← Book details Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 94

Sashe 90

Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

." tana k'okarin fita daga d'akin shi kuma yana k'ok'arin shigowa tayi saurin dawowa cikin d'akin inda ya zubawa maryama idanunshi batare da yace komai ba ,ahankali doctor ta soma masa bayani cikin sanyi murya"cikin ya fita ko?"ya fad'a yana ciza lip's dinsa da karfi tace "kayi hakuri yalla'bai ya fita sai dai fatan Allah ya bada wani rayayye mai albar.."tun kafin ta k'arasa maganarta ya runtse idanunshi da karfi yana sak ciza lip's dinsa ."ahankali ta juya ta fice daga d'akin da kyar ya soma neman number umma bayan ta d'aga da kyar ya iya bud'e bakinsa yayi mata bayani halin da maryama take ciki aiko ta rikice yace ta shirya zai turo azo a d'auketa yana gama fad'ar haka ya jawo kujera gabanta ya zauna tare da riko hannunta cikin nashi ba'a d'auki lokaci ba umma tazo dan haka ta maye gurbin sa shi kuma ya wuce police station dan tun awanni uku da suka gabata yake samun kira ta bangaren dabam dabam acikin yan'uwansa koda ya isa station ya cika makil da yan uwa duk wanda ya bud'e bakinsa acikin yan uwa cewa yake ban da halin adamcy wannan case din ai na gida ne a gida ya dace ayisa ." Har sanda adamcy yazo alhji kabir bai sak d'aga kiran aunty khadija ba dan tana fad'a masa abinda ya faru yace babu ruwansa" nan fa hanka linta ya soma tashi sai dai ta dake taki nuna damu warta. gabad'aya zaune suke a Office din commissione yayinda adamcy ya bala'i had'e rai aka bukaci ya fara magana a natse yayi bayani komai da yayita faruwa yace "gasu nan babu wacce ban kira mijinta acikinsu ba amman suka d'auki maganata banza gashi a yau sun zama sanadin dana rasa gudan jinina "me nayi maku da yasa kuka zabi ku min haka ?kun zubar min da cikina "aunty khadija ta sauke sanyayyen ajiyar zuciya tace "ka dai zubar da abunka "ni yanzu banason Jin komai commissione take us to court" aunty khadija tace "sai me muje mana wake jin tsoron shari'a amar yace " aa aunty khadi kiyi shiru karki sake cewa komai saboda sulhu ake nema. cikin haka alhaji bashir ya shigo customer controller ne na jahar lagos kuma miji ga aunty shahida." cikin haka alhji kabir ya Kira commissioner yace yasa wayar a handsfree ya soma bawa adamcy hakuri yana kuma tabbatar masa shi dai zai d'auki mataki akan matarsa "takama take da matsayinka ni kuma zan nuna mata kafafuna suna da tsawon daya fi na mijinta "ba sai anyi haka ba amar ma ya saka baki yana bashi hakuri sai dai fur adamcy yaki"kun sa fa matsalarsa taurin kai awa mutanen farko inji cewar salim ya waigo inda yake ya watsa masa kallon banza. juyin d'uniya akayi dashi yace wallahi sai anje kotu idan kuwa har sai anje kotu ai babu makawa anan zasu kwana.nan fa hankalin maryam yafi na kowa tashi dan ma salim ya kawo mata khaira ta sha nono ."aka kira baba babba shima yace ai hjy zulai ta kirashi bazai zo bane kuma bazai kira adam ba ai sai daya fad'a masu sukai kunnen uwar shegu da maganarsa suna taimaka da mazajensu to sai suyi amfani da karfin ikon su su fito dasu ". "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun hisham ya furta adaidai lokacin da adamcy ya mike ya fice abunsa yana waya "Aunty khadija ta kalli aunty shahida tai mata rada a kunne"kin wani daga hankalinki ki kwantar da hankalinki bafa zamu kwana anan ba, ni wallahi ko kwana nayi bazan yi takaici ba tunda cikin shegiyar yarinyar nan ya zube ."Kus kus haka sukai ta magana hisham yace "bari na kira momy ko idan tasa baki zai ji aiko itama tace babu ruwanta har karfe goma na dare mami sai faman Kira waya take taji halin da'ake ciki amman babu wani bayani sai ce mata sukai magana ake zuwa anjima za'a sallamesu zabiba kam ta sha kuka har ta gaji idanunta sun kunbura "bakincikin ta wai yau danuwansu wanda yafi kowa so da kaunar su shine ya zama silar kawo yan'uwanta hukuma wannan wacce irin rayuwa ce."? Abu fa kamar wasa dare ya fara hankalin kowa na sak tashi alhji kabir ya sake kiran commissioner sun jima suna waya yace shifa gaskiya kar ya bari matarsa ta kwana a gurin.ya d'aga kafa ne saboda adam danuwan matarsa ne if not shima yasan zai iya amfani da matsayinsa na commissioner wannan haka yake amman dake case din na gida ne dole ayi hakuri ai saboda kai nima na tsaya da yanzu na Kama gabana suna gama waya alhji kabir ya kira adamcy bai wani tsaya bashi hakuri ba yace "kaga kaje ka janye case din"adamcy yace akan wani dalili ne kenan zan janye case ?" "saboda bazan d'auki wulakancin ga matata ba wannan ma ai tozarci ne "aikin banza kawai ni kuma abubuwan da sukai matata ance maka zan d'auka ne ?bari kaji idan zaka zama cikakken namiji a gidanka ka zama idan kuma zaka cigaba da zama lusari ne fine amman ni ba a haifi matar da zan fad'awa magana taki bi ba ko na kafa mata doka taki ba, babu wannan matar matsayi kake takama dashi to bissimillah kayi amfanin dashi ni kuma zan biyo maka ta sama adamcy yana fad'a shima alhj kabir yana fad'a." cikin haka direban mami ya kawota itama tayi kuka kamar me hisham ya sake kiran mumy "dan girman Allah kisa baki mumy a halin yanzu nayi imani ke kad'ai ce zaki masa magana yaji dan girman Allah mumy kinsan halinsa sai ya bari su kwana anan kinga kuma hakan ba daidai bane da kyar aka shawo kanta ta kirasa tana bashi hakuri yayi shiru yana sauroronta har ta dasa aya yace "shikenan mumy sunci darajanki wallahi if not da sai dai mu had'u a kotu tace "aa baza'a yi haka ba yaron kirki allah yayi maka albarka kayi hakuri da yanuwanka Allah kuma ya sake bamu wasu baby's rayayyu masu albarka ka gaishe min da maryama zan kirata zuwa gobe in sha allahu Allah yayiwa rayuwarka albarka yace "ameen! na gode daka mutuntani suna gama wayar ya kira commissioner alokcin hankalin kowa ya kara tashi yan uwa kowa yayi curko curko adare aka sallamosu akace su rubuta undertaking akan bazasu sake shiga lamarinta ba aunty khadija tace bazata rubuta ba sai aunty shahida ce ta rubuta ." maryama dai batasan iya awanni nawa ta kwashe a hospital ba ita dai ta farka karfe d'aya na rana ta ganta kwance a gadon hospital ganinta kwance a dakin hospital yasa ta fashe da wani matsanancin kuka tana kiran sunan Allah cikin haka ta soma jiyo kamshin turarensa da motsin shigowarsa take tayi shiru ta hadiye kukanta.tana ganinsa ta hau rawar jiki ta sunkuyar da kanta kasa tana son ta rokesa sannan ta bashi hakuri amman bakinta ya kasa furta hakan " jikin bango d'akin ya k'arasa ya jingina jikinsa tare da zuba mata tsumammun idanunshi batare da yace komai ba sai dai zuciyarsa ban da tafasa babu abinda take "wato bazata ce masa komai ba ita kuwa duk hankalinta a tashe yake shirunsa ya sake d'aga mata hankali.kusan mintuna talatin yana tsaye yana kallonta sannna ya soma magana na gode sosai maryama ,shiga cikin abinda bai shafeki ba ya janyo min asara na rasa d'ana ko 'yata amman kisani zaki girbi abinda kika min "sai daya mai mata mata haka har sau uku sannan ya fice daga d'akin yana huci ". "Inna lillahi wa inna lillahi rajiun kawai take furta wa tana maimaitawa a fili yayinda take Jin wani irin mugun zafi da ciwo "da gaske ta rasa cikinta? "mike wa tayi zaune ta had'e tafin hannu wanta duka waje d'aya tana kuka "dame zataji da cikinta data rasa ko kuma da fushin daya d'auka daita ?tana cikin wannan halin umma ta shigo d'akin da sauri ta karaso tana cewa "ke kuma daga tashinki sai kuka? "umma .." sai kuka yaci karfinta ta kasa cigaba da magana umma tace "kiyi hakuri Allah zai baki wasu masu albarka."ba rayayye bane shiyasa kuka rasa ta rungu mota tana shafa bayanta tana rarrashinta ." Kullum adamcy zai zo ganinta akalla sau biyu amman babu wata magana dake shiga tsakaninsu kota gaishesa baya amsawa ita kam tarasa mene ne laifinta, ba wani abu tayiwa cikin ba daya d'auki fushi daita ,idan ma sanadi ne ai shine ya janyo ta rasa cikinta , dan haka itama ta fita batunsa ta d'auki fushi dashi ko yazo bata ma kallonsa har sai taga idanun umma ne take sakin fuska idan ta fita kuwa had'e fuska take har ya gaji ya wuce ." adaidai wannan lokacin idan akwai abinda take so be wuce ta samawa kanta mafitar da zata kubuta daga fushinsa ba sai dai babu fuskar da zata samu sausauci ,lumshe idanu tayi da karfi lokaci guda ruwan hawaye dake kwance a tsakiyar idanunta suka fara zubowa cikin tsananin tausayin kaina.tambaya daya ce ke damunta da har yanzu ta kasa samun cikakkiyar amsar da zata gamsar da kanta ,"shin ta ya zai d'aura mata laifi har ya dinga mata barazana da fushinsa ,wallahi sani ne bai yi ba amman fushinsa na raunana zuciyarta .wani kuka ta fashe dashi umma tace "dadina dake raki da son kuka yanzu sabida Allah bazaki hakura da kukan nan haka ba Ifyrki fa itace komai cikin kwana nawa zaki sak samun wani indai ciki ne sai kin gaji dashi ". Maryama ta share hawayenta tana shesheka ita fa umma duk tunaninta saboda tayi barin cikin ne batasan damuwarta ta mijinta bace shiru tayi batare da tace komai ba taci gaba da tsiyayar hawaye ahankali ta gyara kwanciyata tana tunanin had'uwarsu dashi gobe a gida tunanin take sosai most especially maganarsa ta karshe a ranar da abun ya faru "wallahi wallahi kikayi gigi wani abu ya samu cikin nan zan bala'i canza miki maryama zan miki abinda har ki mutu bazaki manta dani ba canzawa kam ta gani sauran abinda zai mata da har ta matu bazata manta ba Anya kuwa zata koma gidan ko dai tabi umma zuwa gida?to a gidan ma nashi ne!ta zabga tagumi tana sauke numfashi ." Mmn sudais MAR'ADAMS
Chapter 90 · 0% Book details