← Book details Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 94

Sashe 4

Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dole dai sai tasani idan lokacin mutuwar auren yazo maza ki karasa aikinki kafin ya dawo ko kuma ki barshi na karasa a umma bari na karasa ai nama kusan gamawa yazo, maryama ta mikawa umma takardun hannunta takardun gidan daya baku ne yace duk lokacin da kuka shirya tarewa ayi masa magana zai turo azo a d auke ku umma ta kar ba tana washe baki ita kuma maryama ta duka domin cigaba da aikinta umma tace kai masha Allah Allah mun gode maka da wannna niimar da kayi mana umma tayita kallon takardun tana santin gidan da bata gani ba kafin daga baya ta ajiye a gefe tasa hannu cikin d ayan bucket din tana d auraye kaya tana shanya tana wa mryama hirar adamcy abinda ta lura dashi tun da batun auren nan ya taso umma bada da wata hira sai tashi bini bini tace adamcy kaza ko ranar auren kaza zatayi atare suka k arasa aikin maryama ta d auraye bucket din da tai amafani dasu suka shige ciki sai dai ita kam duk arikice take bata da wani kuzuri . Maryama tana zaune cikin zullumi sai ga subai a ta kawo mata ziyara cike da murna ta tarbeta suka rungume juna maryama tace subai a kinga yadda kika dawo kuwa ?ya na dawo kin yi kiba kinyi kyau ,ke baki ga yadda kikayi fresh ba ? maryama ta harareta tana nuna mata wajen zama ana kai ina ke ta kaya Allah dai ya rufa asiri kawai inji cewar maryama ,ki zauna bari naje na kawo miki ruwa subai a ta samu waje ta zauna tana tambayr maryama umma daga inda take tsaye gaban fridge tace tana cikin d akinta tana lazimi ,ta dawo hannunta rike da ruwa da lemu ta ajiye mata kana ta zauna suka fara hira k awata kisan abinda ya kawoni? maryama ta girgiza mata Kai tun bayan da aka ganki nayita son nazo muyi magana akan batun aurenki da alhji mansor sai dai ban samu time ba saboda yanayin aikinmu to jiya na d auki hutu saboda Ina son zan biya kudin zuwa umara cikin wannnn sati tun kafin ta gama magana maryama ta fad a da fuskarta da murmushin farinciki tana riko hannun subai a cikin nata Kai masa Allah subai a na tayaki murna Allah yasa ayi ibada kar babbiya tace ameen k awata na gode shine nace nazo naji ya ake ciki idan har zan iya zuwa naje na dawo na sani duk dai sati biyu ne kawai zanyi kiyi tafiyar ki subai a dan tuni an fasa wannan auren subai a ta zaro ido waje tana cewa me yasa aka fasa kuma matsalar daga Ina ce ?to wannan Karon dai matsalar daga wajena ce Allah dai ya zaba mana abinda yafi zama alkhairi arayuwarmu . Ikon Allah amamn mai yasa zaki fasa aurensa maryama a inda yanzu maza suke wuyar samu ko dan kinga kina da saurin samu ne yasa kika fasa ? Sam ba haka bane subai a wata matsala ce ta taso wace matsala ce ki fad a min ko akwai shawarar da zan baki?wannnan matsalar bazata fad u ba subai a domin fad ar sa kamar sake jefa kaina cikin damuwa ne ni dai idan kinje umara kiyi min addua sosai dan Ina bukace da addua wallahi ai shikenan daman sai da nayi tunanin bazaki fada min ba kina nan dai da wannna zurfin cikin naki addua kuma in sha allahu zan miki maryama tai murmushi tace na gode . awata nima fa Ina da damuwa kusan ma abinda yasa zanje umara kenan akwai wanda na kamu da son shi a wajen aiki sai dai wallahi bazan iya fad a masa cewar Ina son shi ba amman wallahi ina mutuwar son shi zanje na roki Allah idan har alkhairi ne agareni Allah ya bani shi cikin sauki idan babu alkhairi Allah ya musanyamun da wanda yafi shi . kai subai a mutun bai ce yana sonki ba kawai sai ki kamu da son shi ? wallahi maryama jarabawar data same ni kenan mutumin ya had u sosai sai dai ayi min nisa da yawa dan ko gaisuwata ma da kyar yake amsawa a min waye shi a wajen aikin ? bazan fad a miki ba domin nasan muddin kikasani zaki shigar da kanki wajen nemo min abinda nake mutuwar so dan nasan muddin kika shiga ciki lallai zan iya samunsa sai dai ina gudun wulakacin da cin mutunci domin matuqar ba namiji ne yace yana son auren mace ba bata ta ba samun kwanciyar hankali daga garesa . Maryama tai shiru k waluwarta na budewa domin son gano wanda k awarta take mutuwar so haka a wajen aikinta to waye wanda take da yakinin muddin ta shiga ciki lallai zata iya samunsa ? me yasa subai a bazaki fad a min ko waye ba tunda kina ganin zaki iya samunsa ta hannuna? aa k awata bari dai naje nayi addua na dawo muga mai Allah zaiyi sun samu tsawon lokaci suna tautauna kafin daga bisa umma ta fito suka gaisa inda maryama ta sheida mata tafiyar subai a umma tayi farinciki tai mata addua sannna tace tai mika gaisuwarta ga maiaiki maryama sukai sallama da subai a har bakin sabon titi rakota sannan ta dawo . umma tayita zuba idanun dawowar mr ata amamn taji shiru har karfe goma na dare ta kasa hakuri tace maryama ba kince adamu zai dawo ba ? maryama tai tsam da ranta kafin tace haka yace min amman Ina ganin ya canza raayi ne umma ta d an numfasa nifa wallahi banason kuna nisa da juna ,daya zo bai ce miki ga ranar da wakilansa zasu zo bane ? maryama ta girgiza mata Kai alamun bai ce ba ni kam ayi ayi auren nan ko zan samu natsuwa dan wallahi bani da wata cikikiyar natsuwa, umma dan girman Allah ki kwantar da hankalinki duk abinda kikaga bai zo hannun mutun ba to wallahi Allah ba rabonsa bane haka ne Allah yasa muji alkhairi . Tunda mr ata ya barta bai sake nemanta ko a waya ba haka itama bata nemesa ba har sukai sati d aya sai dai sakonin tunin da wannan yar uwarsa tasa take mata kullum shine abinda ke jefata cikin zullumi da rashin kwanciyar hankali sai dai kullum sukai chart da subai a tana maimaita mata tai mata addua ita kuma kullum tana cikin addua tana zaune shiru tana tunani kwanakin da suka rage mata acikin lokacin da suka bata, sosai tayi zurfi cikin tunanin har k arfe shida yamamcin ranar ta buga ahankali wayarta ta soma ringing ko data duba mr ata ne ta gani ai bata tsaya bata lokaci ba ta d aga had e da sallam ya amsa mata yana cewa princess yunwa nake ta lumshe idanunta sakamakon wani sanyi daya ziyara ilahirin jikinta kina jina ? tace Ina ji me zaka ci Ki dafa min wani abu mai sauki tun safe banci komai ba me yasa zaka dinga barin kanka da yunwa ? bani da cikakkiyar natsuwa ne zuwa 7 :30 zan zo okay sir ! ta fad a tana jiran ya katse kiran bayan ya katse jollof din kuskus tayi tunanin tayi masa dan shine abinci mafi saukin dafawa dan lokacin ya tafi bare tayi tunanin dafa masa wani Abu dabam . ta shiga kitchen ta fara d auko abubuwan da zatayi amafani dasu cikin kankanin lokaci ta dafa masa kuskus wacce taji koren tattassai da kwakwamba albasa da hanta ta sauke ta zuba masa acikin wata yar madaidaiciyar kula sannan ta rufe sauran wanda umma zata ci dan ita kam murna son ganinsa ma yasa bata Jin zata iya cin komai ta fito ta duba fridge taga akwai sauran nah nahr da umma tayi ta maida fridge din ta rufe ta shiga d akin umma ta fad a mata zuwansa ai ko umma tayi farinciki yayinda maryama ta fito ta shiga wanka tare da dauro alwala ta fito . Bayan ta fito ta goge jikinta turare kawai ta fesa a ilahirin jikinta ta shirya kanta da wata atamfa light blue mai zanen fulawa blue black kayan sun zauna ajikinta most especially Siket din dan ya fito mata da hips dinta ta gama shiri adaidai lokacin da aka kira sallah ta d auki hijab ta zira ta tada sallah bayan ta idar tai addua ta mike ta saka takalmi flat ta d auko mayafi blue black zata d aura sai kuma ta fasa dan bata son tana bayyana jikinta ta d auki hijab Wanda yabi kayanta ta saka . Karfe bakwai da rabi saura ta fito parlour n ta zauna tana tunanin mr ata dake manne acikin zuciyarta bata wani jima da zama ba sai ga kiransa ta daga a natse tana gaishesa ya amsa yana shafa sumar kanshi tare da yin shiru zaka iya shigowa ina parlour Ina kan titin unguwarku na fito ne ?amman ahankali dan nasan kinyi missing dina sosai ta harare ta cikin waya tana cewa inji wa yace maka nayi missing sonka na gode da harara akayi min Ina jiranki . numfashi ta sauke sannan ta mike ta shiga d akin umma ta sanar mata da zuwansa amamn yana bakin titi ki gaishesa !tace to ta juya ta d auki jakar data had a masa abinci ta fito tana tafiya kamar mai tausayin kasa. natse ta karaso bakin titi inda ta hangosa tsaye a jikin motarsa sai kwayar idanunshi na kan hanyar fitowa daga lungunsu ahankali ta cigaba d aga kafafunta ta karaso ta tsaya a gabansa tana cewa yallabai bai dace ka tsaya anan ba inji wa ? ya fad a yana bud e gaban mota ya zauna a mazaunin direba yace bissimillah shigo . Take ta fahimci abinda yake nufi maimakon hakan daya bukata sai ta bud e bayan mota ta ajiye jakar hannunta sannna ta zagaya ta shiga ta zauna ta rufe kofar tana cewa Ina yini ! madadin ya amasa mata da lafiya sai kawai taji ya kamo hannunta ya sumbata ina son muyi wata magana dake mai mahimmanci bissimillah Ina sauraron ka ta fad a tana kokarin zare hannunta maganar tana bukatar natsuwa wanda ya nuna bai dace ayita anan
Chapter 4 · 0% Book details