← Book details Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 94

Sashe 84

Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 2 min read

fuskarta ya kai hannunsa kan nata yana shafawa yana k'ok'ari kamo lip's dinta haka suka kasance makale cikin tsananin son juna ." ****** zaune sadam yake a office d'in jakadanci ta kasar amerca Kusan awa d'aya kenan daya kifa kanshi asaman table ya tsunduma duniyar tunanin duk yadda yaso ya manta da rayuwarsa ta baya, ya sake shinfid'a ma kanshi wata sabuwar rayuwar.abun ya cutura da zarar ya runtsa idanunshi ummansa da maryama yake gani "hakika bai kyautawa mahai fiyarsa ba kuma bai kyautawa maryama ba me ma yasa zai yi haka ?"ahankali ya d'ago kan shi tare da mik'ewa tsaye ya rungume hannuwanshi duka a baya yana sauke numfashi cike da jimami cikin ranshi yake fad'in"kasan yarinyar nan mareniya ce bata da kowa sai mahaifiyarta haka zalika ummanka duk duniya bata da kowa sai Kai iyayenta duk sun mutu lallai idan baka koma zuwa ga mahaifiyarka ka nemi yafiyarta ba hakika zuciyarka baza ta'ba samun sukuni ba haka ma hakin maryama bazai barka kasamu kwanciyar hankali ba ,kuma hakan zai sa ka kamu da cutar depression har abun ya fara zame maka menta problem a yanzu tausayin kanshi yake ji dan wallahi yasan zuciyarsa ta kamu da matsananciyar soyayyar maryama a gaske a she dausarar kanshi yayi tayi kamar ma kar ya auri nadia shikenan yaji komai ya sauya agaresa dan haka ma yake son ya soma kar'bar allurar mantau ta yadda zai manta da son da yake ma maryama yayi tunanin ta yadda ya fuskancinci ummansa lallai ya kamata ya ajiye komai ya koma gida ga mahaifiyarsa ."kana ganin a soyayyar da kake wa maryama yanzu akwai wata allura ko maganin da za kai amfani dashi yasa ka manta daita ?"kwakwaluwarsa ta aiko masa da wannan tambayar ."bango ya kai wa naushi batare daya san ya aikata hakan ba radadin azabar da yaji ne yasa har ya fahimci abinda yayi ya yarfar da hannunsa yana runtse ido "ina sonta wallahi ina sonta wannna shine kawai abinda yake maimaitawa." Mmn Sudais MAR'ADAMS
Chapter 84 · 0% Book details