukai magana daga nan ya cigaba da kula wa daita minti talatin sai ga likita ta karaso ta gaishe da mami sannan tayi mata bayanin yalla'bai ne yake son ganinta mami tace "to yana samansa sai dai haka nan taji ta kasa samun natsuwar zuciya babu wani abinda ke damun maryama kamar dai yadda adamcy ya fahimta ciki gareta dan haka bata wani bata magani ba ba sai dai tace za'a kara mata ruwan tunda tana amai sai pain relief "likita babu yadda zaayi kar a k'ara min ruwan nan dan wahalar samun jijiya ake ajikina "karki damu kin san kowa da yadda yake aikinsa sau d'aya in sha allahu zan samu jijiya "tana gama fad'ar haka ta fita da sauri saboda zata dawo ta bar adamcy cikin tsananin farinciki yana sak kamkame maryama ajikinsa "me zan miki dadina wanda zai sakaki farinciki? ni banason komai kawai ka cigaba da sona duk runtsi duk wuya karka rabu dani "ki ajiye wannn a gefe babu rabuwa a tsakaninmu just say anything you want from me bansan yadda zan kwatanta miki irin farinciki da nake ciki ba bari naje na kawo miki abinci kici kafin likita ta dawo ,likita tana sauka kasa mami ta tamabayeta "waye bashi da lafiya ?"kai tsaye tace madam ce bata ji dadi amman ba wani ciwo bane ango ko kishiya zaki samu a matuka firgice mami tace "kina nufin ciki gareta ?"likita da mamaki tace "eh ciki gareta !aiko mami ta soma karanto kalmar "inna lillahi wa inna rajiun "shikenan na shiga uku ni zulai na sake rasa adamcy ." Mmn sudais MAR'ADAMS
Chapter 81 · 0% Book details