Sashe 37
Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta karkashi tare da sake runtse tsumammun idanunshi dan harbawar da take babu sauki ." ringing din da wayarsa ya sake yi ne ya dawo da Maryama daga fita haiyacinta da tayi na wuncin gadi ,dake wayar tana kusa daita ta waiga inda wayar take tana sauke wani wahalallen numfashi idanunta suka sauka a akan wayar sunan amar ta ga yana yawo a screen din wayar hannunta ta Kai ta dafe goshinta tana sake sauke wani wahalallen numfashi adaidai lokacin daya juyo ya tsura mata idanunshi yna kallonta cikin tsananin sha'awarta har lokacin wannan abar tasa bata kwanta ba tana nan a mike ,tana k'okarin kawar da fuskarta daga kallonsa taga yay mata alamar ta kawo masa wayar"a natse ta jawo wayar da d'ayan hannunta ta yunkura ta mike tsaye ta nufo inda yake kwance da kyar take d'aga kafafunta saka makon idanunshi dake tsaye kyam kanta jiki a sanyaye ta miko masa wayar ya kai hannunsa ya amsa had'e da riko yatsun hannunta ya fixgota aiko nan take ta zubo jikinsa saurin d'auke numfashi sukai atare alokcin da kiran ya katse." bakinsa dake daidai kunnenta yasa ya d'an ciza gefen kunnenta,ahankali ta lumshe idanunta tare d'an zabura zata mike ya sake maidaita jikinsa yana hura mata iskar bakinsa sannan ya danna wayar yabi kiran amar yana cigaba da hura mata zazzafan iskar bakinsa dake tsananin kashe mata sansar jikinta,ajiyar zuciya ta sauke da karfin gaske,lokaci guda kuma zuciyarta na wani irin bugud'en bugu,ringin d'aya amar d'in ya d'aga da k'yar adamcy yace "amar ya'akayi ne ?". yanayin yadda amar yaji muryarsa yaji kmr ya kwashe masa da dariya amman sai ya samu kanshi da danne dariyarsa, yace"adamcy lafiyrka kuwa naji muryarka wani iri ?"babu komai ya akayi ne ?".amar ya toshe bakinsa gudun kar dariya ta kufce masa ya shiga uku dan yasan halin abokinsa mugun rigimamme ne yanzu zai birkice masa "idan ma ba rainin yawo irin nasa ba a hannu yake fa amman wai babu komai yace "to naji babu komai aje a haka duk da nasan ango a hannu yake dan .."amar...!" ya kira sunansa cikin wata irin kasalalliyar murya " Amar yayi murmushi yana shafa sumar kanshi yace "nifa ban gane wa wannan muryar ba "amar fad'a dalilin kiran idan babu dalili na ajiye wayar?"kana jina daman akan batun chemical cement din da za'a shigo dashi ne wannan satin nake son muyi magana akai "Okay Ina jinka!" adamcy ya fad'a yana mikewa zaune tare da maryama ya zaunar daita akan cinyarsa yana kissing din wuyanta. wani iri felling's taji from know where yana bin kowace gaba ajikinta wanda ya haddasawa tsigar jikinta mikewa tsaye tayi kasa da kanta ta kasa had'a idanu dashi ." Ahankali amar ya dinga masa bayani sai dai shi adamcy kwata kwata hankalinsa baya garesa yana ga gashin jikin maryama daya ga suna mikewa ." tafin hannunsa ya kai yana kwanrtawa kafin ahankali ya maida yatsan hannunsa k'irjinta zuwa wuyata yana yawo dashi ,ita dai kmr an dasata zaune akan cinyarsa dan kasa dakatar dashi tai duk da abinda take son yi kenan amar yace "kana jina kuwa ?"adamcy yayi sauri ya fixgo numfashi ya sauke yace "hello ..!hello !! alamun baya jinsa can kuma yace "sorry amar network ba kyau kwata kwata bana ji abinda kace ba ko zaka iya sake maimaita min abinda kace ."? ganin da gaske dai adamcy baya haiyacinsa kuma komai zai fad'a masa alokacin bazai fahimcesa ba yasa shi cewa "bari kawai zan tura maka komai sai kayi min reply kawai "okay !" ya fad'a yana rungume maryama tsam ajikinsa tare da zagayo da hannuwansa saman cikinta cikin kasalalliyar muryarsa yake mata magana acikin kunnenta "my princess karki bari yau ma nayi bacci irin na jiya batare da na samu natsuwa daga gareki ba ". Tana jinsa tayi shiru tana jin yadda zuciyarta ke rawa "zan biki ahankali bazan miki yadda zaki sha wahala ba "a d'an rikice ta d'ago ido suna kallon juna ido cikin ido ,maryama dake zaune akan cinyarsa ji tayi kamar ta sume masa dan ita kanta tana jin kwatan kwacin abinda yake ji sai dai ita kam bazata iya wannan juriyar ba tayi shiru tana kallonsa kamar yadda yake kallonta da idanunshi da suka gama canza kala hakan ne yasa hawaye ke shirin zubo mata ya sake kai bakinsa saitin kunnenta "kul!"karki kuskura wannan hawayen ya zuba dan zai iya canza min lissafi ." da sauri ta share hawayen kumatunta dan tuni sun zubo muryata a sanyaye tace "yallabai dan Allah kayi hak'uri wlhy ina jin tsoro dan nasan muddin kayi mutuwa zanyi "bazaki mutu ba !" "Allah zaka kasheni idan kuma kana son ka kashe ni ne shikenan na ma huta da wannan rayuwa gabad'aya "tayi maganar fuskarta d'auke da tsananin tashin hankali."murmushin gefen baki yayi tsumammun idanunshi na kanta yace"bazan kasheki ba my princess kawai dadi zamu jiyar da juna kamar yadda na sanar miki ahkl zan biki ki kwantar da hankalinki kawai cikakkiyar mace zan maidake "ya fad'a yana kissing din soft lip's dinta kanta ta girgiza masa tana sake share sauran hawayen"kinsa yadda ake murza stearing mota ?"ta kasan idanunta ta d'an saci kallonsa batare data ce masa uffan ba "yadda kika ga ana murza stearing mota ahankali haka zanbi dake cigaba da satar kallonsa take .ahankali ya janye idanunshi akanta sannan ya zaunar daita cike da basarwa kamar bashi ya gama narkewa ba ya tashi ya koma gaban mirror duk uzirinsa yayi ya gama sannan ya matsa ga wardrobe ya ciro kayan da yake buk'atar sakawa . ganin haka yasa maryama ta zame ta kwanta akan katifa ta yadda bazata gansaba dan taga alamun yana shirin sakin towel din da yake d'aure dashi ,baki kawai ya ta'be a ransa yace "duk wannan bashi zai sa na cigaba da d'aga miki kafa ba Allah dai ya kai mu gobe ."anatse ya cigaba da saka kayansa kananan kaya wando da riga army green, ya sake d'aukar kwalbar turare ya feshe jikinsa nan take d'akin ya sake gauraye wa da kamshi turarensa yayi kyau sosai . bayan ya gama ya matso kusada ita ya kai hannunsa kan bombom dinta ya d'an matsa yana cewa "tashi ki min rakani wajen sweetheart." Ahankali ta juyo daga kwanciyar da tayi tana dubansa sai dai fuskarta ta d'an sauya alamun bata ji dadin abinda ya fad'a ba kamar tace wani abu sai kuma ta yunk'ura ta tashi kawai dan bata son ta nuna masa bata son zuwa wajenta yayi tunani wani abu da sauri ,hannunta ya kama ya taimaka mata ta tashi zaune sanan ya fita abinsa hakan yasa ta fahimtar zai jirata a parlour kenan bata 'bata lokaci ba ta bud'e akwatinta da niyyar d'aukar mayafi hannunta yaci karo da after dress shi ta d'auka ta d'aura a saman kayanta sannan ta nad'a vail d'in rigar, fes ta fito kamar ka saceta ka gudu abinka.." Tunda ta fito ya zuba mata tsumammun idanun shi yana kallonta ko kiftawa ba yayi shi kansa yasan mugun maye ne akanta duk basarwarsa duk ajinsa tattare da miskilincinsa basa wani tasiri akanta, haka ne yasa take d'auka jikinta yake so ba ita ba , tana gama k'arasowa garesa ya mik'e tsaye yaso ya rungumeta sai dai sanin abinda zai biyo baya ne yasa yayi gaba. a natse ta biyosa abaya tana jin wani irin mummunar fad'uwa gaba da tashin hankali mara misaltuwa shi kuwa ko ajikinsa alamun ya nuna ma hanka linsa a kwance yake dan yadda yake taka steps d'in zai fahimtar da Kai babu wata damuwa atattare dashi, komai nashi a natse yake hatta yadda yake taka step dole ne ya birgeka, duk takunsa idanunta na kai yayinda itama take binsa a hankali,babu kowa a falon, dan haka suka nufi bangaren mami a parlour'nta na biyu suka iskesu gabad'aya har hajiya zulfa'u da ya'yan mami ya sha mamaki ganisu kenan a gidan ma suka shi kam ya rasa me suka d'auki mazajensu ?.shi kam duk mutuwar da zai yi akan mace bazai ta'ba bata wannan damar ba " Ahankali maryama ta rage takun da take ta koma tana tafiya kamar wacce bata da laka ajikinta ."Tana kallonsa har ya k'arasa kusa da mami yana kokarin zama ne idanunshi ya sauka akanta kallon second biyu yayi mata yasa ta karaso inda taga an sakar mata fuska wato kusa da hajiya zulfa'u ta raku'be kamar zata shige jikinta tana gaisheta cike da sakin fuska hajiya zulfa'u ta kamo hannun maryama cikin nata ta damke tace "lafiya kalau maryama ya kika tashi ya kuma bakunta ?"maryama kam shiru tayi ta kasa amsa mata saboda abu biyu ne suka had'e mata waje d'aya tsananin tsoro da kuma matsanancin kunya ."zabiba ma fuska a sake take dubanta tana jin lokacin da kannensa suka gaishesa ya amsa masu muryarsa a dake babu alamun wasa sannan ya gaishe da mahaifiyarsa inda ta amsa masa taja bakinta tayi shiru,dalilin da yasa maryama ta d'an d'ago a natse ta saci kallon fuskarta ,"inna lillahi wa inna ilaihi rajiun "wannan shine karo na biyu data sanyata acikin kwayar idanunta yau din ma fuskarta kamar ranar farko data fara ganinta ce fuska babu yabo babu fallasa bare ayi tunanin annuri yayinda idanun yan'uwansa mutun uku ke kanta sun zuba mata ido wanda babu komai acikinsu sai zallar gargadi hakan ne yasa jikinta ya kama bari ." Adamcy ya gaishe da hajiya zulfa'u fuskarta cike da matsanancin farinciki ta amsa, bai kalli inda su aunty khadija suke ba bare su samu darajar gaisuwa daga garesa ,hakan kuwa ya bakantawa mami rai dan ta tsini wannan rainin da yayi masu ahankali maryama ta maida idanunta akan mami dake hankince cikin shiga ta kamala tana motsa bakinta taji sun kama rawa har hakoranta bata san ya'akayi taji magana ta d'auke mata ba ta d'an saci kallon adamcy ,da kwayar idanunshi yayi mata alamar ta gaishe daita ."ta sake aro jarumta ta sanyawa jikinta tace "Ina kwana !". ta k'arasa maganar jikinta na wani irin kyarma mami da duk wad'an da suke zaune a parlour'n sunji amman ta share duk da tasan ita aka gaisar adamcy ya kai hannunsa ya kamo na mami cikin nashi tare da yin kasa da muryarsa "sweetheart maryama na gaisheki "ta rike gaisuwarta