Sashe 85
Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
BOOK 4 AYSHA A BAGUDO WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Page 28 kwance sadam yake akan doguwar kujera mai zaman mutun uku a parlour'n gidansa sanye cikin doguwar rigar jallabiya maron colour yana kallon hotunan maryama yana zurfafa tunanin abubuwan da suka faru a tsakaninsu daita,irin soyayyar data fara nuna masa kafin yayi mata butulci ,hawaye ne ya dinga zuba daga cikin kwarnin idanunsa saka makon ummansa da zuciyarsa ta hasko masa ,mace jaruma mai hkr da tsananin tausayinsa da kaunarsa ya gujeta saboda gudun rayuwa da maryama yau gashi mrayama tana tare da iyayenta shi kuma yana tare da wata ,yayi imani idan itace bazata ta'ba gudu ta bar ahlinta saboda an bata mijin da bata so ba tunda ya gani a zahiri tun bata son shi ta hakura ta dawo tana son shi."to ai shima yana ji aransa bada son ran shi komai ya faru ba shima tsintar kanshi yayi acikin rayuwar da yake, yanzu ne yake nadamar abinda ya aikata sosai yayi zurfi cikin tunanin bai kula ba sai jiyo sautin muryar nadia yayi daga saman step"ashe kana nan ?."wata irin zabura yayi ya mike tsaye har wayarsa tai tsalle akan kujera sai dai bai damu ba ya tsaya yana kallonta yana sauke numfashi muryarsa a tsarke yace "eh ..Ina nan !Ina tura wani sakoni ne, ya k'arasa maganr yana kallon agogon bangon dake manne da parlour'n lokaci ya tafi sosai lallai ya d'auki lokaci mai tsawo cikin tunani mai tarin yawa ,ahankali ta cigaba da kallonsa fuskarta d'auke da tsananin damuwa domin duk abinda yake ta dade tsaye tana kallonsa kusan mintuna talatin ta d'auka tsaye tana kallonsa yana kallon hotunan maryama yarinyar da take jin duk duniya bata da makiyiya kamarta yarinyar data so tayi wasa da rayuwarta taimakon mahaifiyarta ya taimaketa ta cigaba da rayuwa da muradin ranta,ahankali ya waigo ya dubeta domin yasan tana nan ta tsareshi da idanu ilai kuwa hakan ce ta kasance gabansa ne yayi mummunar fad'uwa ganin yadda launin idanunta da yanayinta ya sauya duk sai hankalinsa ya sake tashi Allah yasa bata ga abinda yake yi ba ." "Sadam Kai macuci ne kuma mayaudari tunda ka dawo daga aiki nake faman tambayarka ka fad'a min damuwarka amman sai ka min karya akan tunanin ummanka ne ashe tunanin wannan banzar yar iskar yarinyar kake "wai shin ko ka manta kai din yanzu amatsayin matacce kake ?"."kowa ya rigada ya tsaida zuciyarsa akan cewar ka mutu you're nor more exit in this life ka mutu acikin zukatansu "sadam ya kasa tsayuwa saboda tsananin fad'uwar gaba sai dai ya cigaba da dubanta cikin tsananin tashin hankali mai tarin yawa "nasan da haka nadia amman Ina ganin lokaci yayi da zan goge wannan tunanin a zuciyar mahaifiyata da yan..."dakata sadam bafa zai yuwu ba ,yadda ka kashe kanka da kanka haka zaka hakura mu cigaba da rayuwa,yaran da zamu haifa su maye maka gurbin yan'uwanka"hawayen dake zuba a idanunshi bai sa ta tausaya masa ba. ta k'ara taku ta karaso inda yake zaune tana wani irin huci da zufa "ni zaka wa haka ko?ni zaka d'aga wa hankali ko ?"me yasa kasan kana son maryama ka dawo gareni "?ahankali ya mike tsaye yana cigaba da kallonta gabansa na cigaba da fad'uwa "me yasa ka gudu ka barta alhalin kasan kana sonta "? okay shiyasa nake ta binka ka saketa kaki sakinta saboda kasan akwai mugun nufi acikin zuciyarka ?"to Ina son ayanzu ka saketa kuma saki uku kanshi ya soma girgiza mata alamun bazai iya ba aiko ta damki wuya nsa tana wani irin huci "wallahi baka isa ba sai ka saketa bazai yuwu ka maidani sakariya shakatafi ba ko dan kaga Ina sonka?"to wallahi ka rubuta ka ajiye muddin kayi yunkurin had'ata dani sai nayi maka kisan gaske dan bazan barka a raye kayi rayuwar jin dadi da wata ba, yadda kake son ka hargitsa min lissafi kai ma haka zanyi da kai"tana magana tana sak matse masa wuya wanda hakan yayi sanadiyyar data rusa komai acikin zuciyarsa nan take tsananin tsoronta da yake ji ya kau acikin zuciya dama gangar jikinsa "yadda jikinta yake rawa abun sai ya bawa mai karatu tsoro d'aura hannunsa yayi akan nata yana k'ok'arin cirewa ta sake shake masa wuya lallai ya tabbatar da zata iya aikasa lahira ". "da gaske zaki kasheni nadiya ?idanunta da suka yo waje ta zaro tana dubansa "meye amfanin mayaudari irin ka sai na kasheka na kashe banza tunda daman kai din amatsayin matace kake mara amfani "ta k'a rasa maganr tana sake shake masa wuya "sakar min wuya ina d'aga miki kafa ne saboda cikin jikinki "daga yau idan ka sake d'aga min kafa Allah ya tsine maka albarka d'an iska mara mutunci mara tausayi wallahi baka isa ka min iskanci da kayi wa waccan yarinyar na barka lafiya ba sai duk mu taru mu rasa da kyar ya samu ya janye hannunta yana sauke numfashi yana kallonta itama kallonsa take cike da matsanancin tashin hankali ."a zahirin gaskiya bai san ya cuci kansa ba sai ayanzu bai san jahila mara ilimi ya guji uwa da yan'uwansa akanta ba sai a yanzu muryarsa a raunane yace "nadia nayi dana sanin saninki arayuwata kuma nayi dana sanin d'aukar shawarrinki kinsan na aikata abubuwa tamkar mara ilimi domin kuwa duk wani mai ilimi bazai biye miki ba ." "kinsa na aikata wa kaina mummunar tabo amman babu komai nayi nadama kuma in sha all ahu zan koma ga mahaifiyata kuma zan roketa gafara maryama kuma daman tana nan amatsa yin matata bazan ta'ba sakinta ba kije kiyi duk abinda zakiyi "wallahi baka isa ba! ya girgiza Kai yace wallahi ba da wasa nake miki ba zan koma kasata nigeria kuma zan yi rayuwa da maryama idan kin so ki cigaba da zama dani idan kuma kinji bazaki iya ba bazan takura miki ba,idanunsa sukai jawur hankalinsa a wani bahangonce, shine dalilin da yasa ta tabbatar da ainihin abinda ya fad'a din da gaske yake amman kuma me yasa aikinta zai karye haka da sauri bayan ance mata har karshen rayuwarsu bazai so ya koma ga ahlinsa ba sai gashi tun baaje koina ba komai yana son lalace mata koma tace ya lalace ." ta rushe masa da wani kuka mai tsuma zuciya sai dai ko ajikin sadam kafin yanzu sadam idan yaji sautin kukanta haka sai hankalinsa yayi mugu mugun tashi har sai ya ninka nata tashi amman yanzu ko ajikinsa"ya taka ahankali ya d'auki wayarsa ya juya zai hau step sai kuma ya tsaya tare da juyowa yana kallonta"kibi ahankali nadiya idan kika matsa wallahi aurenki ne zai kare kuma gabad'aya ta zaro masa ido yace "yes haka nake nufi zan iya barinki kuma har cikin jikinki ki rike kayanki na bar miki yana gama fad'ar haka ya cigaba da taku cikin fushi ya shiga d'aki yana jan tsaki ."shi ma rasa ya'akayi yake biye mata yake tana aikata abubuwa ahlin ita tana tare da yan'uwanta amman shi ta raba masa hankali ya jefe kanshi cikin mummunar tashin hankali."nadia fa yau iya tashin hankali ta shiga gaba d'aya ta kasa gane karshen maganarsa tashin hankali ne kawai ke dawainiya daita ."hankalinta ya rabu gida biyu tarin tunani dalilin afkuwar wannna barnar take ,da sauri ta haye sama ta kutsa cikin d'akin baccinsu inda ta iske shi kwance yana kallon saman d'akin ta d'auki wayarta ta sauko zuwa kasa ta shige kitchen number mahaifiyata ta soma nema sai dai number na shiga ba'a d'agawa dan ita gabad'aya tashin hankalin da take ciki yasa ta manta acikin tsakiyar dare suke .zariya ta dinga yi acikin kitchen din kunneta manne da waya ."ganin mahaifiyarta bata d'auki wayar ba ta kira yayarta itama the same thing ta sauke wayar tana share hawaye "ya Allah karka sa na rasa sadam wallahi ina son shi kuma kasan saboda tsananin son da nake masa ne na aikata duk abinda na aikata ."D'akin ta dawo ta zauna akan kujerar sofa tana dubansa kwance ya tsarke kafafuwansa waje d'aya yana jijigawa yana cigaba da kallon saman d'akin ." Idan har bai manta ba yasan yana sonta kuma har sunyi alkwarin aure alokcin ummansa bata shigo masa da maganar maryama ba bayan ta shigo masa da batun auren maryama yaji tashin hankali saboda alkwarin da yayi mata sai dai yaji bazai kin bin umarninta ba dan haka ya sheidawa nadia gaskiya kuma ya bata hakuri nan hankalinta ya tashi tace ita sam bata san da haka ba ."sai kuma daga baya yaji komai ya sauya masa har yake Jin zai iya komai akanta da yaje gidansu tace ya fasa auren maryama ya kaita gidansu ,amma yace mahaifiyarsa bazata karb'arta ba kai tsaye bai amince mata ba dan bashi da dalilin da zai kai wa mahaifiyarsa itace ta shirya masa komai ya kuma amince mata tasa masa mgna a bakinsa da zuciyarsa da duk abinda zai yi a karshe ya aureta su cigaba da rayuwarsu shi dai alokcin bai san meke faruwa dashi ba amman ji yake bazai iya rayuwa babu ita ba." yasan yana tsananin sonta amman son yazo ya karu ta yadda yake jin zai iya komai akanta kuma zai iya rabuwa da kowa akanta numfashi ya sauke alokcin yace ".wa zai min wakilci tace karka damu bari mu gama da wannan matsalar ni burina ka fita arayuwar maryama tukun ,idan kuma zaka yarda zan nemo dr lukman zai yi maka wakilci ."sai dai fa muna gama komai zaka saki maryama yace yaji kuma ya yarda dr lukman zai mishi wakilci kuma zai saki maryama domin samun nutsuwa da tabbaci akan zamansu tare bai san irin mawuyaciyar rayuwar da zai yi kenan ba sakamakon rashin ahalinsa kuma a yanzu yasan mantar dashi komai akayi ,bak'aramin lalata masa rayuwarsa tayi ba duk wani tabbacin da tai masa na zata bashi kulawa har izuwa k'arshen rayuwarta bai ga komai ba sai sa'banin haka domin hatta albashinsa cikin account dinta yake shiga direct ga tsananin takura da bin diddiginsa babu damar taga ya dade online yanzu ne zata hau sa da matsefa da mata yake chart this and that to dai ko mai yazo karshe ta barshi ya koma gurin yan'uwansa da mahaifi yarsa da matarsa maryama ko kuma ya